Dalilin da su Jerry Gana suka fice daga PDP

Yayin da Jam’iyyar PDP ta fara yunkurin hade kan jam’iyyun adawa don fafatawa da Jam’iyyar APC a zaven badi. Wadansu jigogin jam’’iyyar da sukahada da tsofaffin ministoci Farfesa Jerry Gana da Farfesa Tunde Adeniran da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar tare da komawa cikin Jam’iyar SDP ta […]

Dalilin da su Jerry Gana suka fice daga PDP

Yayin da Jam’iyyar PDP ta fara yunkurin hade kan jam’iyyun adawa don fafatawa da Jam’iyyar APC a zaven badi. Wadansu jigogin jam’’iyyar da sukahada da tsofaffin ministoci Farfesa Jerry Gana da Farfesa Tunde Adeniran da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar tare da komawa cikin Jam’iyar SDP ta Cif Olu Falae.

Sababbin hujjoji da wata majiya ta samu  da ke da alaka da Jam’iyyar PDP sun bayyana cewa jiga-jigan ’ya’yan PDP din sun fice ne daga jam’iyyar saboda sun fusata a kan dan takararsu  ba samu nasara a zaven shugabancin jam’iyar ba a babban taron da ta gudanar. Ya shaida wa majiyar cewa: “Sun dade suna jujjuya akalar jam’iyyar. Sun saba su suke tafiyar da ita don haka suna mamakin yadda aka yi waje da su.” Ya kara da cewa ba mu damu ba sabowa wadansu daga cikin wadanda suka bar PDP suka koma SDP ba su tava cin koda zaven kansila ba ko kowane mukami tun daga 1999. Suna zaune a Jam’iyyar PDP ne kamar kaska. Suna cin gajiyarta amma sai suka yi watsi da ita, wannan ya sa sunansu ya dada tambari.                                                           

 Sauran wadanda suka fice daga PDP din suna hada da tsohon Kantoman Mulkin Soja na Jihar Katsina, Sanata Joseph Akaagerger da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa lokacin mulkin Cif Goodluck Jonathan, Cif Mike Oghiadhome da tsohon Ministan Tsaro Dokta Olu Ogunloye da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Jihar Ondo, Dare Emiola. Sauran sun hada da Dokta Junaidu Mohammed da Sanata Bassey Ewa Henshaw da Alhaji Shehu Gabam da shugabannin  kungiyar Mutanen Tsakiyar Najeriya da sauransu. Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ce, vangaren na PDP a karkashin Jerry Gana da Shugaban Jam’iiayr SDP, Cif Olu Falae suka sanya hannu a kan takardar amincewa su yi aolo tare domin tabbatar da wasu kudirori da suka hada da sake fasalin zamantakewar tarayya da tabbatar da ’yanci da al’ummar da ta ginu kan dimokuradiyya da ingantaccen shirin farfado da tattalin arziki mai kazar-kazar da tabbatar da adalci da daidaito da zaman lafiya da kuma  al’adar samar da shugabanni nagari ta hanyar sanya ido yadda ya kamata. Wata majiyar SDP ta ce Gangamin Obasanjo ya bukaci ya tuntuve ta inda suke sa ran haifar da da mai ido.