Dalilin da nake neman maye gurbin Sanata Barau Jibrin a Kano ta Arewa — Gwarzo
Gwarzo ya taɓa shan kaye bayan fafatawa da Barau a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2015.
Tsohon ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Tijjani Muhammad Gwarzo, ya bayyana cewa aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Kano ta Arewa na da nufin inganta wakilci, bunƙasa ci gaba da kuma ɗaga murya kan bukatun al’umma a matakin ƙasa.
Gwarzo ya bayyana haka ne yayin wani taro da magoya bayansa da jiga-jigan jam’iyya a gidansa da ke Kano a ranar Asabar, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan nazari mai zurfi da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki.
Ya ce kiraye-kirayen da ya samu daga mazabu, dattawa, matasa da ƙungiyoyin mata ne suka ƙarfafa masa gwiwa ya fito takara.
“Ba mu yi kunnen uwar shegu da kiran al’umma ba. Amincewar da suka nuna min babban abin godiya ne,” in ji shi.
Ya soki yadda aikin faɗaɗa titin Kano–Gwarzo–Dayi ke tafiya a hankali, duk da cewa an ware masa kuɗi, yana mai cewa dole ne a inganta sa ido da wakilci domin ganin an aiwatar da irin waɗannan ayyuka yadda ya kamata.
Gwarzo ya yi alƙawarin ƙarfafa shirye-shiryen horas da matasa sana’o’i, yana mai cewa cibiyar ATM Gwarzo da ke bai wa matasa horo za a faɗaɗa ta zuwa sauran ƙananan hukumomin yankin.
A ɓangaren siyasa, ya bayyana cewa yana neman kujerar ne domin maye gurbin Sanatan da ke kan mulki, Barau Jibrin, wanda a halin yanzu shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Tun farko dai Gwarzo ya taɓa shan kaye bayan fafatawa da Barau a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2015.
Ya kuma yaba wa Bola Ahmed Tinubu kan manufofin “Renewed Hope Agenda”, da kuma ƙarfafa Asusun Ba da Lamunin Ilimi (NELFUND), tare da ambaton ayyukan bututun gas na AKK da layin dogo na Kano–Katsina–Maradi.
Haka kuma ya jinjina wa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf kan rawar da suke takawa wajen ci gaban jihar.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsoffin kwamishinoni da jiga-jigan jam’iyya, ciki har da Mukhtar Ishaq Yakasai da Kabiru Getso da sauransu.
Gwarzo, wanda ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukuma har sau huɗu, sannan ya riƙe muƙamin Mataimakin Gwamna da kwamishina, ya kuma jagoranci APC a Kano a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, na daga cikin fitattun ’yan siyasa a jihar.