‘Dalilin da Tinubu ya yi wa dukkanin Jakadun Najeriya kiranye’
Kiranyen bai shafi jakadun Najeriya na Majalisar DInkin Duniya ba.
Fadar Shugaban Kasa ta zayyana dalilin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa dukkanin jakadun kasar kiranyen dawowa gida Najeriya.
A Yammacin wannan Asabar din ce Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya sanar da yi wa dukkanin manya da kananan jakadun kasar kiranye ba tare da fadin dalili ba.
- Ba za mu janye dokar hana dalibai mata sanya abaya a makarantu ba — Faransa
- KAROTA ta kama jabun magunguna na Naira miliyan 50
Yusuf Tuggar ya ce an yi wa duka jakadun kiranye ne bisa umarnin Shugaba Tinubu.
“Jakadu a matsayinsu na wakilan ƙasar, suna aiki ne da umarnin shugaban ƙasa, domin kuma shi ne ke da ikon aikawa da mayar da jakadun zuwa ga kowacce ƙasa,” kamar yadda sanarwar Ma’aikatar Harkokin Kasashen ƙasashen wajen ta bayyana.
Tun da farko shugaba Tinubu ya dawo da Jakadan Najeriya a Birtaniya Ambasada Sarafa Tunji Ishola wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a watan Janairun 2021.
Cikin takardar umarnin mayar da jakadan, Yusuf Tuggar ya ce “ina amfani da wannan dama wajen bayyana godiyar Shugaban Kasa bisa aikin da ka yi a matsayin Jakadan Najeriya a Birtaniya.”
Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Cif Ajuri Ngelale, ya ce Tinubu ya yi wa jakadun kiranye ne a matsayin wani yunkuri na tabbatar da ajandar gwamnatinsa ta kawo sauyi a Najeriya da ake yi wa lakabi da Sabunta Fatan ’Yan Kasa wato ‘Renewed Hope Agenda’.
Kazalika, sanarwar ta ce kiranyen bai shafi wakilan Najeriya na Majalisar Dinkin Duniya ba da ke birnin New York na Amurka da kuma na birnin Geneva da ke kasar Switzerland, “bisa la’akari da taron Majalisar Dinkin Duniya mai zuwa, wanda za a yi a karshen wannan watan.”