Dalilin da nake yi wa Janar Buhari waka- Murtala Mamsa

Murtala Abdullahi Musa wanda aka fi sani da Murtala  Mamsa da ke zaune a garin Jos a Jihar Filato, mawaki ne da ya yi fice wajen rera wakokin siyasa da na fina-finan Hausa. A yanzu shi ne babban mawakin Janar Buhari. Ya tattauna da Wakilin Aminiya, inda ya bayyana yadda ya fara harkar waka da […]

Dalilin da nake yi wa Janar Buhari waka- Murtala Mamsa
Dalilin da nake yi wa Janar Buhari waka- Murtala Mamsa

Murtala Abdullahi Musa wanda aka fi sani da Murtala  Mamsa da ke zaune a garin Jos a Jihar Filato, mawaki ne da ya yi fice wajen rera wakokin siyasa da na fina-finan Hausa. A yanzu shi ne babban mawakin Janar Buhari. Ya tattauna da Wakilin Aminiya, inda ya bayyana yadda ya fara harkar waka da kuma irin nasarorin da ya cimma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Za mu fara da takaitaccen tarihin rayuwarka?
An haife ni a garin Samurun Zariya da ke Jihar Kaduna, a yanzu ina zaune a garin Jos da ke Jihar Filato. Shekarata 25. Ban yi gaji waka ba, sana’ar fawa na gada a wajen iyayena.  Daga baya ne na fara rubuce-rubucen wakoki tare da rerawa, inda na fi karfi wajen rubuta wakokin abubuwan al’ajabi da na soyayya. Daga nan har Allah Ya hada ni da wasu masu harkar fina-finan Hausa. Na fara rubuta musu wakokin fina-finai. Daga nan  Allah Ya dora mini son dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC  Janar Muhammad Buhari.  Don haka a halin yanzu kusan duk wakokina, na yi su ne a kansa.
Mene ne ya karfafa maka gwiwa harka shiga harkar waka?
Ka san idan Allah Ya ba ka abu ko yaya yake sai ka karba. Don haka ba zan iya ce maka na fara waka don sha’awa ko don kudi ba. Ni dai na tsinci kaina ne a wannan harka. Nakan tsinci kaina ina rera waka ko ina tafiya a kafa. Daga nan na fara rubutawa, daga baya na shiga cikin wannan harka gadan-gadan, inda a yanzu duniya ta san ni.
Ya zuwa yanzu ka kai kamar shekara nawa a harkar waka?
A yanzu ina da kamar shekara 11 da fara wannan harka, kuma bayan harkar waka ina daukar nauyin shirya fina-finan Hausa.
Shin za ka iya kiyasta yawan wakokin da ka yi?
 A gaskiya a yanzu ba zan iya cewa ga yawan wakokin da na yi ba, domin a lokaci daya idan na je daukar wakoki, nakan yi uku zuwa hudu.
Kamar wadanne wakoki kake ganin suka fitar da kai?
Wakokin da nake ganin suka fitar da ni su ne wakar ‘Mutanen Arewa Suna Kuka’ da wakokin Janar Muhammad Buhari na siyasa. Wadannan wakoki su ne suka fitar da ni a duniya. Ko taron kaddamar da takarar Janar Buhari da aka yi a kwanakin baya a Abuja, a duk mawakansa, ni kadai aka ba dama in fito gaban jama’a in yi masa waka a wajen  taron.
Wadanne nasarori ka cimma a harkar waka?
Na samu nasarori da dama a harkar waka. Babbar nasarar da zan ce na samu a wannan harka ita ce, na san mutane, kuma duk inda na je mutane suna dafifi don su gan ni, suna so su ga mawakin Janar Buhari, kuma a kullum suna yi mani addu’o’i.
Me ya sa ka mayar da hankalinka wajen yi wa Janar Buhari wakoki?
Ni dai ba ni da wata alaka da Janar Buhari. Ganin yadda jama’a suke dafifi a kansa saboda gaskiyarsa da rikon amana da son jama’a da son ci gaban kasa, sannan  ba ya nuna bambancin addini da kabilanci, wadannan dalilai ya sanya na rungumi yi masa wakoki. Kai a ’yan kwanakin nan ma da matata ta haihu na sanya wa dana sunan Janar Buhari, saboda kaunar da nake yi masa.
Mene ne babban burinka a harkar waka?
Babban burina in yi wakokin da za su taimaka Janar Buhari ya zama shugaban kasa.
Mene ne sakonka ga masu yi wa ’yan siyasa waka?
Sakona shi ne, mu rika fadar gaskiya a cikin wakokin da muke yi wa ’yan siyasa. Mu guji karbar kudinsu muna fadar karya. Domin ta sanadin wakokin da muke yi ake zabar wadansu ’yan takarar. Kuma mu guji cin mutuncin jama’a a cikin wakokinmu. Dole ne sai an yi siyasa da wakoki domin waka tana dauke da sakon da take isarwa.