Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa
Ƙudirin bai bayyana cewa jami’ar tana da hurumin da za ta riƙa bayar da shaidar karatun digiri ba
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata.
- Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani
- HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja
Wasiƙar shugaban ta kare matakin da ya ɗauka na ƙin amincewa bisa la’akari da tanadin da sashe na 22 da ke cikin ƙudirin kafa jami’ar ya yi.
Ya yi bayanin cewa sashen ya yi tanadin cewa filin da za a gina jami’ar zai kasance a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Jihar Adamawa wanda ya saɓa wa ƙa’idar kasancewa a ƙarƙashin ikon Gwamnatin Tarayya.
Kazalika, wasiƙar ta Shugaba Tinubu ta kafa hujjar cewa sashe na 25 (b) da ke ƙunshe a cikin ƙudirin bai bayyana cewa jami’ar tana da hurumin da za ta riƙa bayar da shaidar karatun digiri ba.
Idan ba a manta ba, a shekarar da gabata ce Majalisar Wakilan ta amince da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Numan da ke Jihar Adamawa kuma ta miƙa wa shugaban ƙasar domin neman sahalewarsa.