Dalilin da ya hana ’yan Najeriya samun bizar Umarah — Hukumar Alhazai

Muna ƙoƙarin ganin an shawo kan wannan matsala ta rashin bizar Umarah da ’yan Najeriya ke nema.

Dalilin da ya hana ’yan Najeriya samun bizar Umarah — Hukumar Alhazai

Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ta bayyana cewa saba wa ka’idar bizar da Saudiyya ta ba su ce dalilin da ya hana ’yan Najeriya da dama samun damar tafiya Umarah a wannan wata na Ramadana. 

Aminiya ta ruwaito cewa da dama daga cikin ‘yan Najeriya da suka ɗauki niyyar tafiya kasa mai tsari domin yin Umarah a wannan wata na Ramadana sun fuskanci matsalar samun biza.

Cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulɗa da jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa an ware bizar Umrah ne bisa ƙa’idar adadin da bizar da ake bai wa ƙasashe wanda kuma sanin kowa ne cewa ta Ramadan yawanci ya fi tsada.

Ta bayyana cewa Saudiyya ta tsawaita wa’adin bizar zuwa kwanaki 90, inda ’yan Najeriya da dama suka mallaki tasu bizar a kan farashi mai rahusa tun a lokutan baya tare da sa ran gudanar da aikin Umrah a cikin watan Ramadan.

Hajiya Usara ta ce “Waɗannan mutane sun yi amfani da tsawaita wa’adin bizar da Saudiyya ta yi domin su tsawaita zamansu a ƙasa mai tsarki ko kuma su riƙe bizar ba tare da amfani da ita ba har zuwa watan Ramadan, wanda wannan ne dalilin da ya haifar da ƙarancin samun biza ga sauran ‘yan Najeriya.”

Usara ta kuma bayyana cewa, yawan masu neman bizar Umrah a watan Ramadan ya ƙara tsananta ƙarancinta a wannan lokaci.

“Ya zuwa yanzu, biza kaɗan ake samu daga lokaci zuwa lokaci wanda ya danganta adadin ’yan Najeriya da ke buƙatar bizar.”

Sai dai ta ce ana ƙoƙarin ganin an shawo kan lamarin domin jami’in hulɗa da jama’a na Saudiyya ya tattauna da ma’aikatar Hajji da Umrah kan lamarin.

“Duk da cewa tattaunawar ta kasance mai ma’ana, amma ya tabbatar da cewa rabon bizar an yi amfani da tsarin na’ura mai kwakwalwa.”