Dalilin da ya dace a gaggauta kama Wike — Edwin Clark

Babu wanda ya fi ƙarfin doka kuma dole ne doka ta ɗauki mataki kansa.

Dalilin da ya dace a gaggauta kama Wike — Edwin Clark

Ɗaya daga cikin dattijan ƙasa kuma jagora a yankin Neja Delta, Edwin Clark, ya yi kira ga babban sufeta janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun da ya damƙe Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Clark ya yi wannan kiran ne a matsayin martani kan kalaman da Wike ya yi kan jihohin da gwamnonin jam’iyyar PDP ke iko da su, bayan ziyarar da suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas.

A cewar Gwamnonin PDP bayan taron nasu sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Fubara a matsayin shugaban jam’iyyar a Jihar Ribas.

Gwamnonin sun kuma yi alƙawarin haɗa kai da kwamitin zartarwa na jam’iyyar domin tabbatar da ganin gwamnan ya samu damar ɗaukaka siyasarsa a jihar.

Sai dai Ministan Abuja, Wike wanda shi ne tsohon gwamnan Ribas, ya yi barazanar dagula al’amura ga duk gwamnan da ya tsoma baki a harkokin siyasar cikin jihar.

Da yake bayyana damuwa kan lamarin, Clark a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya aike wa Egbetokun a ranar Alhamis mai taken ‘A gaggauta kama Wike’, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya bari dangantakarsa da Wike ta kawo cikas ga muradun ƙasa.

Ya tunatar da Sufeto Janar ɗin muhimmancin kiyaye tsarin mulki na bin doka da oda ba tare da nuna ɓangaranci ba.

Clark ya jaddada cewa barazanar Wike ba wai tana kawo haɗari ga zaman lafiyar jama’a ba ne kawai, har ma da tayar da hankali, wanda ke zama babban laifi a ƙarƙashin dokokin Nijeriya.

Ya ce: “Babu wanda ya fi ƙarfin doka kuma dole ne doka ta ɗauki mataki kansa.

“Idan a baya za ku iya kama Omoyele Sowore a dalilin irin wannan barazana mai dagula zaman lafiyar jama’a. Sannan kuma a halin yanzu da ake shirin gurfanar da mutanen da suka halarci zanga-zangar tsadar rayuwa. Mene ne amfanin jinkirin ɗaukar mataki kan wannan batu na Wike?

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos