Dalilin da ya sa kotu ta kawo karshen Shari’ar Naziru Sarkin Waka

Wata kotun Majistire da ke zamanta a Jihar Kano, ta sallami Shari’ar Naziru Ahmed (Sarkin Waka) bayan ya nemi afuwar gwamnatin Jihar Kano kan wata waka da ya saki ba tare da sahalewar hukumar tace fina-finai ta jihar ba. Kotun, wadda Mai Shari’a Aminu Gabari yake jagoranta, ta sallami shari’ar da take yi wa Sarkin […]

Dalilin da ya sa kotu ta kawo karshen Shari’ar Naziru Sarkin Waka

Naziru Ahmed; Sarkin Waka

Wata kotun Majistire da ke zamanta a Jihar Kano, ta sallami Shari’ar Naziru Ahmed (Sarkin Waka) bayan ya nemi afuwar gwamnatin Jihar Kano kan wata waka da ya saki ba tare da sahalewar hukumar tace fina-finai ta jihar ba.

Kotun, wadda Mai Shari’a Aminu Gabari yake jagoranta, ta sallami shari’ar da take yi wa Sarkin Wakar bayan ya yi nadama da neman gafarar laifin da ya aikata na sakin wata waka ba tare da samun izini ba.

A zaman kotun na ranar Talata, lauyan da ke wakiltar Gwamnatin Jihar Kano a shari’ar, Wada Ahmad Wada, ya gabatar da wata takardar bayar da hakuri zuwa ga gwamnatin jihar.

Lauyan ya gabatar da takardar ne a madadin wanda ake zargi da aikata laifin kuma ya bayyana cewa takardar ta fito ne daga shi Sarkin Wakar.

Takardar, wadda Naziru Ahmad din ya rubuta zuwa ga Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, ta ce: “Ni Naziru M. Ahmed ina bayar da hakuri bisa zargin da aka yi min kuma na yi da-na-sanin abin da ya faru.”

Lauyan da ke kare Naziru M. Ahmed, Sadik Kurawa, ya ce sun cimma wannan matsaya ne sakamakon fahimtar junan da aka samu tsakaninsu da masu wakiltar Gwamnatin Jihar.

Sarkin Wakar ya bayyana cewa, ya bayar da hakurin ne bayan masu ruwa da tsaki sun saka baki kan lamarin.

Takardar neman afuwar Gwamnatin Kano da Naziru M. Ahmad ya gabatarwa Kotu.

Waiwaye kan Shari’ar Sarkin Waka

Idan ba’a manta ba a cikin watan Satumbar shekarar 2019 ne kotun ta tsare Sarkin Wakar, daga baya kuma ta sake shi bayan ya cika wasu ka’idoji da sharudan belin da ta gindaya masa.

Daga baya kuma cikin Nuwambar 2020 kotun ta soke belin da Nazirun ya samu inda ta sake sanya masa wasu sabbin sharuda wanda bayan ya gaza cikawa a kan lokaci ta aike da shi kurkuku.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya