Dalilin da na kikiro bakake da wasulan harshen Kahugu – Kwamared Joseph

Kwamared Joseph  Ma’aji  Hamza,  matashi ne dan kabilar Kahugu da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. A yanzu haka dalibi ne da ke karatun digiri a harshen Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.  Matashin ya yi babban kokari na kirkiro bakake da wasula na rubutun harshensa na Kahugu. A tattaunawa da wakilinmu, […]

Dalilin da na kikiro bakake da wasulan harshen Kahugu – Kwamared Joseph

Kwamared Joseph  Ma’aji  Hamza,  matashi ne dan kabilar Kahugu da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. A yanzu haka dalibi ne da ke karatun digiri a harshen Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.  Matashin ya yi babban kokari na kirkiro bakake da wasula na rubutun harshensa na Kahugu. A tattaunawa da wakilinmu, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar yin wannan aiki. Kuma ya bayyana mahimmancin rungumar harsunan kasa, maimakon na kasashen waje, kamar haka:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?

Kwamared Joseph: An haife ni a kauyen Kahugu da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna shekara 47 da suka gabata. Kuma ni dan kabilar Kahugu ne.

Na yi makarantar firamare a Dingin Kahugu, kuma na yi sakandaren kauyen Kono  da ke a Karamar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna. Na yi karatu a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya a Kafanchan,  daga nan na tafi Jami’ar Ahamdu Bello da ke Zariya, inda a yanzu nake karatun digiri a harshen Hausa.

Aminiya: To me ya karfafa maka gwiwar kirkiro rubutun bakake da wasula na  harshen Kahugu?

 Kwamared Joseph: Babban abin da ya karfafa min gwiwar kirkiro rubutun bakaken harshen Kahugu shi ne tsoron abin da  wani lauya  dan kasar Amurka, mai suna  Paul ya fada cewa, akwai wasu harsuna a duniya da za a neme su a rasa  nan gaba, saboda masu magana da wadannan harsuna,  sun yarda su rungumi harshe na biyu, maimakon nasu.

Yanzu ko a nan Najeriya  akwai harsunan da dama da suka mutu, saboda wannan dalili. Ko a  Karamar Hukumar Lere  akwai harsuna irin su harshen  Sheni, tuni sun   mutu saboda yadda masu shi, suka yi watsi da shi.

Ganin haka ya sanya na samu karfin gwiwar kirkiro bakaken rubutun na harshen Kahugu. Domin kabilar Kahugu da sauran masu jin harshen su rika amfani da su, wajen rubuce-rubuce don a bar wa na baya tarihi da gado. A samu hanyar rubuce-rubuce na al’adu da wake-wake da harkokin kasuwanci da rubuta littattafai da sauransu.

Bayan haka kuma na samu karfin gwiwar kirkiro bakaken  harshen  Kahugu ne, saboda na samu fahimta a karatun harshen Hausa da nake yi a Jami’ar Ahamadu Bello. Wannan ne ya dada karfafa min gwiwar kirkiro wadannan bakake da wasula na wannan harshe na Kahugu. Domin bai kamata mu dogara da bakon harshe ba, mu bar namu ya mutu.

Aminiya: Kamar yaya wadannan bakake da wasula na harshen Kahugu da ka kirkiro suke?

Kwamared Joseph:  Wadannan bakake  da wasula na harshen Kahugu da na kirkiro  sun kai bakake 42, kamar haka:

Manyan bakaken su ne: B,  B,  C, D, D, F, G, GB, GH, GW, GY, H, J, K, K, KH, KP, KW, KY, L, MP, N, N, N, P, PK, PY,  R,  R, S,  SH,  TS,  T,  W,  DY,  Y,  Y,? Z,

Kananan bakaken su ne b, b, c, d, d, f, g, gb, gh, gw, gy, h, j, k, k, kh, kp, kw, ky, l, m, mm, mp, n, n, n, pk, py, r, r, s, sh, ts, t, w, dy, y, y,? z.

 

Wasulan kuma  guda 18 ne.

Manyan bakaken wasulan su ne A, E, I, O, U, AA, EE, EL, II, OO, UU, AI, AU, OI, UI, IU, W, Y,

Kananan bakaken wasulan su ne: a,  e,  I,  o,  u,  aa, ee,  el,  ii,  oo,  uu, ai, au, oi, ui, iu, w, y,

 

Aminiya: Wane ci gaba ne kake ganin  aikin da ka yi, zai kawo ga harshen Kahugu da al’umma baki daya?

 Kwamared Joseph: Ci gaban da nake ganin wannan aiki zai kawo wa harshen Kahugu shi ne,  kabilar Kahugu musamman matasa za su samu abin da za su rike wannan harshe, ta yadda za su rika magana da  rubutu da shi. Kuma wannan aiki zai sanya sauran mutane wadanda ba sa jin harshen, su koyi magana da harshen, tare da rubutu da shi.

Aminiya: A matsayinka na mai nazari kan harshe, wace gudunmawa kake ganin harsunan kasar nan, za su iya bayarwa ga ci gaban kasa?

Kwamared Joseph: Babu shakka idan ana son a ci gaba a kasar nan, musamman ta fannin tattalin arziki dole, mu rungumi harsunanmu na kasar nan. Domin idan muka rungumi harsunanmu za a samu alfanu ta wajen rubuta littattafai da habaka harsunan su rayu ta yadda ba za su bace ba a duniya.

Aminiya: To wane kira kake da shi ga al’ummarku na Kahugu, dangane da wannan aiki da ka sanya a gaba?

 Kwamared Joseph: Kirana ga al’ummar Kahugu shi ne su sani cewa wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka su bayar da goyon baya kan wannan aiki, domin mu bunkasa wannan harshe ta hanyar samar da rubuce-rubucen adabi da littattafai  da wannan harshe. Yin haka zai sanya wannan harshe ya yadu a duniya, kamar yadda manyan harsunanmu na Najeriya irin su  Hausa da Yarbanci da Ibo suka yadu a duniya.

 

Aminiya: Mane ne babban burinka kan wannan aiki da ka yi?

 Kwamared Joseph: Babban burina shi ne in rubuta littattafai da harshen Kahugu, domin mutanen Najeriya da duniya baki daya, su san da wannan harshe. Domin harshen da yake da rubutun bakake ana iya yin amfani da shi a ko’ina.

 

Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati dangane da muhimmancin tallafawa wajen bunkasa harsunan kasa?

 Kwamared Joseph: Jan hankalina ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu  shi ne su rika tallafawa wajen yin rubuce-rubuce a harsunan kasar nan. Bai kamata mu rika dogaro da harsunan kasashen waje ba, wajen nazarin harkokin kimiyya da kere-kere da sauran harkokin yau da kullum. Ya kamata mu rika dogara da harsunanmu wajen yin wadannan abubuwa.

Misali kamar kasar China ta rungumi harsunanta, kuma yanzu a duniya babu wanda ya kai ta ci gaba saboda dogaro da harsunata da ta yi, haka Japan da Jamus da sauran kasashen da suka ci gaba.

 

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano