Dalilin da sojoji ke samun nasarar juyin mulki — Janar Abdulsalami

An yi juyin mulki har sau biyar tun bayan da Nijeriya ta samu ’yancin kai a shekarar 1960 kawo yanzu.

Dalilin da sojoji ke samun nasarar juyin mulki — Janar Abdulsalami

Tsohon Shugaban Nijeriya, Janar Abdulsami Abubakar, ya bayyana cewa sojoji ba su da damar aiwatar da juyin mulki a kowacce ƙasa face sai sun samu gudunmawa daga ’yan siyasa.

Abdulsalami wanda shi ne shugaban mulkin soji na ƙarshe a Nijeriya, ya faɗi hakan ne a wata hira ta musamman da Jaridar The Sun ta wallafa a ƙarshen mako.

Ana iya tuna cewa dai a bayan nan an fuskanci juyin mulkin soji a wasu ƙasashe na Yammacin Afirka da suka hada da Burkina Faso, Nijar da Mali.

A bara ce dai sojoji suka yi wa Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum juyin mulki, wanda Janar Abdulsalami na ɗaya daga cikin wakilan Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da suka riƙa faɗi tashin ganin an yi sulhu da sojojin tare da mayar da mulkin hannun farar hula.

Wannan dai na zuwa bayan da ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar ɗin jerin takunkumai sanadiyar hawa kujerar naƙi da sojojin suka yi na mayar da mulki hannun farar hula.

Sai dai a lokacin da ECOWAS ta janye takunkuman da lafta wa ƙasar, tuni Nijar ɗin ta riga da ƙulla alaƙa da ƙasashen da su ma suka karɓe akalar jagoranci daga hannun gwamnatin farar hula.

A cikin hirarsa da Jaridar ta The Sun, tsohon Shugaban Kasar ya ce, “duk wani abu [juyin mulki] da ya faru, dole ne sai ’yan siyasa sun buɗe wa sojoji ƙofar aiwatar da hakan.

“Idan kana gwamnati amma ya zamana babu daidaito da adalci, to kuwa hakan zai buɗe ƙofa ta fuskantar matsaloli da ɓarna a ƙasa.

“Akwai jam’iyyun siyasa, amma kowacce jam’iyya mutum ya tsinci kansa a ciki a yanzu, zai tarar babu dimokuraɗiyya.

“Muddin hakan ta kasance dole a sa rai cewa za a fuskanci bore daga wasu ɓangarori, wanda idan ba a ɗauki matakin da ya dace ba, za a wayi gari sojoji sun karɓe akalar jagoranci.

“Kar a manta cewa babu wani soja da zai yi juyin mulki ba tare da gudunmawar ’yan siyasa da fararen hula ba.”

Alƙaluma na tarihi sun nuna cewa kawo yanzu an yi juyin mulki har sau biyar tun bayan da Nijeriya ta samu ’yancin kai a shekarar 1960.

Tun daga shekarar 1966 zuwa 1999, sojoji ne suka mulki Nijeriya ba tare da tsagaitawa ba in ban da mulkin farar hula na dimokuraɗiyya da aka samu na ɗan taƙaitaccen lokaci a Jamhuriyar ta Biyu tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania