Dalilin da ya sa hukumarmu ta bai wa Noman Kashu muhimmanci – Dakta Ibrahim Doko
Aminiya: Mu fara da jin tarihin wannar hukuma da kuma aikace-aikacenta? An kafa wannar hukuma ne a Shekarar 1987 sannan ta fara aiki gadan-gadan a shekara ta 1988. Makasudin kafata shi ne ta habbaka samar da sinadaran da masana’antun kasar nan za su bukata don gudanar da ayyukansu daga nan gida a maimakon a rika […]
Aminiya: Mu fara da jin tarihin wannar hukuma da kuma aikace-aikacenta?
An kafa wannar hukuma ne a Shekarar 1987 sannan ta fara aiki gadan-gadan a shekara ta 1988. Makasudin kafata shi ne ta habbaka samar da sinadaran da masana’antun kasar nan za su bukata don gudanar da ayyukansu daga nan gida a maimakon a rika shigo da na waje, hakan zai sa kayan da su ke samar wa ya samu cikin saukin farashi. kasar nan na kashe makudan kudi wajen shigo da kayan da masana’antu ke bukata daga waje, inda hakan ke rage ayyukan yi da kuma nakasa tattalin arzikinta. Haka nan hukumar na bada gudunmowar ne ta hanyan aiwatar da nazari akan abubuwan da masana’antun ke bukata da kuma yadda za ta saukake masu su same shi daga nan gida idan akwai shi. Wannan ya hada da ma’adinai da amfanin gona da dai sauransu, irin shuka da mu ke da shi da kuma yadda za a inganta shi don samun amfani mai yawa. A dalilin hakan hukumar ta kakkafa wuraren gwaji da koyar da dabarun neman sinadaran ga masu sana’ar cikin sauki ta hanyan amfani da na’urorin zamani.
Aminiya: A bangaren noma, harkar Kashu na daya daga cikin wurare da ku ka baiwa muhimmaci a aikace-aikacenku. Shin me ya karfafa maku gwiwa akan hakan?
Kashu na daya daga cikin ’ya’yan itatuwa da masana’antu ke bukata dake samar da kudi da kuma taimakawa mahalli wajen kara masa inganci ta hanyan magance zaizayar kasa ko koma yakar hamada. Sannan za a iya shuka shi a yankunan Jihohin Najeriya kamar 27 a matakin kasuwanci ba na dan biyan bukata kawai ba, saboda yanayin jure fako da ya ke da shi, haka nan inda ake da yawan ruwa, abu guda da bai jurewa shi ne waje da ke da yanayin fadama. Ya na samar da biliyoyin kudin shiga ga masana’antunmu a nan gida da kuma ta hanyar fitar da shi zuwa kasashen waje. Bayan nazari a kan irin da a ke shukawa a kasar nan na tsawon shekaru aru-aru, hukumar nan ta gano cewa irin da yawanci a ke shukawa baida yabanya mai yawa ga kuma kankanta baya ga tsawon lokaci da yake dauka kafin a fara cin gajiyarsa. A dalilin hakan hukumar nan tare da abokan huldarta kamar cibiyar bincike akan Koko dake Ibadan ta shigo da wani iri mai inganci daga kasar Brazil da ake kira “Brazil Jumbo Size” wanda ke da manyan kwara da kuma naman kansa sannan kuma cikin shekara biyu ya fara zuba ’ya’ya sabanin irin da mu ke da shi, dake kai har shekara hudu kafin ya fara. Hakan ya sa adadin ’ya’yansa da ake samar wa a duk shekara ya karu sosai, idan aka yi la’akari da baya. An raba wannan iri wajen kwaya 7,000 a lokacin noma na shekara ta 2015 da kuma 2016 wanda wani kamfani ya aiwatar a madadin hukumarmu, inda wasu gidan gonakai su ka amfana daga tsarin.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne ake yi da kashu da manomansa za su ci gajiyarsa sosai idan sun sarrafa shi?
Manomi zai ribatu sosai da kashu da ya ke samarwa a gonarsa idan ya sarrafa shi kuma a dalilin hakan hukumar nan ta shiga wani tsarin hadin gwiwa da Jami’ar Jihar Kogi dake garin Ayingba daya daga cikin wurare da a ka fi noma shi, da kuma Jami’ar Habbaka Ayyukan Noma ta Tarayya dake Abeokuta na Jihar Ogun, inda su ka samar da na’uran sarrafa sinadaransa don cin cikakken gajiyarsa a maimakon safarar kwararsa zuwa kasar waje kadai ba tare da mu anan Najeriya mu na sarrafashi ba. Wannan zai bada damar cin gajiyarsa sosai kamar yadda ake cin gajiyar gyada idan aka yi matsarta wato za a samu mai a samu tunkuza. To shi a kashu ana samun wani ruwa wanda wasu masana’antun magunguna ke bukata don yin magani, ko kuma ya bada mai idan an soya, sannan a sarrafa dusarta zuwa sinadarin abincin dabbobi ko kuma sarrafa shi zuwa wani mai da ke hade da gari kamar na cin buredi, sannan namansa kuma a juya shi zuwa lemo wato juice a maimakon zubar da shi da ake yi ana amfani da kwallon kadai. Sannan akwai shirin samar da kananan injuna wadanda ba za su wuce nara mliyan 3 ba, da mai gonan kashu zai iya kafawa a gonarsa don sarrafa shi zuwa wadannan nau’uka daban-daban da kansa, hakan zai kara masa kudin shiga da kuma samar da ayyukan yi ga kasa a maimakon safarar ’ya’yan zuwa kasashen ketare ba tare da an sarrafa shi ba, su suci gajiyar harkar fiye da mu da mu ka nomata.
Aminiya: Me ye matsayin kasar nan a harkar samar da kashu a duniya?
Najeriya na matsayin kasa ta biyu wajen samar da kashu a duniya. kasar betnam ita ce ke kan gaba a duniya wajen noma kashu, saboda ta na samar da kamar kashi 28 a cikin 100 na daukacin adadin kashu da ake samu a duniya, sai Najeriya ke biye mata da ke samar da kamar kashi 19 a cikin 100, sai Indiya mai kashi 15, sai kasar Kwaddebuwa mai kashi 9, sai Brazil mai kashi 5. Sai dai Najeriya nada dukkan dama na zama kasa ta daya idan manomanta za su samu cikakken taimako da su ke bukata ta dukkan nau’uka. Ma’ana maye gurabun tsoffin bishiyoyi da su ka shekara sama da 25 da wasu sabbi, saboda shi kashu idan bishiyarsa ta kai kamar shekara 25 to za ta rage samar da yabanya ta rika komawa baya-baya. Sannan kuma manoman su samu inganceccen iri da ke da saurin fara yabanya da kuma manyan ’ya’ya.
Aminiya: Ta yaya ka ke jin manomanta za su kara inganta harkar don karin cin gajiyar yadda ya kamata?
Kamar yadda na yi bayani a baya, hukumar RMRDC tare da hadin gwiwa da wasu jami’o’in kasar nan biyu ta samar da na’urorin saukakawa da kuma karin cin gajiyar wannnan harka ga manoma ta yadda za su sarrafa amfanin da su ka samu tare da kara masa kima gabanin sayarwa don samun gwaggwabar riba. Wannan kuma ya biyo bayan bincike da mu ka gudanar ne da ya gano cewa kimanin kashi 90 cikin 100 na kashu da kasar nan ke samarwa ana kai su ne zuwa wasu kasashen ketare irinsu Indiya ba tare da an ci karin gajiya da ake samu ba, a can ne za a sarrafa shi sannan a sake dawo mana da shi kasar nan a sayar mana akan farashi mai kima. A dalilin hakan a yanzu haka ana sarrafa kashun a kasar na zuwa nau’uka daban-daban don sayarwa ga masana’antunmu na nan gida sannan wasu ’ya’yansa kuma a sayar da su ga manyan kantunan kasar nan. wannan ya biyo bayan samar da injunan gudanar da ayyukan sarrafa shi ne da ya hada da na gurzansa da soya shi da kuma nikawa da dai sauransu, wadanda duk a nan gida ake kera su in banda guda da mu ke kawowa daga waje shi ne na packaging dinsa.
Aminiya: A fuskar kalubale fa wadanne matsaloli ne hukumar ta fi fuskanta?
kalubale a kullum bai wuce na rashin wadataccen kudin gudanarwa ba. Kamar rangadi da mu ke yi zuwa yankunan da ake nomasu don karfafawa manomansa gwiwa da kuma yi musu bayani akan sababbin dabaru na habaka harkar, duk bai yiwu wa sai idan akwai wadaceccen kudi. Kamar yadda yawanci aka sani noman kashu ya fi karfi ne a jihohin kudu maso gabas a sakamakon amfani da shi da su ke yi wajen magance matsalar zaizayar kasa da ya ke yi, sai dai a yanzu ya watsu zuwa karin wasu yankunan kasar nan bayan gano dumbin alheran da ke cikansa.
Aminiya: Wane sha’awara za ku baiwa masu sha’awar shuka kashu?
Da farko dai lokacin shuka kashu kamar na amfanin gona ne ma’ana da zaran damina ta zauna sai a shuka shi. Mu na da tsarin raba ingaceccen iri ga wadanda su ka rubuta takardar neman su na so daga hukumarmu a ofisoshinmu 36 da ke jihohin kasar nan da kuma nan Abuja. A yanzu haka mu na daf da kaddamar da wani sabon iri da ya dara wanda ake kira “Brazil Jumbo” akwai kuma hanyoyin da ake bi wajen shuka daban-daban da ya hada da dashe da tsarin aure, ma’ana a cire bangare na kashu da ya fara a hada shi da na karamin bishiya, sai kuma maye gurbin tsoffin itatuwa da su ka dara shekara 25 da sababbi don inganta adadin yabanya, shi irin wannan a na yinsa ne rukuni-rukuni yau ka dibi kamar hekta biyu misali sannan wata shekarar ka sake sabon shuki a wani hektan, kasancewar ba a son girman bishiya su bambanta a waje guda don kada wasu su hana wasu samun rana, hanyoyin suna da dama.