Dalilin da na yi aikin Hajji a Kano —Maniyyaci

Maniyyacin Jihar Kano da jirgi ya bari bai samu zuwa sauke farali ba, ya bayyana dalilinsa na gudanar da aikin Hajjinsa a Kano.

Dalilin da na yi aikin Hajji a Kano —Maniyyaci

Maniyyacin Jihar Kano da jirgi ya bari bai samu zuwa sauke farali ba, ya bayyana dalilinsa na gudanar da aikin Hajjinsa a Kano.

Aminiya ta rawaito cewa maniyyacin da bai samu tashi a jirgin karshe ba zuwa kasar Saudiyya ranar Alhamis ya ce zai yi aikin Hajjinsa na bana a sansanin horar da alhazai na jihar.

Maniyyacin, mai suna Malam Jibrin Abdu, daga Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano dai ya dauki hankulan jama’a ne lokacin da aka gan shi sanye da harami, inda ya ce shi tuni ya fara gudanar da aikin Hajjin nasa a Kano.

A tattaunawarsa da wakilinmu ranar biyu ga Sallah, Abdu, ya bayyana cewa yanayin da ya shiga na damuwa ne ya sa shi yin alwala ya yi Sallah sannan ya fara gabatar da aikinsa da tunanin hakan zai saukaka masa damuwa.

Ya kara da cewa, “Yadda hankulan jama’a suka tashi, kowa na cikin damuwa, ana ta kuka ana ta tsinuwa ya sa na yi wannan shigar don jan hankulan mutane ko sa samu sauki.

“Alhamdulillah, hakan ya yi tasiri kwarai da gaske domin na ga mutanen da ke kuka sun koma dariya.”

Sai dai ya bayyana cewa bai samu damar zuwa ya karasa aikin Hajjin nasa ba saboda ba ingantacce ba ne kuma Kano ba Saudiyya ba ce.

“Allah Bai kira mu ba. Wadanda suka samu damar zuwa kuma Allah Ya dawo da su cikin koshin lafiya, Ya kai mu wata shekarar cikin koshin lafiya.”

Idan za a iya tunawa, Aminiya ta rawaito yadda jirgin karshe ya bar Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar Kano, Abba Danbatta da wasu daraktocin hukumar da wasu maniyyata 745 a kasa, inda ba za su sami damar sauke farali ba a bana.

Jirgin na kamfanin Azman, wanda ya tashi da misalin karfe 3:40 na yammacin Alhamis, ya bar maniyyatan ne duk da karin wa’adin da kasar Saudiyya ta yi wa Najeriya.