Dalilin da Ronaldo bai haska a wasan Al-Nassr ba
Tauraron na Portugal ba zai taka leda a wasanni biyu da kungiyar za ta doka nan gaba ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta ce ta mutunta hukuncin Hukumar Kwallon Kafar Ingila FA kan sabon dan wasan da ta saya, Cristiano Ronaldo game da haramcin wasanni biyu da ke kansa.
Wani jigo a Al Nassr ya shaida wa AFP ranar Juma’a cewa, tauraron na Portugal ba zai taka leda a wasanni biyu da kungiyar za ta doka nan gaba ba, domin mutunta hukuncin.
- Za a iya samun bullar Covid-19 fiye da yadda aka fuskanta a baya —NCDC
- Chadi ta kame sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki
Bayanai sun ce Ronaldo dan kallo kawai ya zama yayin da kungiyarsa ta kara da Al-Tai a gasar Saudi Pro League a ranar Juma’a.
Sai dai duk da rashin haskawa a wasan, Ronaldo ya ja hankalin yayin magoya bayan kungiyar ta Al-Nassr suka rera sunan sabon tauraron nasu.
Ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba dan wasan na Portugal ya samu abin fara’a, inda a minti na 42 Anderson Talisca ya zura kwallon a raga.
An hasko Ronaldo yana yaba wa Al-Nassr kwallon farko da sabuwan kungiyarsa ta jefa, yayin da suke kokarin ci gaba da jan ragama a saman teburin gasar.
Tun a watan Nuwamba ne dai, hukumar FA ta dakatar da Ronaldo a wasanni biyu saboda samunsa da laifin tankwabe wayar salula daga hannun wani magoyin bayan Everton a lokacin da ya ke shirin daukar hotonsa bayan rashin nasarar Manchester United hannun Everton a Goodison Park.
Har zuwa yanzu dai Al-Nassr ba ta yi wa Ronaldo rijista ba, kasancewar kungiyar ta zarta adadin ‘yan wasa 8 da Hukumar Kwallon Kafar Saudiya ta sahale mata saye daga ketare duk kaka.
Zuwa yanzu dai Al-Nassr ta sayi ‘yan wasan da yawansu ya kai 9 daga ketare ciki har da Ronaldo da ta sayo kan yuro miliyan 200 bayan dan wasan gaban na Portugal ya raba gari da Manchester United ana tsaka da Gasar Kofin Duniya.
Kwantiragin dan wasan mai shekaru 38 zai kai shi har zuwa watan Yunin 2025.
Yanzu haka dai Al-Nassr na bukatar raba gari da dan wasa guda gabanin bai wa Ronaldo damar samun gurbi a kulob din yayin da ake jita-jitar yiwuwar kungiyar za ta rabu ne da Jaloliddin Masharipov don samun gurbin yi wa tauraron na Portugal da ya lashe Ballon d’Or sau 5 rijista.