Dalilin da nake hidimar kasa bayan shekara 22 — Hannatu Musawa
Saboda haka babu wata doka da na sabawa a Najeriya,
Sabuwar Ministar Al’adu da Bunkasar Tattalin Arziki, Hannatu Musawa, ta magantu dangane da cece-kucen da ake a kanta na rike mukamin gwamnati a lokaci guda da take yi wa kasa hidima.
Duk da cewa batun kasancewarta daya daga kunshin matasan da ke yi wa kasa hidima ya dade da bayyana, lamarin ya sake yamutsa hazo a bayan nan yayin da Kungiyar Marubuta Kare Hakkin Bil Adama a Najeriya (HURIWA), ta sake bijiro da batun cewa Ministar Shugaba Bola Tinubu tana yi wa kasa hidima.
- Barcelona ta sha da kyar a gidan Villarreal a La Liga
- Shugaban Amurka ya buƙaci ganawa ta musamman da Tinubu
Kan haka ne a bayan nan Darektan Hulda da Jama’a na Hukumar Kula da Matasa Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC), Eddy Megwa, ya ce rike mukamin minista ya saba wa Dokar hukumar.
Da yake zantawa da Aminiya, Mista Megwa ya yi bayanin cewa yi wa Dokar NYSC karen tsaye ce ga duk wani mai yi wa kasa hidima ya karbi wani mukamin gwamnati alhali bai kammala bautar kasar ba ta shekara guda.
Ya yi bayanin cewa, tun a shekarar 2001 aka tura sabuwar Ministar Jihar Ebonyi domin yi wa kasa hidimar, amma daga bisani aka mayar da ita Jihar Kaduna domin ci gaba da aikin bautar kasar.
Sai dai Megwa ya ce bayan komawar Hannatu Musawa Jihar Kaduna, ba ta iya karasa aikin bautar kasar ba, lamarin da Hukumar ta NYSC ta ce za ta yi nazari a kanta domin daukar matakin da ya dace.
Martanin Hannatu Musawa
Cikin wata sanarwa da ta fitar a Yammacin wannan Lahadin, sabuwar Ministar ta bayyana dalilin da ta jingine yi wa kasa hidimar tun a wancan lokaci sai a bana.
Ta yi karin haske da cewa Jihar Akwa Ibom aka tura ta yi wa kasa hidimar sabanin ikirarin da Darektan Hulda da Jama’a na Hukumar NYSC ya yi na cewa Jihar Ebonyi aka tura ta.
A cewarta, “babu inda na saba wa wata Doka ko Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kasancewata minista kuma mai yi wa kasa hidima a lokaci guda.
“Ya kamata a sani karara cewa babu wata Doka a Najeriya ko Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ko Dokar Hukumar NYSC da hana a bai wa mai yi wa kasa hidima mukami a gwamnati.
“Haka kuma, babu wani sashe na wata Doka ko Dokar Hukumar NYSC ta ce dole sai mai yi wa kasa hidima ya kammala bautar kasar gabanin samun wani mukami a gwamnati.
“Saboda haka babu wata doka da na sabawa a Najeriya,” inji ta.