Dalilin da ya sa majalisarmu ta zama ta farko wajen tsige Gwamna a kasar nan – Halle Jani
Alhaji Halle Jani, jigo ne a Jam’iyyar PDP, kuma daya ne daga cikin tsofaffin ’yan majalisar dokokin tsohuwar Jihar Kaduna a Jamhuriyyya ta Biyu a karkashin Jam’iyyar NPN, kuma shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, har ila yau daya daga cikin ’yan majalisar da suka tsige Gwamna Abdulkadir Balarabe Musa a shekarar 1982, […]
Alhaji Halle Jani, jigo ne a Jam’iyyar PDP, kuma daya ne daga cikin tsofaffin ’yan majalisar dokokin tsohuwar Jihar Kaduna a Jamhuriyyya ta Biyu a karkashin Jam’iyyar NPN, kuma shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, har ila yau daya daga cikin ’yan majalisar da suka tsige Gwamna Abdulkadir Balarabe Musa a shekarar 1982, tsigewar da za a iya cewa ita ce ta farko a tarihin siyasar Najeriya. Ya bayyana dalilin da suka sa suka tsige Gwamnan kamar haka:
Aminiya: Kana cikin ’yan majalisar da suka tsige Gwamna Balarabe Musa a wancan lokaci, wadanne dalilai ne suka ja hankalinku har kuka dauki matakin tsige shi?
Halle Jani: Mun tsige Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ne bisa ga dalillai da dama, musamman abin da ya shafi kudade da kuma kafewa. Zahirin gaskiya ma a wancan lokaci, Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna tana cike da wakillan NPN ne, shi kuma an zabe shi a karkashin Jam’iyyar PRP ne. Me ya kamata Balarabe Musa ya yi a wancan lokaci? A wancan lokaci a kasar nan kowa ya ji lokacin da yake bude baki yana cewa ba zai yi aiki da mutanen NPN ba. Wanda kuma mutanen NPN ne suke cike da majalisa. Domin lokacin nan mu 99 ne, NPN tana da mambobi 66, sauran jam’iyyun UPN da GNPP da PRP suna da 33. To amma duk da haka, wannan ba shi ne makasudin tsige shi ba. Zai yi garbabau, ya yi gaban kansa ya aikata wani abu ba tare da shawartar majalisa ba. Irin wadannan abubuwa ne muka ga ba za mu iya jure musu ba, ba za mu iya bari a ci gaba da barna haka nan ana bata dukiyar al’ummar Jihar Kaduna ba. Da muka ga dai mutumin nan ba ya jin magana, sai muka jawo hankalinsa bisa ga wasu abubuwa, ba ya saurara mana, shi ya sa muka yanke shawara muka rubuta zarge-zargen da muke yi masa, muka aika masa amma bai mayar mana da amsa ba, muka ga me ya kamata mu yi saboda mu kawar da wannan mutum don samun ci gaban Jihar Kaduna. Shi ne muka nemi mai shari’a na jiha don ya kaddamar da kwamiti kamar yadda tsarin mulki ya nuna, ina jin ko kashi na 82 ko 83 ne. Ba zan iya tunawa ba. Aka kafa kwamiti na adalai mutum bakwai, wanda babu harkar addini ko yi musu katsalandan. Kwamiti ya yi zama muka je muka ba da shaida, aka gayyaci Gwamna bai zo ba, suka kammala rahotonsu suka kawo mana majalisa.
Aminiya: Shin kotu ce ke kafa wannan kwamiti ko majalisa?
Halle Jani: Kotu ce ke kafawa, don haka tsarin mulki ya ce. To bayan duba rahoton sai muka ga lallai sai mun tsige shi, haka kuma aka yi, ta hanyar jefa kuri’ar ’yar tunke. Kashi 2 bisa 3 muka amince.
Aminiya: Dukkanku daga jam’iyya daya?
Halle Jani: Eh, amma fa ba don bambancin jam’iyya ne ba, sai don ci gaban jama’a.
Aminiya: Shin ko Gwamnatin Tarayya a wancan lokaci ta nuna sha’awarta a wannan yunkuri naku?
Ai babu maganar sha’awa daga gwamnati, duk da dai gwamnatin da muke da su mutanen NPN ne kamar mu. A lokacin Shugaban kasa Shagari babu irin mutanen da bai aiko Kaduna ba don a dakatar da mu daga haka, amma muka kiya. Domin har marigayi Umaru Dikko, Shagari ya aiko shi daga Legas ya same mu, a karshe ma ko mutum daya bai gani ba, don mun riga mun yanke shawara.
To wace fa’ida ake samu?
Halle Jani: Ci gaban Jihar Kaduna. Don an rantsar da Mataimakinsa kamar yadda tsarin mulki ya nuna.
Aminiya: Shin doka ta ba da damar a tsige Gwamna da Mataimakinsa a lokaci guda ba Gwamna kadai ba?
Halle Jani: Doka ta ba da dama, ai tsarin mulki ne. Kamar yadda Majalisar Adamawa ta so ta yi.
Aminiya: A yanzu wadansu ’yan majalisun jihohin suna kokarin mayar da batun tsige Gwamna tamkar wani abin yayi ko ado, kai yaya kake ganin abin?
Halle Jani: Eh, zai zamo ado kuma ba ado ba, domin kamar yadda tsarin mulki ya nuna, bangaren gwamnati uku ne. Akwai bangaren zartarwa na Shugaban kasa da ministoci da masu ba shi shawara da Gwamna da kwamishinoninsa da masu ba shi shawara. Sai bangaren shari’a wanda shi ma zaman kansa yake yi, sai bangaren majalisa. Wadda ita majalisar nan take kan gaba. Ai ko Shugaban kasa ko Gwamna idan suka yi kasafin kudi sai sun kai gaban majalisa don neman amincewa.
Aminiya: Idan ka dubi wannan iska mai kadawa na batun tsige-tsige, ga Adamawa sai kuma ga Jihar Nasarawa, anya za a haifar da da mai ido?
Halle Jani: To me ko zai hana? Ai dimokuradiyyar ke nan. Misali, ba Najeriya ba, inda yanzu muke koyo, inda ma suka kirkiro ta wato Amurka ai an yi haka. Sun yi yunkurin tsige Shugaba Dikson amma ya yi murabus da ya ga abin da gaske ake yi. Ga kuma na kwanan nan na Ukrain, inda su ma ’yan majalisa ne suka tsige Shugaban kasar. Haka ta gada, idan ka yi a yi maka.
Akwai hange da ake yi cewa ana son mayar da wannan batu na tsigewa tamkar wata sabuwar hanyar kasuwanci ga su ’yan majalisa inda ake zargin ana ba su na goro don tsige wanda ake gani zai zamo katanga ga biyan bukatun wasu?
To, wannan ai har abada dan Adam bai rasa zargi. Mafi yawa zargi ne. In dai ’yan majalisa suna da kishin jiharsu, to zai yi wuya a ce za a ba su kudi don tsige wani su amsa.