‘Dalilin da ya sa ba za a kara rage farashin mai a Najeriya ba’
Hukumar kayyade Farashin Man Fetur ta kasa (PPPRA) ta ce ba za a rage farashin man fetur kasa da Naira 87 ga kowace lita ba sakamakon yanayin da kasuwar mai ta samu kanta a ciki.Babban Sakataren hukumar Mista Farouk Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani a Abuja […]

Hukumar kayyade Farashin Man Fetur ta kasa (PPPRA) ta ce ba za a rage farashin man fetur kasa da Naira 87 ga kowace lita ba sakamakon yanayin da kasuwar mai ta samu kanta a ciki.
Babban Sakataren hukumar Mista Farouk Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ’yan jarida bayani a Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce a yanzu ba a fahimci inda kasuwar mai ta sa gaba ba duk da cewa farashin ya fara hauhawa, amma duk da haka ba za a rage farashin mai a Najeriya ba.
Ahmed ya ce a watan Janairu ana sayar da kowace gangar mai a kan Dala 47, inda a yanzu kuwa ake sayar da ita a kan Dala 56.
Ya tabbatar da cewa a yanzu gwamnati na biyan Naira 11 ga kowace litar mai a matsayin tallafi. “Don haka idan wani ya yi dakon mai dinsa daga kasashen ketare jiya (Asabar) ya kuma kai kasuwa a Najeriya bayan kamar kwana 40, to za mu biya shi Naira 11 ga kowace lita a matsayin tallafi.”
Ya ce “wadannan batutuwa muke la’akari da su, don haka idan aka ce mun rage farashin mai fiye da Naira 10, ya zama dole gwamnati ta rika biyan Naira 30 ga kowace lita a matsayin kudin tallafi.”
Ya ce ’yan Najeriya suna biyan Naira 87 ga kowace lita a lokacin da kowace gangar mai take Dala 50, don haka duk abin da ya haura haka to gwamnati ce take cike gibin, wato kudin tallafi ke nan.
Batun ko a cire dokar da ke kula da farashin man fetur sai ya ce, ba zai yi magana a madadin gwamnati ba, amma yana da masananiyar gwamnati za ta yi nazari a kan dukkan abubuwan da suka dace kafin ta yanke shawara a kan batun janye tallafin mai.
Duk da halin da kasuwar man fetur ta shiga amma farashin man dizel da na jirgin sama na kara hauhawa.
“Tun da gwamnati ta tsame hannunta daga batun man dizel da makamantansa ’yan kasuwa sai sun shiga sun fita don su samo Dala, inda kuma kudinta ya fi na yadda Babban Bankin Najeriya yake sayarwa.
“Yawaitar bukatar Dala zai sa ’yan kasuwa su kasa rage farashin kayayyakinsu. Misali, tun da har yanzu gwamnati tana da hannu wajen hada-hadar mai a kasar nan, don haka ya sa dole Babban Bankin Najeriya ya nemo Dala a kan Naira 167 ga kowace Dala.” Inji shi.