Dalilin da rikicin zabe ya ki ci ya ki cinye wa a Najeriya
Shugabar Kotunan Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ce matsalolin matakan gudanar da zaben Najeriya ne silar rikice-rikicen zabe
Shugabar Kotunan Daukaka Kara ta Kasa Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta ce tarin matsalolin da matakan gudanar da zaben Najeriya ke da shi ne ummul’aba’isin rikice-rikicen a fannin.
Mai shari’a Dongban-Mense ta ce yiwuwar rikice-rikicen ce ta sanya aka kafa kotunan sauraron kararrakin zabe, don warware rigingimun zabe da dangoginsu.
Ta ce matukar ana son kawo karshen wadannan fitintinu, to dole sai an gyara tsarin zabe daidai da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da kuma Dokar Zabe ta 2022.
“A matsayin kotunan daukaka kara na matakin kusa da karshe a shari’a, aikinsu ne kafa irin wadannan kotunan da kuma bude wuraren rajista akalla sati daya kafin gudanar da zaben.
“Haka kuma alhakinsu ne kula da gudanarwar kotunan, bisa jagorancin mai mukamin sakatare”, in ji ta.
Ta bayyana hakan ne a jawabinta na bude taron kara wa juna sani na kwana biyu ga sakatariyar kotun zabe a jiya a Abuja.