Dalilin da na mayar da N10m da aka yi kuskuren turawa asusuna — Mai POS
A kullum ina samun fiye da Naira dubu biyar domin ina da manyan abokan ciniki.
Muhammad Sani Abdurrahman wani mai hada-hadar kudi ta POS ne a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano.
A kwanan nan ya zama abin kwatance sakamakon kyautar Naira dubu 500 da aka yi masa, bayan ya mayar da Naira miliyan 10 da aka yi kuskuren tura wa asusunsa na banki.
Duk da cewa lamarin ya faru tun a watan Disamban 2023, sai dai an dauki tsawon wata uku kafin ’yan sanda su kammala bincike, inda kuma suka yi sa’ar samun mai kudin.
Aminiya ta tattauna da shi game da dalilin da ya sa ya mayar da kudin duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan.
Yaya aka yi ka mayar da Naira miliyan 10 da aka yi kuskuren tura wa asusunka na banki?
Zan iya tunawa, a ranar 21 ga Disamban 2023, wani abokin cinikina ya zo shagona yana so ya cire Naira dubu 10.
Bayan mun tashi daga shago sai muka fara lissafin harkokin da muka yi a wannan rana.
Sai muka gano cewa mun samu karin Naira miliyan 10.
Mun yi ta kokarin gano wanda ya sa wannan kudi ba tare da saninmu ba.
Muka yi ta bincikenmu don ganin haƙiƙanin yadda lamarin ya faru, daga ƙarshen muka gano cewa wani ne ya yi kuskuren sanya kudin a asusun. Tunda ba mu san shi ba, ba zai yiwu mu iya gano shi ba.
Bayan na yi wa makwabtana bayani, sai muka yi kokarin sanar da ’yan sandan Kwakwaci.
Bayan mun yi musu bayani sai suka ce lamarin ya fi karfinsu, don haka suka tura mu sashen da ke kula da manyan laifuffuka na Bompai.
Tsawon wannan lokaci ban ji kira daga wani ba sai a ranar 13 ga Maris 2024 ’yan sanda suka kira ni cewa, sun samu mai kudin, don haka suna so in je ofishinsu.
Ina zuwa na ga fuskarsa sai na gane shi, abokin cinikina ne da yake yawan zuwa shagona don yin harkokin kudi.
Bayan ’yan sanda sun gama duk abubuwan da ya kamata, sai suka tafi da ni wajen Kwamishinan ’Yan sanda.
Daga baya na tura masa ragowar kudinsa cikin asusunsa.
Shin ka samu wani alheri bayan haka?
Eh, mutumin ya ba ni Naira dubu 500. Ya fada min cewa, shi bai ma san cewa ya kara kudin ba har sai lokacin da ’yan sanda suka kira shi a waya sannan ne ya gane kuskuren da ya yi.
Shin ka samu wata kyauta daga wani wajen?
Gaskiya ban samu ba, domin har zuwa yanzu babu wanda ya kira ni kan lamarin.
Ladana yana wurin Ubangiji, amma duk wanda ya ya ba ni wani abu, zan karba.
Me ya ja hankalinka ka mayar da kudin?
Na yi imanin cewa, duk kudin da ba nawa ba, bai kamata in yi amfani da shi ba.
Kowane irin yanayin ake ciki ya kamata in nemi mai kudin, in mayar masa.
Rayuwar nan ba wai duniya ce kawai ba, akwai Lahira, kuma za a yi mana hisabi a kan abin da muka aikata.
Ba na so in yi amfani da duk wani abu da ba nawa ba.
Ka san akwai abubuwan rashin gaskiya da ake yi a yanzu, ban san cewa wannan kudi na halal ne ko na haram ba ne ko kuma na wani aikin barna ne, don haka na zabi in sanar da ’yan sanda.
Shin irin hakan ta taba faruwa da kai a baya?
Kwarai na taba haduwa da irin wannan, sai dai wancan kudi Naira dubu 100 ne.
Shi ma wani ne ya tura min kuma ban san shi ba. Na yi ta jiran sa, ya zo ya karɓi abinsa.
Bayan kwana hudu sai ’yan sanda suka yi min waya, inda suka nemi in je in yi bayanin yadda na samu kuɗin, duba da cewa suna zargin kuɗin an same su ne ta wata hanyar da ba ta dace ba.
Na gode Allah da na je da lauyana wurin, don haka aka warware abin cikin sauki.
Yaya ka ji da ka ajiye kuɗin a wurinka kafin ka samu mai su?
Gaskiya na shiga ruɗani. Ranar farko ma ban iya yin barci ba, domin kuɗi ne masu yawa. Ban taba riƙe irin wadannan kuɗin a rayuwata ba.
Nawa kake samu a rana?
A kullum ina samun fiye da Naira dubu biyar domin ina da manyan abokan ciniki masu yawa. Nakan yi hada-hadar kuɗi kamar sau 100 a rana. Alhamdulillah, ina samu.