Dalilin da shugaban NNPP ya koma APC a Gombe
NNPP na cika kunnuwan masu zabe da tatsuniya da karairayi.
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Gombe, Abdullahi Maikano Umar ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Wannan dai na zuwa ne yayin da rage kwanaki akalla 20 a gudanar da Babban Zabe na 2023.
- Real Madrid ta kara matse wa Barcelona lamba a teburin La Liga
- Dalilin da Abba Gida-gida bai je muhawarar ’yan takara gwamann Kano ba
Bayan ficewarsa daga jam’iyyar mai alamar kayan marmari, Maikano ya gana da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a Fadar Gwamnatin Jihar inda ya jaddada masa hadin kai da goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben da ke tafe.
Maikano ya ce rashin sanin makama a siyasance da shugabanci nagari ne dalilansa na ficewa daga jam’iyyar ta NNPP.
Da yake ci gaba da zayyana dalilansa na sauya sheka, Maikano ya ce shawarar da ya yanke ta komawa jam’iyyar APC ta samo asali ne a dalilin rashin gabatar da manufofi daga bangaren dan takarar gwamna a jam’iyyar Ahmed Khamisu Mailantarki.
Maikano ya yi zargin cewa dan takarar gwamnan ya gaza bayyana tsare-tsaren yadda zai tunkari yakin zabe har ya iya ciyar da Jihar Gombe gaba da magance kalubalen da take fuskanta idan aka zabe shi.
“Ba zan iya ci gaba da zama a inda karya da shaci fadi ke zama tushen yakin neman zabe da harkokin siyasa ba.
“Maimakon mayar da hankali kan taswira da tsare-tsaren magance matsalolin shugabanci da ci gaba.
“Na jima da fahimtar cewa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya shugaba ne mai hazaka da hangen nesa kuma mai fafutukar kawo ci gaba ga Jihar Gombe, tare da samar da kyakkyawan shugabanci ta yadda al’umma ke kwankwadar romon dimokuradiyya.
“Sannan idan aka duba jam’iyyar APC jam’iyya ce ta kamilallun mutane da kishin kasa, masu mai da hankali kan ci gaba maimakon cika kunnuwan masu zabe da tatsuniya da karairayi.”
Abudullahi Maikano ya kara da cewa a halin yanzu ’yan jam’iyyar NNPP da dama sun nuna sha’awar biyo shi zuwa jam’iyyar ta APC.
Kazalika, ya yi kira ga al’ummar Gombe da su mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya a kudurinsa na neman wa’adi na biyu domin ci gaban jihar.