Dalilin da ya sa muke shakkar Jega -PDP

Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali shi ne mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, ya tabo batutuwan da suka shafi amfani da na’ura mai tantance katin zabe na dindindin, da batun ficewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga jam’iyyar PDP, ya bayyana dalilan da jam’iyyarsu ke shakkar shugaban Hukumar Zabe na kasa, Farfesa […]

Dalilin da ya sa muke shakkar Jega -PDP

Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali shi ne mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, ya tabo batutuwan da suka shafi amfani da na’ura mai tantance katin zabe na dindindin, da batun ficewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga jam’iyyar PDP, ya bayyana dalilan da jam’iyyarsu ke shakkar shugaban Hukumar Zabe na kasa, Farfesa Attahiru Jega. Ya tambayi hukamar zabe wadansu tambayoyi, inda hakan ya sanya suke dari-dari da shirin hukumar zabe na gudanar da sahihin zabe a kasar nan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: An zargi cewa jam’iyyarku ce ta sanya aka dage zabe saboda kun tsorata, kuna ganin za ku sha kaye, sannan yanzu tun da aka dage zabe ina jirgin kamfen dinku ya dosa?
Farfesa Alkali: Da farko za mu gode wa Allah da Ya kawo mu wannan lokacin, shirye-shiryen kamfen da muka yi a kwanakin baya abubuwa sun yi kyau, lokacin da aka fara shirin kamfen kowa ya razana saboda ana ganin babu lokaci, a lokacin ana maganar bai fi kwana 40 ba, sannan ana so a zagaya jihohin Najeriya 36 har da Abuja, hakan ba karamin aiki ba ne, duk da haka da Allah ya shige mana gaba mun samu nasarar zagaya Najeriya gaba daya, abin da muka gani, muka ji sun faranta mana zuciya, domin PDP tana nan da karfinta. Al’ada ce a duk lokacin da za a yi wani abu da ya shafi kasa, to dole sai majalisar kasa ta zauna, sai a kira wanda abin ya shafa don ya bada bayani, idan suka gamsu shi ke nan, idan suna da wani bayani, ko tambayoyi sai su yi, haka aka kira hukumar zabe don ta bada bahasi, sun ce sun shirya wa zabe a lokacin, maganar ta zama kashi biyu, daya ba za a shirya zabe ba sai an raba katunan zabe, a lokacin INEC ta ce a cikin mutane miliyan 68 da dubu 900, mutane kusan miliyan 24 ba su samu katunan zabensu ba, sai aka ce daga ranar da aka yi wannan taron zuwa ranar zabe bai kai mako daya ba. Amma da yake komai mutum ya yi ne sai an kalle shi a bangarori da dama, musamman ma ga bangaren hamayya, komai kallon baki suke yi masa, inda a yanzu suke ta nanata maganar tsaro, wannan ma ba laifi ba ne, hakkin gwamnati ne ta kare rayukan mutane da dukiyarsu. Majalisar kasa ba ta da damar ta hana ko ta sa hukumar zabe shirya zabe ko dagewa, hukumar zabe ce za ta sa rana, shi ne suka koma sannan suka sake sanya wadannan ranakun da za a yi zaben. A yanzu mun koma neman jama’a. Jama’a su ne siyasa.
Aminiya: Abubuwa da yawa sun taso dangane da na’ura mai tantance katin zabe, inda aka yi zargin jam’iyyarku ta PDP ba ta so a yi amfani da wannan na’urar saboda hakan zai hana ku yin magudin zabe, a yanzu jama’a za su so ka yi musu bayanin matsayin jam’iyyarku a kan wannan na’ura?
Farfesa Alkali: Batun na’aurar da ke tantance katin zabe na cikin abin da ake dubawa, mu fa sani karatu bai ishi mutane a kasar nan ba, musamman ma ga batun na’ura da kuma aiki da ita, ko wayar salula da muke gani, wani bai san yadda ake aiki da ita ba, komai sai an koya maka, duk wani abu sabo da ya shafi siyasa, sai an yi kace-nace a kansa. Don haka muna kira ga hukumar zabe ta fito bainar jama’a ta gwada mana yadda ake amfani da wannan na’ura kowa ya gani, a gwada a kauye, a gwada a karkara, a gwada da rana, a gwada da daddare, a gwada a wurin da akwai wutar lantarki da kuma wurin da babu. Idan dokar tsarin zabe ta ce a yi amfani da wannan na’ura to babu laifi, abin tambaya shi ne, minti nawa na’urar za ta karanta katin zaben? Awa nawa ake da shi daga lokacin da aka bude mazaba zuwa lokacin rufewa? Sannan jama’a nawa ake samu a kowace mazaba? Shin lokacin da na’urar za ta tantance katunan zaben da ke mazabar ba zai kawo tsaiko wajen gudanar da sahihin zabe ba? Sannan a sanar da jama’a shin wannan na’ura tana amfani da wutar lantarki ne, ko batir ne? Idan batir ne shin yana amfani da ruwa ne? Ko hasken rana ne? Idan da batir take amfani, shin awa nawa batir din yake kafin ya mutu? Idan wanda ake sake gasa shi ne, idan a kauye ne a ina za a gasa shi? Idan da janareto za a rika gasa shi, janareto nawa za a kai kauyuka? Kasancewar a shekarar 2011 an smau irin wannan matsalar an kawo na’urar laptop da ake rijista, amma tun ba a je ko’ina ba sai ka ga an dauko ta niki-niki kamar mace mai ciki, an kai ta nan gyara, an kai ta can gyara. Idan ba lokacin zabe ba ne za a iya gwadawa babu damuwa, amma a yanzu idan aka samu kuskure kadan, ko kuma aka yi rashin sa’a ma’aikatan zabe ba su san aikinsu ba, sai al’amarin ya yi rubar guna, sai kowa ya yi asara. Kada ku manta tun ba a kai ga zabe ba ana ta zage-zage, a tara mutane a wajen zabe, sannan na’ura ta ki aiki, me kuke tunanin zai faru? Don haka ina so hukumar zabe ta yi hattara.
Aminiya: dage zaben ya yi wa jam’iyyarku dadi ke nan, sannan kana ganin hukumar zabe ta yi shirin da ya kamata?
Farfesa Alkali: daya daga cikin alamar shiri shi ne duk wadanda suka yi rijista, to a ce sun samu katunan zabensu, kuma na bayyana muku fiye da mutane miliyan 24 ba su samu wadannan katin zabe na dindindin ba, a yanzu da nake yi muku maganar tun bayan da aka kara kwanakin nan an samu mutane fiye da miliyan 6 da dubu 400 da suka karbi katinsu, idan ka dubi kasashe da yawa a Afirka akwai kasashe masu yawa da yawan mutanensu bai kai miliyan 6 ba, sai ya kasance mutane fiye da miliyan 6 ba su samu katin zabensu ba, a yanzu kuma sun samu, riba aka samu ko faduwa? Har su ma ’yan hamayyar da suke so a yi zaben idan ba mugunta ga magoya bayansu ba, ba za su ce a yi zaben ba, yanzu haka sun bazama suna kira ga mutanensu su je su karbi katin zabe na dindindin, mun ga yawan mutanensu da suka karbi katinsu, tambaya gare su ita ce me ya sa suke so a yi zabe duk da kasancewar mutanensu ba su karbi katin zabe ba? Suna da kyakkyawan nufin kuwa? Suna amfani da farfaganda, wacce ita ce cinsu da kuma shansu. Kudin da suke batarwa kan farfaganda shi muke kashewa kan makarantu da gyara hanyoyi. A yanzu a dauki gwamnoninmu da suka bar PDP suka koma jam’iyyar adawa, sun yi kokari amma a karkashin PDP, har ma ana kiransu, suna amsawa, har ma ake ta mutunta su, sun yi mana kwace ke nan, da bazarmu suke rawa.

Daga shafi na 2

Ka duba jihohin da suke karkashin ANPP su ne a baya, abin da nake nufi shi ne, ANPP ita ta haifi CPC, CPC kuma ta haifi APC, to wadannan jihohi suna baya. Ka dauko Barno ka hada ta da Bauchi, ka duba Yobe ka hada ta da Gombe, ko Katsina ka hada ta Zamfara, idan akwai wani ci gaba da aka samu a Jihar sai lokacin da PDP ta yi mulki a jihar, abin da muke farin ciki shi ne, a yanzu idon ’yan Najeriya ya bude. Ba laifi ba ne adawa, amma batun tayar da hankali, to su yi hattara. A kamfen dinsu an kona motocin PDP, an zazzage mu, an bi mu da duka, amma shugaban kasa da na jam’iyya muka ce kowa ya kwantar da hankalinsa, kada mu biye musu, idan muka biye musu za mu lalace, idan ba su daina ba karshenta su ne za su yi kuka. Amfanin siyasa a kawo wa talaka sauki.
Aminiya: Wane tabbaci kake da shi cewa jam’iyyarku za ta yarda a gudanar da sahihin zabe?
Farfesa Alkali: Nauyin gudanar da sahihin zabe ya ta’allaka ne a kan mutane da yawa, babban nauyin ya fi rataya a kan hukumar zabe, saboda muna alfahari da gyaran fuskar da aka yi wa dokokin zabe a kasar nan, yau za a ce akwai hukumar zabe mai zaman kanta, da ai babu wannan, a da za ka samu ’yan siyasa ne a cikin hukumar zabe, yanzu babu dan siyasa da ke cikin hukumar zabe. Na biyu da ma hukumar zabe kan bi sahu kamar sauran ma’aikatun da ke da ministoci don su karbi kudinsu na aiki, a yanzu gwamnati ba ta san yadda hukumar ke karbar kudinta ba, na uku kuma babu wani dan PDP da yake cikin hukumar zabe, wannan bai faru ba saboda shugabanci a karkashin PDP, amma ina so in tambayi jihohin da jam’iyyun adawa suke mulki yaya hukumar zabensu suke? Hukumar zabensu na ’yan siyasarsu ne, ta ’ya’yansu ne, ta matansu ne, ta abokansu ne, su suke gudanar da komai, ko zabe aka yi bugu daya suke, su dauke komai da komai, amma kuma suna son canji, a sama, ba sa son canji a kasa. Gudanar da sahihin zabe ya ta’allaka a kan shugaban hukumar zabe na kasa.
Na biyu, mu kanmu, ai mun ce a yi kamfen amma ban da doke, abin da nake so ’yan Arewa mu sani shi ne, ba a taba yin jam’iyya daya a Arewa ba, ko a zamanin Sardauna ma an samu jam’iyyun hamayya, akwai NEPU, akwai BYM da kuma UMDC, haka aka yi siyasa ba kashe-kashe da kone-kone kamar yadda muke gani a yanzu, sannan a zamanin Shagari wanda dan Arewa ne, amma akwai Ibrahim Waziri ya fita daga GNPP, Balarabe Musa ya fito daga PRP, amma ba a hana kowa yi ba, ba a yi kashe-kashe ba, ba a ce ga jam’iyyar Musulmi ko ta Kirista ba. A yanzu muna so a daina siyasar gaba da shashanci. Yanzu idan Arewa muka ci gaba da nuna kiyayya wane irin kallo sauran shiyyoyin kasar za su yi mana? Ta bangaren shugaban kasa ya yi alkawarin za a yi zabe cikin kwanciyar hankali, sannan ya ce kada wani ya yi rikici domin shi, kada a kashe wani dominsa.
Aminiya: Ba ka ganin yaga katin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi zai kawo muku nakasu a jam’iyyarku?
Farfesa Alkali: Idan kuka lura ba na shiga kace-nace a kan abin da ya shafi tsofaffin shugabanninmu, idan aka ce mutum shugaba ne, to ya san nauyin shugabanci, yana kai ko ba ya kai, domin akwai abin da Allah Ya ba shi, duk abin da shugaba ya yi tsohon shugaba ne ko a kai yake, to ba zan ce komai ba, domin tunaninsa ya bambanta da na sauran mutane, don haka ba mu san dalilin da ya sa ya yaga katinsa ba, sai jam’iyya ta bincika, ta gano abin da ya faru sannan ta san me za ta yi a kai, ni ba zan iya cewa komai ba, muna son gyara ne.
Aminiya: Jamiyyar PDP na ci gaba da korafi a kan hukumar zabe, shin ko kuna fargabar fuskantar zaben ne?
Farfesa Alkali: Ba gaskiya ba ne a ce jam’iyyar PDP ce kadai ke korafi a kan matakin shirin hukumar zabe, saboda akwai wasu jam’iyyu daban, illa iyaka dai an fi sa wa PDP ido ne, saboda ita ce jam’iyya da ke kan mulkin kasar nan. kuma ko a game da dage zabe da aka yi a baya ma ai an samu karin jama’a wadanda adadinsu ya kai wajen miliyan bakwai da su ka amshi katin zabensu bayan karin wadanda ba don dagewar ba ai da ba za su samu damar yin zaben ba.
Aminiya: Akwai bayanai da ke nuna cewa akwai take-taken neman a kori Farfesa Jega kafin lokacin ritayarsa, mene ne fargabarku na fuskantar zabe a karkashinsa?
Farfesa Alkali: Ni a bakinka na fara jin zancen kawar da shi, ku ma kai da ka ce ka ji hakan ai sai ka fuskanci inda maganar ta fito, sannan ka nemi jin hujjarsu a kan hakan, bai kamata mu rika gina siyasa a kan shaci fadi ba, don ba zai kai mu zuwa ko ina ba.
Aminiya: Ire-iren wadannan jam’iyyun a yanzu haka sun fara kiran da sake dage wannan zaben, kasancewar a baya su ne suka fara bukatar dage zabe, daga bisani kuka goyi baya, mene ne matsayinku a yanzu?
Farfesa Jega: Suna zaman kansu, kuma ba shawartar mu suke yi idan za su bayyana ra’ayinsu a kan wani al’amari ba, saboda haka wannan ra’ayinsu ne, mu dai a bangarenmu mun san zabe na tafe a wannan lokaci, kamar yadda aka tsara, kuma muna ci gaba da shirye-shiryenmu a kan hakan wajen ganin mun samu nasara a kai.