Dalilin da shugabannin EFCC ba sa gamawa lafiya
Matsala ta farko ita ce yadda Fadar Shugaban Kasa ke amfani da EFCC don cim ma burinta na siyasa.
A ranar Alhamis din makon jiya ne Daraktan Ayyuka a Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Abdulkarim Chukkol ya zama Mukaddashin Shugaban Hukumar.
Abdulkarim Chukkol ya maye gurbin Abdulrasheed Bawa ne da Shugaba Bola Tinubu ya dakatar a matsayin shugaban hukumar don yin bincike a kansa.
- An ci direba tarar Naira miliyan 96 kan gudun wuce kima
- Dalilin da saura kiris Najeriya ta shawo kan matsalar tsaro — Buni
Chukkol, wanda Babban Jami’in Bincike ne a hukumar, zai ci gaba da jan ragamar hukumar zuwa lokacin da za a nada sabon shugaba.
Sanarwar dakatarwar ta ce, “Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da dakatar da Abdurasheed Bawa daga shugabancin Hukumar EFCC har sai abin da hali ya yi domin a samu damar bincikar sa a kan abubuwan da ya yi lokacin da yake shugabantar hukumar.
“Hakan ya biyo bayan wasu zarge-zarge masu nauyin gaske da ake yi masa. Ana umartar sa ya gaggauta mika ragamar shugabancin hukumar ga Daraktan Ayyukanta zuwa lokacin da za a kammala binciken.”
An dakatar da Bawa ne mako daya bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda shi ma ake bincikar sa.
Akwai zarge-zarge masu yawa a kan Abdulrasheed Bawa, amma na kwana-kwanan nan shi ne wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya yi inda ya zarge shi da neman cin hancin Dalar Amurka miliyan biyu, zargin da Bawan ya musanta.
Hukumar Tsaro ta SSS ta gayyaci Abdulrasheed Bawa bayan dakatar da shi, inda ba bata lokaci ya kai kansa ofishin na SSS.
Da wannan Bawa ya bi sahun magabatansa tsofaffin shugabannin Hukumar EFCC na baya, wadanda aka raba da shugabancinta a wani yanayi marar dadi.
Aminiya ta gano tunda aka kafa hukumar, dukkan shugabanninta ba sa rabu da ita lafiya ba.
Duk da cewa ana tantancewa tare da zabo wanda zai jagoranci hukumar, duk shugabannin da suka jagoranci hukumar da aka yi zuwa yanzu, suna karewa ne da zargin aikata ba daidai ba ko kuma wata dambarwa.
Daga lokacin da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya kirkiro EFCC zuwa yanzu, ta samu shugabanni biyar: Nuhu Ribadu da Farida Waziri da Ibrahim Lamorde da Ibrahim Magu sai kuma Abdulrasheed Bawa.
Nuhu Ribadu
Shi ne ya fara jagorantar hukumar bayan Obasanjo ya zabo shi daga Rundunar ’Yan sandan Najeriya a shekarar 2003 zuwa 2007, inda Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa ya cire shi.
Nuhu Ribadu ya yi ayyuka da dama na yakar cin-hanci inda har ya gabatar da shaidar Naira biliyan 15 a gaban kotu da wani Gwamna da ya yi kokarin sayensa domin dakatar da bincike a kansa.
Ya kuma bankado wasu manyan laifuffuka, amma daga karshe aka sauke shi kuma aka nemi a kama shi, har sai da ya tsere daga kasar nan. Sai dai an yi ta zarginsa da kasancewa karen farautar da Gwamnatin Obasanjo ke amfani da shi wajen gallaza wa wadanda suke takun-saka da ita.
Da farko Babban Sufetan ’Yan sanda na lokacin Mike Okiro ya umarci Ribadu da ya ajiye aikin EFCC domin ya halarci wani kwas na wucin-gadi na shekara daya a Kuru da ke Jihar Filato.
Mutane da kungiyoyi sun yi Allah wadai da matakin, amma a karshe Hukumar Kula da ’Yan sanda ta kore shi daga aiki, aka kuma cire shi daga mukaminsa, sannan aka fara nemansa ruwa-a-jallo kafin daga bisani ya tsere daga kasar nan.
Farida Mzamber Waziri
Bayan Nuhu Ribadu, marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa ya nada Farida Mzamber Waziri wadda ta shugabanci hukumar daga watan Mayu 2008 zuwa Nuwamba, 2011.
Nasarorin Farida wajen yaki da cin-hanci sun hada da kama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP mai mulki, bisa laifin rashin biyayya ga kasa da kuma badakalar kwangilar Naira biliyan 84, har kotu ta daure shi na wata 30.
Ta kuma kwato Naira biliyan 17 daga tsohon Sufeto Janar na ’Yan sanda, marigayi Mustapha Adebayo Balogun.
Sannan ta binciki tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu da na Ribas, Peter Odili da Joshua Dariye na Filato da Saminu Turaki na Jigawa da kuma Jolly Nyame na Taraba.
A yayin da take EFCC, Farida Waziri ta ce satar da wasu jami’an gwamnati ke yi na kamanceceniya da tabin hankali, inda ta bayyana takaicin cewa kotuna ba sa yanke musu hukunci.
Daga karshe, Shugaba Goodluck Jonathan ya sallame ta bisa zargin nuna son kai da zabar mutanen da take bincika.
Ta kuma yi ta samun sabani da Ministan Shari’a na wancan lokacin Muhammad Bello Adoke, wanda ya zarge ta da hana ruwa-gudu a binciken Gwamnan Bayelsa, Timipreye Sylva.
Ibrahim Lamorde
Ya ja ragamar EFCC daga watan Nuwamba, 2011 har ya kammala shekarunsa hudu, amma Shugaba Muhammadu Buhari bai ba shi damar zarcewa ba, shi ma dai ya hadu da matsala bayan saukarsa.
Ibrahim Magu
Shi ne wanda ake yi masa lakabi da mai rikon amana kuma marar tsoro wajen yaki da cinhanci.
Ya shugabanci hukumar a matsayin riko tun daga 9 ga Nuwamba 2015 har zuwa lokacin da aka dakatar da shi a ranar 7 ga Yulin, 2020.
Magu daya ne daga cikin jami’an bincike na farko da Nuhu Ribadu ya yi amfani da su wajen yakar cin-hanci.
An kuma yi masa lakabi da sarkin yakin yaki da cin hanci da rashawa na Gwamnatin Buhari.
Daga cikin binciken da Magu ya jagoranta a karkashin Ribadu akwai na Gwamna Bukola Saraki da na tsohon Gwamnan Jihar Delta James Ibori.
A shugabancinsa, EFCC ta kwace kadarori da kudaden badakala na biliyoyin Naira da miliyoyin Daloli da Fama-famai daga hannun tsofaffin jami’an gwamnati da masu ci da attajirai da ’yan siyasa.
Kazalika EFCC ta yi nasarar ganin kotu ta yanke hukuncin dauri ga wasu manyan mutane da ta kama da laifin satar dukiyar kasa da wasu shari’o’i da aka shafe shekaru ana yi.
Shi ma Magu an zarge shi da mayar da EFCC ’yar amshin gwamnati wajen takura wa ’yan adawa da kuma kawar da kai daga wasu fitattun zarge-zarge.
Bayan haka an sha zargin hukumar da gazawa wajen bincike da gabatar da gamsassun hujjoji domin yanke wa masu laifi hukunci, lamarin da ya sa hukumar ke yawan shan kaye a kotu.
Farida Waziri ta zargi Magu da boye takardun binciken wasu manyan mutane, inda ta sa aka binciki gidansa, amma ba a kama shi da wani laifi ba.
Daga nan aka mayar da shi hedikwatar ’yan sanda kafin daga baya a dakatar da shi daga aiki ba tare albashi ba.
Bayan Ibrahim Lamorde ya karbi Farida Waziri, ya nemi a dawo da Magu EFCC su yi aiki tare.
Amma da ya tura wa Babban Sufeton ’Yan sanda jerin sunaye da sunan Magu a ciki, sai aka cire sunan Magu, sai da Shugaban Kasa ya sa baki sannan aka dawo da shi.
Haka kuma Magu bai samu amincewar Majalisar Dattawa ba, sakamkon zarginsa da rashawa da Hukumar SSS ta yi a rahotonta ga majalisar.
An kuma zarge shi da mallakar kadarori a ciki da wajen Najeriya da suka zarce albashinsa.
Hakazalika, an yi ta samun takun-saka a tsakaninsa da Ministan Shari’a bisa zargin yin kafar ungulu a yakin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi da rashawa.
Daga karshe rahoton Ministan Shari’a Abubakar Malami ya sa an dakatar da shi bisa zargi 22 da ya gabatar wa Shugaban Kasa.
Rahoton ya ce, a dakatar da Magu ne domin samun damar gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da kudaden gwamnati da aka kwato daga wadanda suka wawure.
Yaki da cin-hanci da Magu ya yi a tsawon lokacin da ya kwashe a matsayin shugaba ya taba manyan mutane da dama.
Abin da ya sa shugabannin EFCC ba sai gamawa lafiya —Rafsanjani
Aminiya ta ji ta bakin Shugaban Kungiyar Hakkin Dan Adam ta CISLAC, Malam Auwal Musa Rafsanjani a kan wannan batu, inda ya ce matsala ta farko ita ce yadda Fadar Shugaban Kasa ke amfani da wannan ofishi na EFCC don cim ma burinta na siyasa ko ta musguna wa wasu da take ganin ba sa bayan gwamnati.
Ya ce, “Dalilin da ya sa muke ta kiraye-kirayen cewa yaki da cin -hanci ba wani abu ne da za a tsaya ana yaudara ko ana damfarar mutane da shi ba.
“Dole ne a kawo tsare-tsare a kawo wasu hukumomi wadanda za su yi aiki da gaskiya da adalci kuma a ba su dama ta yadda za su yi aikace-aikacensu ba tare da an yi musu katsalandan ko amfani da karfin siyasa ko karfin gwamnati a bata aikace-aikacen da suke yi ba.”
Ya ce irin wannan katsalandan tana raunana irin aikace-aikacen da EFCC ke yi.
Ya ce, idan jami’an Hukumar EFCC suka ce za su binciki na kusa da gwamnati ko wasu da ake ganin ’yan jam’iyyar gwamnati mai ci ne, shi ke nan sai a yi kutun-kutun ganin an cire shugaban, wanda a cewarsa hakan yana raunana hukumar da shugabanninta da suke son tsayawa su yi aiki a tsakaninsu da Allah, gudun kada a ci mutuncinsu ko kada a zarge su don sun taba shafaffu da mai da ke kusa da Shugaban Kasa ko na kusa da aminan Shugaban Kasa, inda ya ce hakan na daga cikin dalilan rashin gamawarsu lafiya, musamman idan har sun rufe ido sun taba wani na jikin Shugaban Kasa ko aminansa ko na jam’iyyar Shugaban Kasa.
A cewarsa, “Wadanda ake bincike a kan sata da cin-hanci sai kuma su juya su ce kai ne ma mai kashi a gindi.
“Saboda haka dole ’yan Najeriya su gane cewa idan ba su tashi tsaye sun kare mutuncin hukumomin yaki da cin-hanci ba, an daina amfani da su don siyasa, an daina amfani da su don a ci mutuncin wasu mutane wadanda ba lallai ne ma ana zarginsu da cin-hanci ba, to za a samu koma-baya wajen tabbatar da adalci da kawo tsabta da tsari da za su kawo gaskiya da tsari a Najeriya,” in ji shi.