Dalilin da na rubuta littafin koyar da Fulatanci – Laraba Ahmed Kawu
Hajiya Laraba Ahmed Kawu Bafulatana ce yar asali Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe kuma gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati da ta rike mukamin Daraktar Kudi da Mulki ta Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA) ta Jihar Gombe, kafin ta zama Babbar Sakatariya a Hukumar Fansho ta jihar. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ta rubuta […]
Hajiya Laraba Ahmed Kawu Bafulatana ce yar asali Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe kuma gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati da ta rike mukamin Daraktar Kudi da Mulki ta Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA) ta Jihar Gombe, kafin ta zama Babbar Sakatariya a Hukumar Fansho ta jihar. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ta rubuta wani littafi da harshen Fulatanci mai Suna “En Ekkito Fulfulde” wato “Mu Koyi Fulatanci.”
Mene ne dalilin da ya sa kika rubuta littafi da harshen Fulatanci?
Dalilin da ya sa na yi sha’awar rubuta littafin da harshen Fulatanci shi ne ni Bafulatana ce mai kishin harshen. Kuma abin mamaki gari kamar Gombe da duniya ta san garin Fulani ne sai ga harshen yana neman bacewa saboda ba kowane gidan Fulani ba ne za ka je, ka ji suna yi wa ’ya’yansu magana da harshen ba. Saboda takaici ya sa ni kuma don kada Fulatanci ya bace a garin Fulani ya sa na rubuta littafin koyon Fulatanci mai suna ‘En Ekkito Fulfulde’ don amfanin yaranmu masu tasowa.
Yanzu ke kina yin magana da Fulatancin sosai?
Eh na iya Fulatanci tun ina karama mu a gidanmu ba a mana magana da Hausa sai Fulatanci. Idan ka ji muna magana da wani harshe, sai idan muna waje amma ban da a cikin gida, amma yanzu da aka watsar da harshen, sai Hausa ke cinye harsunan mutane shi ya sa ba zan so harshen Fulatanci ya bace ba, hakan ya sa na himmatu na dauki lokaci sosai wajen tsayawa in ga na samar da littafin da za a rika koya wa ’yan baya wannan harshe.
Mene ne burinki kan harshen Fulatanci da har ba ki son ya bace a Gombe?
Ba ni da wani burin da ya wuce in cika wa mahaifina burinsa, wanda kafin ya rasu yake son ganin harshen Fulatanci ya yi fice a duniya, ba a Gombe kawai ba. Shi ya sa burin ba zai cika ba har sai na samar da wata hanya da za a rika koyar da harshen a gida ko a makaranta, hanyar kuma ita ce ta rubuta littafi.
Fulatanci ya fara bacewa musamman ma a kwaryar garin Gombe domin duk da cewa an san Gombe garin Fulani ne amma Fulatancin yana bacewa. Ba sosai ake yin sa ba amma idan ana koyar da shi za a shawo kan matsalar. Ganin haka ya sa nake kira ga al’ummar Fulani a duk inda suke su rika koya wa ’ya’yansu harshen kada su rika haihuwar ’ya’ya su bari su tashi ba sa jin harshen idan aka taba su kuma su ce su Fulani ne alhali ba sa jin harshen.
A ganinki me ya sa Fulatancin ke neman bacewa a kwaryar Gombe?
Rashin kishi na Fulani da suna kishin harshensu da ba zai nemi bacewa ba. Yanzu idan ka dubi kasashe irin su China da Indiya ci gaban da suka samu a duniya ya biyo bayan rike harshensu da al’adunsu ne da suke yi da kuma tsayawa kan abincinsu na gargajiya. Hakan ya sa ko kasashen ka je karatu sai ka fara koyon harshensu sannan ka dora su ba sa sha’awar kwaikwayon harshen wadansu sai nasu, shi ya sa suka zama abin da suka zama yanzu a duniya.
Wane kira za ki yi ga Fulani?
Shawarata gare su, ita ce su tsaya kan harshensu domin wani abin takaici da bakin ciki shi ne ko gidan Fulani ka je idan ka yi musu gaisuwa da Fulatanci kana cewa Nbale Jam sai ka ji sun mayar maka da Hausa cewa lafiya saboda suna kunyar harshen, wannan ba daidai ba ne.
Ko kina da kira ga gwamnati wajen ganin an sanya Fulatanci cikin tsarin koyarwa a makarantun Jihar Gombe?
Kirana ga Gwamnatin Jihar Gombe shi ne tunda Gombe gari ne na Fulani kuma suna da yawa a jihar a shigar da darussan Fulatanci ya zama dole a tsarin koyarwa tun daga firamare har zuwa sakandare don ganin yara suna koyon harshen cikin sauki.
Rubutu cikin wani harshe ba Ingilishi ko Hausa ba ya fi bada wahala wane kalubale kika fuskanta wajen rubuta wannan littafi?
Gaskiya duk da kuncin lokaci amma haka nake kukutawa nake rubutun idan na samu lokaci. Ko a gida ne cikin dare idan na tuna wata kalma sai in tashi in rubuta don kada in manta, haka a ofis da haka da haka na yi ta yin rubtun har na gama cikin shekara daya da wasu watanni.
Ko kina da wani buri naki nan gaba?
Eh, ina da buri kuma burina nan gaba shi ne in samu wadanda za mu hada kai tare mu rubuta ci gaban littafin wanda yake dauke da zane-zanen dabbobi da wasu alamu da za su kara wa yara sha’awar tsayawa su yi karatun domin hotuna na burge yara su sa su tsaya don koyon abu.
Me za ki ce a kan manazarta wannan littafi naki?
Gaskiya ba ni da wata kalmar da zan iya gode wa manazartan wannan littafi nawa na En Ekkito Fulfulde, domin sun yi kokari musamman ma Sashin Nazarin Harsuna na Jami’ar Bayero ta Kano bisa gudumawar da suka bayar wajen duba littafin da yin wasu gyare-gyare kafin a wallafa shi a kai ga kaddamar da shi ya fito kasuwa.