‘Dalilin da ya sa har yanzu Arewa ke baya wajen rungumar fasahar zamani’

Shugabar cibiyar fasaha da kirkire-kirkire ta farko da mace ta mallaka a Arewacin Najeriya, wato Blue Sapphire Hub, Maryam Gwadabe, ta bayyana damuwarta kan

‘Dalilin da ya sa har yanzu Arewa ke baya wajen rungumar fasahar zamani’

Shugabar cibiyar fasaha da kirkire-kirkire ta farko da mace ta mallaka a Arewacin Najeriya, wato Blue Sapphire Hub, Maryam Gwadabe, ta bayyana damuwarta kan yadda yankin Arewacin Najeriya ke ci gaba da zama koma-baya wajen rungumar fasahar zamani.

Ta ce duk da cewa mutane da dama suna da manyan wayoyin, amma ba sa amfani da su yadda ya kamata don inganta rayuwarsu ta yau da kullum.

Shugabar kamfanin ta bayyana hakan ne a yayin bikin bajekolin fasahohin zamani da cibiyar ta shirya a matsayin wani bangare na shirin Bunkasa Amfani da Fasahohin Zamani a Arewacin Najeriya (ADAN) da aka gudanar a Kano a ranar Asabar.

Ta ce, “Mafi yawanmu muna da wayoyin zamani, amma muna amfani da su ne kawai don hawa TikTok ko Instagram. Rungumar fasaha na nufin amfani da wadannan kayan aiki don sauya rayuwarmu, kasuwancinmu da kuma al’ummarmu.”

Ta kara da cewa, “Wannan bikin yana nuni da abin da zai iya yiwuwa. Kira ne ga Arewacin Najeriya da ya zama mai kirkire-kirkire, mai fasaha, da kasuwanci.”

Shugabar kamfanin fasahar ta kuma bukaci al’umma da su daina zama masu kallon fasaha kawai, su koma masu amfani da ita wajen shiga tattalin arzikin zamani, tare da jaddada cewa dole ne yankin ya koyi yadda zai yi amfani da kayan fasaha don kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arzikinsa.

Shi ma a nasa jawabin yayin taron, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce jihar ta sake bude manyan makarantun koyon sana’o’i guda 26 da aka rufe a baya, domin bukatun al’ummar jihar.

Gwamnan, wanda shugaban na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano (KASITDA), Bashir Abdu Muzakkar, ya wakilta, ya ce jihar na da kudurin tabbatar da cewa matasa, wadanda ya ce su ne kaso 65 cikin 100 na yawan jama’ar jihar, sun shirya don cin moriyar damarmakin karni na 21.

Cibiyar Blue Sapphire Hub ce dai ta shirya taron tare da tallafin UK International Development, inda daruruwan matasa suka halarta, kuma aka nuna fasahohin sabbin kamfanoni musamman a bangaren fasahar sadarwa da tattalin arzikin zamani.