Dalilin da ya sa ake yi mini lakabin ‘Mai Ma’asuma’ –Muhammad Sani
Malam Muhammad Sani Bello yana daya daga cikin Sha’iran da ke yi wa Annabi Muhammad da Iyalansa yabo. Yana zaune a Minna babban birnin Jihar Neja, ya share fiye da shekara 16 yana yabon har ta kai ake yi masa lakabi da ‘Mai Ma’asuma’. Ga yadda hirarsu ta kasance da Wakilin Aminiya: Aminiya: Me ya […]
Malam Muhammad Sani Bello yana daya daga cikin Sha’iran da ke yi wa Annabi Muhammad da Iyalansa yabo. Yana zaune a Minna babban birnin Jihar Neja, ya share fiye da shekara 16 yana yabon har ta kai ake yi masa lakabi da ‘Mai Ma’asuma’. Ga yadda hirarsu ta kasance da Wakilin Aminiya:
Aminiya: Me ya ba ka sha’awar wannan wakar da ka dade kana yi?
Mai Ma’asuma: Wannan tambaya ce babba. Babban dalilin da ya sa na rungumi yabon Annabi Muhammad (SAW) da Iyalan gidansa shi ne, umurni daga Allah Madaukakin Sarki wanda ya bayar da umurni a alkur’ani Mai Girma, inda ya nuna Shi kanSa da Mala’ikunSa suna yi wa Annabi Salati, sannan Ya umurci wadanda suka yi imani su yi masa salati. Shi ma Annabi Muhammad (SAW) ya nemi Musulmi su koya wa ’ya’yansu abubuwa guda uku. Na farko, son Annabi da karatun alkur’ani da kuma son Iyalin gidansa. Ka ji hujjoji na da na dogara nake wannan al’amarin.
Aminiya: Wace kasida ce ta sa ka yi fice?
Mai Ma’asuma: Gaskiya kasidar da ta sa na yi fice ita ce wakar ‘Ma’asuma’. Abin da ya sa na gaya maka haka shi ne, na yi kasidu da dan dama kuma suna shiga kasuwa ana sayensu fiye da yadda kake tunani. Da na fitar da wakar ‘Ma’asuma’ kasuwa, ni kaina na ga bambanci, don kuwa nan da nan faya-fayan ke karewa. Sanadiyyar wannan faifan na sa kafa a baki dayan jihohin shiyyar Arewacin kasar nan da wasu na kudanci. Ba a tsaya a nan ba, na samu gayyata zuwa kasar Benin da Kamaru da Chadi da Ghana da Togo da Nijar, inda na yi yabon Annabi Muhammad (SAW) da ’ya’yansa musamman Nana Fatimah.
Aminiya: Ka sanar da mu wasu daga cikin nasarorin da ka samu
Mai Ma’asuma: Babbar nasarar da nake ganin na samu daga lokacin da na fara wannan al’amarin zuwa yanzu shi ne daukakar da na samu a cikin lokaci kankane. Jama’a da dama suna gayyata ta hatta a wuraren bukukuwa na kusa da nesa. Akasari mutanen da suka saurari kasidata suna so a gayyace ni in rera musu suna ganina ido da ido. Daga wannan album na ‘Ma’asuma’ ne na yi sallama da talauci baki daya. Wannan ya yi sanadiyyar da na mallaki filin da nake aikin gininsa. A dalilinsa ne na yi auren da ya sama mini ’ya’ya uku wadanda biyu mata ne, kuma duk sunayensu Fatimah. Lokuta da dama mutane kan turo mini sakonnin kudi ban san iyaka ba, bayan wasu ihsanin da har yanzu ake ci gaba da yi mini.
Aminiya: Wadanne matsaloli ne ka fuskanta a duk tsawon wannan lokacin da kake yabon?
Mai Ma’asuma: Matsala ta farko dai da ni na fuskanta ita ce mummunar fasarar da mutane suka yi wa lamarin daga lokacin da na fara zuwa yanzu. Maimakon su yi tambaya a sanar da su duk abin da ya shige musu duhu, ba su yi haka ba. Ina son mutane su yi la’akari da abu daya, wato su san cewa jahili ba ya waka, kuma ko ya yi, ba za ta samu karbuwa ba kowace iri ce ya sa a gaba.
Aminiya: Mene ne babban burinka?
Mai Ma’asuma: Babban burin da nake son in cika shi ne, in ci gaba da wake iyalan gidan Annabi Muhammad musamman Nana Fatimah har in koma zuwa ga Mahaliccina.