Dalilin da ya sa kafafuwan gizo-gizo suka zama sirara (2)

Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Ya karatu, ina fata kuna karatu sosai don ku ci jarrabawa musamman a wannan lokaci da ake neman fara yin jarrabawa don a ba ku hutu.  Har ila yau a kan hanyarsa sai ya biya ta gidan kunkuru, suna gama gaisawa sai gizo-gizo ya yi farat […]

Dalilin da ya sa kafafuwan gizo-gizo suka zama sirara (2)

Manyan gobe tare da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Ya karatu, ina fata kuna karatu sosai don ku ci jarrabawa musamman a wannan lokaci da ake neman fara yin jarrabawa don a ba ku hutu. 

Har ila yau a kan hanyarsa sai ya biya ta gidan kunkuru, suna gama gaisawa sai gizo-gizo ya yi farat ya ce, “Mhm! na tabbatar dankali kake dafawa”  Sai kunkuru ya bushe da dariya ya ce “Gizo-gizo kenan! Dankali nake dafawa har ma da zuma idan za ka ci ka zauna ka jira saura kadan ya karasa dahuwa” A nan ma sai gizo-gizo ya sake yanke shawawar saka yanarsa wacce ya daure a jikin kafarsa sannan ya daura daya bangaren a jikin tukunyar girkin. Haka ya yi ta zaga gidajen abokansa yana daure kafafuwansa da tukwanensu har sai da ya daure dukkannin kafafuwansa guda takwas.

A  daidai lokacin da gizo-gizo ya isa bakin wani kogi sai ya yi niyyar hutawa a wurin kafin abincin gidajen abokansa  ya karasa dahuwa ya koma ya ci. Nan Gizo ya zauna yana jin dadi tare da alfahari da irin wayon da yake da shi. Yana kuma tunani a zuciyarsa  kan ko tukunyar wane ne za ta fara dahuwa a cikisu? Zuwa can sai  ya ji ana ja masa kafa sai ya ce a ransa “Lallai wannan jan daga gidan zomo ne” Kafin ya gama tabbatarwa sai ya ji ana jan daya kafar.  Ita ma bai farga ba sai ya ji an sake jan ta ukun. Sai abin ya zama kamar hadin baki duk kafafuwan ana jan su a lokaci guda. Tun gizo-gizo yana ihu har ya kasa. Duk ihun da yake bai sa an daina ja masa kafafuwan ba. Bai san

lokacin da ya fada cikin  kogi ba. Yana fadawa kuwa sai ya samu saukin jan da ake yi wa kafafuwan nasa, kasancewar ruwan ya wanke duk sakar yanar da ya yi.

Haka gizo-gizo ya zauna a nan ya yi ta jinyar kafafuwansa. Bai sake biya wa ta kan abincin ba. Shi kenan tun daga wannan lokaci kafafuwansa suka koma sirara sakamakon jan su da aka yi ta yi.