Dalilin da ya sa gwamnatin Oyo ta dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajj

Gwamman Jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya bayyana cewa sun dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajji saboda wasu dalilai. Ajimobi ya ce wannan dakatarwar ba ta shafi wadanda za suje aikin ne domin su taimakawa mahajjata wato ma’aikatan lafiya. Gwamnan ya fadi haka ne a ranar litinin a cikin jawabin bankwana da ya yi […]

Dalilin da ya sa gwamnatin Oyo ta dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajj
Dalilin da ya sa gwamnatin Oyo ta dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajj

Gwamman Jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya bayyana cewa sun dakatar da daukar nauyin mutane zuwa aikin Hajji saboda wasu dalilai.
Ajimobi ya ce wannan dakatarwar ba ta shafi wadanda za suje aikin ne domin su taimakawa mahajjata wato ma’aikatan lafiya.
Gwamnan ya fadi haka ne a ranar litinin a cikin jawabin bankwana da ya yi wa maniyyata aikin hajji na bana a masaukin Alhazai na Olodo dake Ibadan.
Ya ce saboda haka gwamnatin Jihar ta dauki nauyin mutane “31 ne kawai a matsayin jami’ai da za su je kasar Saudiya domin lura da ayarin Alhazai guda dubu 1 da dari 242 da za su yi aikin hajjin bana daga Jihar Oyo.”
Gwamnan ya ce gwamnati ta dakatar da biyan kudaden kujerun aikin hajji ga mutane barkatai da aka saba yi a baya ne “saboda wasu dalilai masu karfi da suka shafi tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.”
Gwamnan ya nemi dukkan maniyyatan jihar da su tabbatar da cewa, sun kiyaye dokokin kasar Saudiya. Ya roki cewa kada su yi abinda zai iya janyo wa Najeriya sunanta ya baci a idan duniya. Ya roki maniyyatan da su girmama aikin da suka je yi domin yana daya daga cikin shika shikan addinin musulunci guda biyar “a matsayinku na wakilai daga Jihar Oyo, idan kun isa kasar Makka ku tabbatar da cewa kun yi amfani da wannan dama wajen rokon Allah (SWT) ya kawo zaman lafiya a Jihar Oyo da kasa baki daya.”
Shi kuwa shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Oyo, Alhaji Taofeek Akeugbagold, ya nuna matukar farin cikinsa ne da irin yadda maniyyatan bana daga Jihar suka rinka amsa kiran hukumar musamman wajen halartar tarukan lacca da aka yi musu a lokuta daban-daban domin ilmantar da su a game da muhimman abubuwa da suka shafi irin yadda maniyyaci zai gudanar da aikin hajji.
Ya ce, a dalilin matakin da kasar Saudiya ta dauka na hana yin aikin hajji ga mata masu dauke da juna biyu, “a bana babu wata mace mai juna biyu da hukumar Alhazai tayi mata rajista domin mun gudanan da binciken kwakwaf ga mata maniyyata da muka tabbatar basu shiga cikin ayarin maniyyatan bana ba.”