Dalilin da ya sa golan United De Gea bai koma Madrid ba
A yayin da magoya bayan kulob din Manchester United da ke Ingila suke farin cikin golansu Dabid De Gea bai canza sheka zuwa Madrid na Sifen ba, su kuwa takwarorinsu na Real Madrid sun shiga bakin ciki ne bayan ciniki a tsakanin kulob din biyu bai kaya ba bayan an rufe kasuwar saye da kuma […]

A yayin da magoya bayan kulob din Manchester United da ke Ingila suke farin cikin golansu Dabid De Gea bai canza sheka zuwa Madrid na Sifen ba, su kuwa takwarorinsu na Real Madrid sun shiga bakin ciki ne bayan ciniki a tsakanin kulob din biyu bai kaya ba bayan an rufe kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.
Shi dai De Gea, golan kulob din Manchester United na Ingila, kulob din Madrid ya dade yana zawarcinsa musamman a kakar wasan da ta wuce. Da yawa daga cikin masoya harkar kwallon kafa sun yi hasashe golan zai koma Madrid kafin a rufe kakar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.
Rahoton da kafar watsa labarin wasanni ta Sky Sport ta kalato ya nuna ya zuwa ranar Litinin da ta wuce da yamma kungiyoyin biyu sun cimma matsaya a kan De Gea a farashin Yuro miliyan 40 sannan da sharadin da za a hada cinikin da golan Madrid na yanzu Keylor Nabas amma zuwa washegari watau ranar Talatar da ta wuce da safe sai al’amarin ya lalace.
Dalilin da ya sa yarjejeniyar canza shekar dan kwallon ba ta yiwu ba shi ne sai bayan an rufe kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallo da kusan minti 30 ne sannan Madrid ta samu takardun yarjejeniyar daga wajen jami’an kulob din United.
Sai dai yayin da jami’an United suka dage kai da fata sun aika da takardun yarjejeniyar a kan lokaci, su kuwa na Madrid sun tabbatar ba su ga takardun ba sai bayan minti 30 da rufe kasuwar da hakan ya sa tilas aka fasa cinikin. Haka shi ma wani masani kuma mai yin sharhin wasan kwallon kafa a Sifen mai suna Guillem Balague ya tabbatar cewa jami’an kulob din Madrid ba su karbi takardun yarjejeniyar a kan lokaci ba.
Jaridar Marca da ake wallafawa a Sifen ta ce za a ci gaba da cinikin ne a watan Janairun badi a lokacin da za a sake bude kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallon. Don haka Dabid De Gea dai zai cigaba da yi wa kulob din Manchester United kwallo ne har zuwa watan Janairun badi.
Idan za a tuna kocin Manchester United Luis baan Gaal ya daina sanya golan a wasa ne har sai bayan ya ga yadda cinikin dan kwallon za ta kaya da kulob din Madrid.