Dalilin da na rubuta littafin ‘Garuruwan Karamar Hukumar Nasarawa’

Rubutu yana inganta ne da yawan karatu.

Dalilin da na rubuta littafin ‘Garuruwan Karamar Hukumar Nasarawa’

Bello Sagir

Bello Sagir shi ne Shugaban Kamfanin Sunrise Language Practitioners (SLP) da ke Jihar Kano.

Aminiya ta tattauna da shi a kan dalilinsa na rubuta tarihin garuruwan Nasarawa da sauran littattafan da yake aiki da kalubalen da yake fuskanta:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Bello Sagir. Ni dan asalin garin Getsi ne mai dimbin tarihi da ke mazabar Tudun Murtala, a karkashin garin Dakata da ke Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano. Na yi karatun difloma a fannin shari’a a Kwalejin Nazarin Shari’a ta Aminu Kano.

Daga bisani na yi digiri a fannin ilimin kimiyyar harshe (Linguistics) a Jami’ar Bayero.

Ni mamba ne a Kungiyar Marubuta ta Kasa, (ANA), reshen Jihar Kano, na taba zama tsohon mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a a kungiyar na wa’adi biyu.

Kuma an wallafa makaloli da dama da na rubuta a jaridu da mujallu.

Me ya ja hankalinka ka rubuta littafin Garuruwan Karamar Hukumar Nasarawa?

Abin da ya ja hankalina na rubuta littafin Garuruwan Karamar Hukumar Nasarawa (1430-2021), shi ne ganin babu irin littafin kuma ana bukatarsa.

Masu bukatar littafin sun hada da dalibai, musamman masu shirin kammala karatu a jami’o’i da sauran makarantun share-fagen shiga jami’a da ’yan jarida da ’yan siyasa da su kansu mutanen Karamar Hukumar Nasarawa da masu alaka da ita da sauran manazarta na Najeriya da na kasashen waje.

A lokacin da nake hira da Mai unguwar Jigirya da ke karkashin garin Dakata, ya shaida min cewa, kamar yadda na je da mai daukar hoto domin yi masa tambayoyi, haka wata Baturiya ta taso takanas tun daga Ingila zuwa fadarsa da rakiyar tafinta, ita ma da mai hoto.

 

Littafin Garuruwan Karamar Hukumar Nassarawa

Mai unguwar ya fada min cewa, tambayoyin da na rika yi masa suna kama da wadanda ta rika yi masa.

Tambaya ita ce, me ta za ta yi da wadannan bayanan da ta samu?

A dan bincikena, tarihin Afirka da Najeriya ko kasar Hausa duka Turawa ne suka rubata mana suka ba mu, mu kuma muka karba, muke koyarwa a makarantunmu, kuma muke kafa hujja da su a matsayin madogara.

Dokta Muhammad Uba Adamu (Allah Ya jikansa) ya yi suka ga wasu daga cikin ikirarin wadannan littaffai, musamman na The Kano Chronicle na H.R. Palmer.

Doktan ya zarge su da saka son rai domin kaskantar da addini da al’adunmu.

A ganin Bature, tarihinmu a Afirka, ya fara ne daga shigowarsa nahiyarmu.

Joseph Conrad a littafinsa mai suna Heart of Darkness ya nuna cewa mu mutanen Afirka ba mu da tarihi.

Akwai littattafai na tarihi da aka rubuta na garuruwa daban-daban a nan Kano da na karanta.

Misali Tarihin Tsanyawa da Dambatta wanda Abba Ibrahim da Mustapha Dambatta suka rubuta. Sai kuma Tarihin Kura da Kabiru da Sa’idu suka rubuta.

Ga kuma na Kutama kai har ma da na Gusau da bijimin malami Farfesa Sa’idu Gusau na BUK ya rubuta.

Na Karaye kuwa Ibrahim da Philips ne suka rubuta.

Tambayar da na yi wa kaina bayan karanta wadannan littafan ita ce, shin me ya sa babu tarihin na Nasarawa? Shin ba mu da marubuta ne?

Ko kuwa mu ba mu da tarihi kamar yadda su Conrad suke fada? Ko kuma jira muke sai Turawa daga Ingila sun zo sun rubuta mana?

A zagayen tattara bayanai, me ka gano muhimmai a garuruwan?

Na rubuta littafin Garuruwan Karamar Hukumar Nassarawa (1430-2021) ne domin taskace tarihinmu da bincike mai inganci domin mu san kanmu da mutanen da suka ba da gudunmawa wajen kafa garuruwanmu da samar musu da ci gaba, matattunsu da rayayyunsu.

Bugu da kari, yana daga manufata taskace wuraren tarihinmu saboda muhimmancinsu.

Misali itatuwa da rijiyoyi da ramuka da gidaje da makarantu da masallatai da sauransu.

Tattare da hakan, akwai damuwa saboda yadda muhimman wuraren tarihinmu suke bata.

Misali a garin Badawa, mai unguwar ya raka mu daukar hoton wata itaciya mai dimbin tarihi da ya ba mu labarinta.

Kamar yadda ya fada mana, zamanin iyaye da kakanni, idan mahara sun kai musu farmaki, a bayanta kakanninsu suke buya da sun buya, nan take sai su bace su kuma maharan sai a ga kamar an yi musu shashatau sun kasa gane ta yaya mutanen suka bace.

Sai su koma su hakura. Abin takaici wannan itaciiyar ana kan sare ta muka je. A lokacin saura kadan a kai ga kututturenta.

A Kawo kuwa, akwai wata rijiya wacce a zamanin da, idan mata suka debo ruwa daga cikinta mutuwa suke yi, kuma ba a diban ruwa da gugar karfe a ciki.

Kwami na masunta daga Wudil ya taba bata, sai Sarkin Ruwansu ya biyo idon ruwa ta karkashin kasa tun daga can ya iso Kawo kuma ya dauki kwamin ya koma ta idon ruwan!

Da muka je da wakilin mai unguwa sai muka tarar an rufe ta. Da muka koma muka yi masa bayani sai ransa ya baci. Ya yi ta fada yana tir da abin da aka aikata.

A Jigirya kuwa, an yi wani dutse da ake kira Dutsen Jirgiya wanda yake da dimbin tarihi.

Dutsen ya wanzu kusan shekara dubu da suka wuce, wato zamanin Barbushe, kamar yadda littafin The Kano Chronicle na H.R. Palmer ya nuna.

A yanzu sai dai kufai na wannan dutsen wanda shi ma kullum gushewa yake yi.

A garuruwan Gama da Hotoro da Unguwar Tudun Murtala da sauran garuruwa da unguwannin Nasarawa, haka batun yake wajen sarayar da kayan tarihi.

A wannan gabar, ina yin kira ga mahukunta da kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun mutane masu hali su shigo ciki domin ceto wuraren tarihinmu.

Gwamnati za ta iya rika samun kudin shiga daga wuraren tarihi na unguwanninmu, idan aka killace gami da alkinta su.

Me ya sa ka zabi rubuta littafin tarihi, maimakon na kagaggun labarai?

Na rubuta kagaggun labarai da wakokin zube a shekarun baya, to amma yanzu ban fiye yin irin wadannan rubutu ba saboda na fi ganin zan fi ba da gudunmawa ta bangaren rubutun da ba kagagge ba, musamman na tarihin gari ko al’umma ko kuma tarihin rayuwar wani fitaccen mutum.

Littattafai nawa ka rubuta?

Wannan shi ne littafi na farko da na wallafa.

Wane littafi ne kake aiki a kai bayan wannan?

Akwai littattafai da dama da nake rubutawa a yanzu. Misali, tarihin rayuwar Aminu Ladan Abubakar (ALA) wanda sauran kiris na kammala da kuma tarihin rayuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Akwai mutanen da suke taya ni bincike da rubutun littattafan saboda girman al’amarin.

Bayan haka, akwai kuma littattafai su ma guda hudu na koyo da kuma inganta yin magana da rubutu a harshen Ingilishi a saukake da na rubuta.

Zan buga da kaddamar da su a badi insha Allah.

An ce matasa ba sa son karatu, yaya kake gani?

Haka ne matasa daga al’ummarmu yawancinsu ba sa son karatu. Saboda dalilai da dama. Misali, akwai abubuwa da yawa masu shagaltarwa daga karatu kamar nishadi da suka yi mana yawa.

Nishadi yana da kyau, saboda ai “rai dangin goro” ne, kuma “taba-kidi, taba-karatu”, amma duk da haka idan ka kalli yadda matasa suke yawan kallon kwallon kafa da yin ta da bibiyarta da hirarta ko musunta, da kallon fina-finai da sauraron wakoki, za ka ga nishadin ya yi yawa.

Al’ummar da take da tarin matsaloli irin namu, ya kamata ta rage nishadi, ta mayar da hankali wajen karance-karance domin ta haka ne mutum yake amfanar da kansa da al’umma.

Bayan haka, akwai talauci da son sai a yi kudi a cikin kankanen lokaci, shi ma ya taka rawa matuka wajen rage wa matasa son karatu.

Yawancin matasa maza da matanmu, so ake kawai a yi kudi na kece-raini a lokaci kankane, wannan ya sa mutum ya kasa samun lokacin zama ya karanta ko da shafi daya ne a kowace rana.

Kafafen sada zumunta su ma suna rage wa matasa sha’awar yin karatu. Akwai kuma gado da muka yi a Afirka cewa sauraro ya fi sauki a kan karatu.

Wannan ne ya sa muka fi sauraron rediyo fiye da karatu. Zan so mai karatu ya karanta mukala a kan muhimmancin karatu da Farfesa Ibrahim Bello Kano (IBK) na Jami’ar Bayero ya rubuta.

Na fassara ta da Hausa da taken “Yi Karatu! Yi Karatu! Yi Karatu!”

Mece ce mafita a kan wannan matsala?

Mafita ita ce, mu tuna fa addininmu na Musulunci addinin karatu ne. Sannan mu rika kallon kasashen da suka ci gaba da yadda karatu yake taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da su gaba.

Gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da masu hali su rika hada gwiwa da kungiyoyin marubuta irin su ANA suna shirya bitoci da tarurruka domin wayar da kan al’umma a kan muhimmancin yin karatu.

Shirye-shirye a gidan rediyo a kan muhimmancin karatu su ma suna da muhimmanci sosai.

Sannan ya kamata mahukunta da kungiyoyi da masu hali su rika saka gasa da daukar dawainiyar bugawa da yada littattafai da sauran abubuwan karfafa gwiwa ga marubuta.

Wace shawara za ka ba manyan mutane a kan rubuta labarinsu?

Yana da matukar muhimmanci duk wanda ya yi gwagwarmaya a rayuwa ya rubuta littafin tarihin rayuwarsa da kansa ko kuma ya hada gwiwa da wani marubucin su rubuta tare, kamar yadda Sheikh Muhammad Abubakar Gumi ya yi tare da Farfesa Isma’il Tsiga a lokacin da malamin yake kusa da rasuwa.

Da a ce saboda ba ya da lokacin rubutawa shi kadai ya ki ya rubuta a madadin yadda ya yi, ya kirawo Tsiga suka yi tare, da yanzu mu ’yan baya ba mu san yadda ya yi gwagwarmaya ba, kuma da ba mu amfana da gwagwarmaya da ya yi ba.

Mutum zai kuma iya bayarwa a rubuta masa. Taskace gwagwarmaya da ta yi nasara a matsayin littafin tarihin rayuwa yana da matukar muhimmanci.

Wace shawara za ka ba masu karatu da marubuta?

Masu karatu su ci gaba da karatu a ko’ina suke. Akwai miliyoyin littattafai a Intanet da mutum zai iya saukewa a wayarsa ya karanta a kyauta!

Babu shakka in dai mutum yana son yin karatu yadda ya kamata, sai ya yi amfani da duk wata dama da ya samu komai kankantarta wajen yin karatu ko da kuwa shafi daya ne a kullum.

A littafi guda daya ana samun ilimi mai yawa wanda wani zai gama rayuwarsa kaf bai samu irinsa ba.

To ina ga mutum ya karanta daruruwa ko dubban littattafai! Masu rubutu kuma kada su gaza.

Al’ummarmu lokuta da yawa ba ta karfafa wa marubuta gwiwa, musamman sababbin marubuta.

Kada mu damu, mu ci gaba da rubutu, amma fa mu sani, karatu ya kamata ya fi rubutu yawa.

Rubutu yana inganta ne da yawan karatu.

Me ya sa ka kafa Kamfanin Sunrise Language Practitioners?

Na assasa Kamfanin Sunrise Language Practitioners (SLP) ne domin kawo sauyi a fagen ayyuka na harshe, musamman yadda ake samun wadanda ba su karanta harshe ba ko kuma sun samu horo na musamman ba, amma suke yin kutse a fassara da sauransu.