Dalilin da na ziyarci Obasanjo — Atiku
Bayanai sun ce an shafe tsawon sa’a ɗaya da rabi ana ganawar wadda aka yi ta a bayan labule.
![Dalilin da na ziyarci Obasanjo — Atiku Dalilin da na ziyarci Obasanjo — Atiku](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/20250210_181016.jpg)
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a wannan Litinin ɗin.
Aminiya ta ruwaito cewa, da misalin ƙarfe 12:36 na yau Litinin ce tawagar da Atikun ya jagoranta ta isa gidan tsohon Shugaban Ƙasar da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
- Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga
- Gwamna Sule ya naɗa Kwamishinoni 16 a Nasarawa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke da takwaransa na Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal haɗi da ɗan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi.
Bayanai sun ce an shafe tsawon sa’a ɗaya da rabi ana ganawar wadda aka yi ta a bayan labule.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai da misalin ƙarfe 2:11, Atiku ya bayyana cewa ziyarar ban girma ce kawai ta kawo shi wurin ubangidan nasa.
Haka kuma duk da tsananta ƙwaƙƙwafi da manema labaran suka yi, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce ba zai ce uffan ba dangane da duk wani batu da ya shafi siyasa.
“Ziyarar ban girma ce ta kawo ni saboda haka ba zan ce komai a kan abin da ya shafi siyasa ba,” in ji Atiku.
Atiku ya kasance mataimaki ga Obasanjo daga watan Mayun 1997 zuwa Mayun 2007.
A bayan nan dai Atiku wanda ke muradin kujerar Shugaban Nijeriya ya yi ganawa daban-daban kan abin da ake zargin shirye-shiryen tunkarar Zaɓen 2027.