Dalilin da ya sa muka zabi Lamido Sanusi – Kwankwaso

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa aka zabi Malam Sanusi Lamido Sanusi ya zama sabon sarkin Kano, daga cikin ’ya’yan sarauta uku da suka yi takara.Sanusi, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya ne, ya kuma shiga gaban ’yan takarar sarauta biyu da masu zaben sarki suka gabatar, wadanda suka hada da Hakimin […]

Dalilin da ya sa muka zabi Lamido Sanusi – Kwankwaso
Dalilin da ya sa muka zabi Lamido Sanusi – Kwankwaso

Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa aka zabi Malam Sanusi Lamido Sanusi ya zama sabon sarkin Kano, daga cikin ’ya’yan sarauta uku da suka yi takara.
Sanusi, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya ne, ya kuma shiga gaban ’yan takarar sarauta biyu da masu zaben sarki suka gabatar, wadanda suka hada da Hakimin Gwale, Alhaji Sanusi Ado Bayero da Wamban Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
Da yake jawabi wajen mika takardar kama aikin sabon sarkin,. Gwamnan Jihar Kano ya ce an zabi Sanusi ne saboda irin gogewarsa da kwarewarsa da cancantarsa a fannonin rayuwa.
“Allah cikin rahamarSa wadda ba ta da iyaka, Ya sanya aka bijiro da sunan Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a jerin mutanen da masu zaben Sarki suka gabatar” a cewar Kwankwaso, inda ya karyata cewa sunan Sanusi ba ya cikin sunayen da masu zaben sarki suka gabatar.
“Mun zabe shi ne saboda gogewarsa da cancantarsa da kwarewarsa, sannan yana cikin wadanda suka gaji sarautar, kamar yadda al’adar masarautar ta tanada, sai gwamnatin Kano ta yanke matsaya wajen zabensa a matsayin sabon sarkin Kano.
“Kamar yadda kuka ji, kuka gani, a taronmu na jiya (ranar Lahadi da ta wuce), wato 8 ga Yuni, bayan taron da muka yi ranar Asabar, 7 ga Yuni, tare da masu zaben sarki, inda muka yanke cewa za mu sake haduwa jiya Lahadi.Sai dai wadansu makiyan wannan jiha da gwamnatinmu, sun yi hanzari tun kafin mu yi taron, sun cusa siyasa, inda suka bayyana a tashoshin talabijin da rediyo, alhali ko zama ba mu yi, mun tattauna da masu takarar sarautar ba’’.
“An jawo hankalina kan abin da ke faruwa a daidai lokacin da muike kokarin shiga taro tare da masu zaben sarki, wadanda suka nusar da ni cewa a matsayina na gwamnan Kano. Sai na yi nazari kan shawarwarinsu, na zabi Mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon Sarkin Kano.” Inji shi.
Kwankwaso ya ce zaben ba shi da wata alaka da siyasa, sabanin yadda ake zargi. “Wadansu mutane na ganin wannan nadin sarkin siyasa ce, alhali ba haka al’amarin yake ba. Allah Kadai ya san wadanda ke da dimbin magoya baya, a tsakanin wadanda suka yi takarar sarauta, saboda al’amarin ba ya bukatar kada kuri’a, kamar yadda ake yi wajen zaben gwamna,” a cewarsa.
“Tande-tanade doka da ka’idojin zaben sarki ba sa bukatar mutane su kada kuri’a. Hakkin masu zaben sarki ne su bai wa gwamna shawara, shi kuma gwamna idan Allah Ya nufa sai ya zabi wanda zai zama sarki,” inji shi.
 Kwankwaso ya yi kira ga hakimai da dagatai da masu unguwanni da su amince da wannan nadi a matsayin nufin Allah ne.
Gwamnan ya bayar da sanarwar cewa gwamnati ta gina sabon gida don sake tsugunnar da iyalan Marigayi Mai martaba Ado Bayero, bayan sun fice daga fada.
“Gwamnatinmu ta gina wa iyalan Marigayin Sarki gida a Sharada, kuma yau Kwmaishinan Ayyuka zai mika makullan ga iyalan marigayin sarkin, ga wadanda ke sha’awar su zauna a cikin gidan, a shirye muke mu gina sabon gida ga iyalan sarki da ke bukatar su ci gba da zama a fada. A shirye muke mu tabbatar da cewa iyalan marigayin sarki sun samu kwankciyar hankali da walwalar rayuwa cikin mutunci,” a cewar Kwankwaso.
Dangane da zanga-zangar da aka yi kan zaben sabon sarki kuwa, Kwankwaso cewa ya yi: “Ina shawartar wadanda ke biyan wadannan matasa su kunna wuta a kan tituna, su sani ba abu ne mai kyau ba..”
“A tsawon shekara 20 da na shafe ina siyasa, kuma na yi ina jan ragamar jihar nan har sau biyu, ban taba daukar ’yan daba ba. Don haka muna gargadinsu da su daina. Wadansu mutane na cewa sunan Mai martaba ba ya cikin jerin sunayen, to ina mai sanar da su cewa, sunansa ba ma a cikin jerin sunayen kadai yake ba, shi ne ma a sahun farko na jerin sunayen,” inji shi.