‘Dalilin da ya sa gwamnonin APC ba su damu da barazanar tsige Fubara ba’
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnonin jam’iyyar APC sam ba su damu da yunkurin tsige Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ba, saboda batun yana gaban kotu.
Gwamnan Jihar Ribas Fubara
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce sam gwamnonin APC ba su damu da yunkurin tsige Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ba, saboda batun na gaban kotu.
Sule ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis a cikin shirin siyasa na Politics Today da tashar talabijin ta Channels ta watsa.
- Kotu ta ba Yahaya Bello damar tafiya Umara a watan azumi
- Mata da miji sun yi garkuwa da kansu, sun karbi N10m a matsayin kudin fansa
Da yake amsa tambayoyi kan ko gwamnonin APC sun damu da yiwuwar tsige ɗaya daga cikinsu, da kuma ko akwai wani mataki na shiga tsakani, Sule ya ce tsarin tsige gwamna yana bin matakan doka da oda ne.
“Ba na damuwa saboda al’amari ne da yake gaban kotu. Ba za ka iya tashi kawai ka tsige gwamna ba, ba tare da bin tsarin doka ba,” in ji shi.
Gwamnan ya ƙara da cewa duk da cewa gwamnonin suna kula da abin da ke faruwa da abokan aikinsu, babu wani dalilin gaggawa da zai sa a ɗauka cewa za a tsige Gwamna Fubara.
“Tabbas, duk abin da ya faru da kowanne daga cikinmu yana da muhimmanci, amma ba mu damu sosai har mu ɗauka cewa za a tsige Gwamna Fubara ba,” in ji Sule.
Ya ƙara da cewa matakan shari’a da na kundin tsarin mulki suna fayyace hanyoyin magance lamarin.
“Daga dukkan alamu, matakai suna gudana. Kotuna suna yanke hukunci, kuma Babban Alkalin jihar ya ɗauki matsayi. Saboda haka ba mu damu ba,” in ji shi.
A halin da ake ciki dai, sabon yunƙurin tsige Gwamna Fubara ya tsaya cak sakamakon ƙalubalen shari’a da na tsarin aikin ’yan majalisar.
A ranar 23 ga Janairu, 2026, Babbar Kotun Jihar Ribas da ke Oyigbo ta dage shari’ar tsige gwamnan har sai abin da hali ya yi, inda ta ce dole ne Kotun Daukaka Kara ta fara yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen da Kakakin Majalisa da wasu ’yan majalisar jihar suka shigar.
Wannan hukunci ya dakatar da ci gaba da shari’ar tsige gwamnan.
A wani mataki, Alkalin alkalan jihar Ribas, Mai Shari’a Simeon Amadi, ya ƙi kafa kwamitin bincike, yana mai cewa akwai umarnin kotu da kuma ka’idar cewa bai kamata kotu ta shiga cikin al’amuran da ake shari’a a kansu ba.
Wannan shi ne yunƙurin tsige Gwamna Fubara na uku cikin ƙasa da shekaru uku.
’Yan majalisar jihar dai sun zarge shi da aikata manyan laifuka, ciki har da kin gabatar da kasafin kuɗi, kashe kuɗaden gwamnati ba bisa ka’ida ba, riƙe kuɗin’yan majalisa, da kuma rushe ginin majalisar a shekara ta 2023.