‘Dalilin da ya sa muka baro mahajjatan Jihar Bauchi biyu a Saudiyya’
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta ce mutum hudu ne suka rasu a cikin alhazan jihar a Hajjin bana, kuma an bar mahajjata biyu a kasar Saudiyya saboda ba su da lafiya. Mukaddashin Sakataren Hukumar Alhaji Kasim Danladi Shall ne ya bayyana haka a filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke […]
Gwamna Bala Mohammed ne mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar Bauchi
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta ce mutum hudu ne suka rasu a cikin alhazan jihar a Hajjin bana, kuma an bar mahajjata biyu a kasar Saudiyya saboda ba su da lafiya.
Mukaddashin Sakataren Hukumar Alhaji Kasim Danladi Shall ne ya bayyana haka a filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi bayan isowar jirgin karshe da ya kwaso alhazan jihar na bana.
Ya ce an baro mutum biyu da ke fama da rashin lafiya suna jinya a wani asibitin Saudiyya kuma za a dawo da su Najeriya da zarar sun samu sauki.
Ya yaba wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed saboda goyon baya da kula da ya rika ba hukumar a lokacin aikin Hajjin bana.
A jawabin Shugaban Kwamitin Tsaro na alhazan, Sanata Adamu Ibrahim ya yaba wa mahajjatan jihar bisa halayen kirki da suka nuna a lokacin zamansu a Kasa Mai tsarki kuma ya bukaci su ci gaba da haka.
Jirgin Mad Air ne ya kawo alhazan 281 da suka rage daga cikin alhazai 1,945 da suka sauke farali daga jihar da misalin karfe 4:00 na dare.