Dalilin da ya sa muke son canja mulkin Jonathan – Ango Abdullahi
Farfesa Ango Abdullahi daya ne daga cikin Dattawan Arewa kuma a wannan zantawa da ‘yan jaridu ya bayyana dalilansu na goyan bayan Janar Buhari da yadda gwamnatin shugaba Janathan ta kasa kawar da talauci a kasar nan. Aminiya: Mene ne makasudin ganawarka da ’yan jarida? Farfesa Ango: Dalilin shi ne an kwana biyu ba a […]
Farfesa Ango Abdullahi daya ne daga cikin Dattawan Arewa kuma a wannan zantawa da ‘yan jaridu ya bayyana dalilansu na goyan bayan Janar Buhari da yadda gwamnatin shugaba Janathan ta kasa kawar da talauci a kasar nan.
Aminiya: Mene ne makasudin ganawarka da ’yan jarida?
Farfesa Ango: Dalilin shi ne an kwana biyu ba a ji muryata ko ta wani dan kungiyarmu ta Dattawan Arewa ba. Mun sa ido ne mu ga yadda abubuwa za su kwaranye kan yadda jam’iyyu ke kokarin fitar da ’yan takarar Shugaban kasa zuwa sauran mukamai don zaben bana. Mun yi ta sa ido da bin yadda abubuwa ke tafiya. A matsayinmu na Dattawan Arewa mun so jam’iyyun nan biyu da ake ganin su ke da karfi, su ba mu ’yan takarar Shugaban kasa daga Arewa. Abin da ya sa muka sa rai, musamman Jam’iyyar PDP, kowa zai iya tunawa tun lokacin da aka fara mulkin farar hula shekara 16 da suka wuce, tana da wani tsari na karba-karba ta yadda mulki zai ruka kewayawa a tsakanin Kudu da Arewa. Wannan ne tsarin da aka yi a wannan jam’iyya tun farkonta, domin ina cikin wadanda suka kafa ta kuma ina cikin wadanda suka rubuta tsarin mulkinta. Saboda haka wannan shiri na karba-karba ya sa ta yi farin jini har aka zabe ta ko’ina a kasar nan. A karkashin tsarin karba-karba sai Kudu suka ce za su fara suka kawo wasu dalilai muka yarda da su duk da yake daga baya wasunmu sun ce mun yi kuskure. Aka ba su dama Obasanjo ya hau mulki, da ya zo ya san cewa shekara hudu ko takwas zai yi wanda shi ne tsarin mulki ya yarda. Daga nan mulki zai dawo Arewa a yi shekara takwas koda yake ya dan yi wutsul-wutsul da nufin neman tazarce amma abin bai yiwu ba. Umaru ’Yar’aduwa (Allah Ya jikansa) ya zo ya karba, Allah Ya yi masa rasuwa cikin shekara ta uku da shiga mulki. Ka ga idan aka lissafa daga cikin shekara takwas da muke sa ran Arewa za ta yi a kan mulki, Umaru kasa da shekara uku ya yi. Idan wannan jam’iyya tana da adalci ba sai an tambaye ta ba, za ta nemi shugabaninn PDP da ke Arewa su kawo wanda zai cikasa sauran shekarun Umaru. Amma sai muka ga ta ki kuma abin haushi wadanda suka ki din yawancinsu ’yan Arewa ne. Yawanci gwamnoni ne da suke cikin jam’iyyar, suka nace sai Jonathan ya zama Shugaban kasa a shekarar 2011 maimakon dan Arewa ya ci gaba daga inda Umaru ya tsaya. Sai ga shi wannan bai isa ba a wannan karo ma jam’iyyar ba ta ba Arewa damar ba, suka tsaya kai-da-fata kuma abin bakin ciki da goyon bayan wasu mutane da suke kiran kansu shugabanni a Arewa suka ce Jonathan din nan shi zai tsaya musu zabe. Sun ki ba mu wannan dama sai APC da ba ma cikinta ta kawo dan takara dan Arewa. Saboda haka mu Dattawan Arewa ba mu da wani ja yanzu muna tare da dan takarar da APC ta bayar wato Janar Muhammadu Buhari. Za mu goyi bayansa, kuma muna kiran mutanen Arewa da masu hankali daga sauran sassan kasar nan su goya masa baya, domin ga alama hankali ya fara dawowa jiki a fadin kasar nan cewa an gaji da wannan tafiya. Saboda haka idan kasar nan tana son zaman lafiya ta rayu lokaci ya yi da za a canja wannan mulki da ya kasa. Rashin zama lafiya da matsanacin talauci ga su nan babu iyaka. Babu yadda za a ce kasa kamar Najeriya da Allah Ya shuka arzikinSa a ce jama’arta na cikin mawuyancin hali kamar yadda muke ciki a yanzu. Wannan ya sa muke kiran mutane a dukkan kasar nan cewa su fito su yi rajista domin yin zabe kuma su zabi shugaba wanda zai canji wanda muke da shi yanzu. Domin wanda muke da shi yanzu hatta ’yan uwansa sun yarda ya kasa. Kuma idan an bar shi zai iya jawo rugujewar kasar nan.
Aminiya: Ba ku ganin hatta Arewa ta rabu domin kwanan nan wata kungiyar Dattawan Arewa takwararku ta ziyarci Shugaban kasa?
Farfesa Ango: Ba ta iya zama takwara a wajenmu ko ba kungiyar Tanko Yakasai kake magana a kai ba? Ba su iya zama takwararmu domin ita ’yar talla ce kuma ana biyanta ladar tallar da take yi, kuma mutanen Arewa su ne alkalai. Sun ce sun yarda Arewa ta samu Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo, mu kuma mun ce Shugaban kasa muke so, kuma tunda ba su ba mu a jam’iyyarsu ba muka ce ba ma so. Muna son jama’a su san cewa su Tanko Yakasai an kafa su ne saboda wannan aiki, ta yaya za a yi a tabbatar an samu Mataimakin Shugaban kasa a Arewa. Mu kuma Dattawan Arewa mun ce muna neman Shugaban kasa ne, ka ji bambancinmu da su ke nan. Muna jira ne mu ga wane irin talla za su yi a Arewa mu kuma ga wane ne mai saye.
Aminiya: Wadannan mutane daga Arewa suke kuma sun yi tarurrukan nuna yadda gwamnatin ke tallafa wa Arewa?
Farfesa Ango: Ka ji an ce wasu ba su jin kanshin miya amma suna jin kanshin Dala, ko ba ka ji wannan waka ba ce. To, mu ba mu cikin masu jin kanshin Dala, muna nan tare da jama’armu, abin da ya dame su ya dame mu. Su kuwa abin da ya dame su shi ne mai za su samu a fadar da suke wa bauta. Sun san cewa jama’arsu na cikin halin kaka-ni-ka-yi da yawa ana kashe su kamar kiyashi, ana tursasa wa jama’a, ana hana mu hakkokinmu kowa ya sani. Kwanan nan aka yi kasafin kudin bana, inda gefe daya a cikin bangarorin nan shida yana da kasafin da ya wuce sauran bangarori biyar kowa ya sani. Shugaban kasa ya san da haka har yana kokarin cewa wai ana binciken yadda hakan ya auku. Kai da jin wannan zance ka san zancen banza ne. Sannan Shugaban kasar ya nemi kare zargin da ake masa na kin jinin ’yan Arewa inda ya ce akwai ’yan Arewa a gwamnatinsa. To, ’yan Arewa irin su Gulak ko Labaran Maku, su Tanko Yakasai, mun san ’yan Arewa ne amma wadanda za su lura da kansu kafin su damu da damuwar ’yan Arewa.
Aminiya: Ana gani zaben 2015 na kawo barazana ga dorewar kasar nan, yaya kake kallon hasashen Amurka cewa Najeriya na iya wargajewa a bayan zaben?
Farfesa Ango: Abubuwa da yawa ke kawo rugujewar kasa kuma in kasarmu ta ruguje ba ita ce ta farko da ta ruguje ta fuskar siyasa ba. Kana da labarin lokacin da kasar Indiya ta samu ’yancin kai, cikin shekara daya da ba su samu daidaituwa ba suka rabu aka samu Pakistan. Cikin shekara daya zuwa biyu ita ma Pakistan din ta rabu aka samu Bangladesh. Kuma shekaru kadan da suka wuce sha’anin siyasa ya kawo rugujewar Tarayyar Subiyet ta tashi daga kasa daya zuwa kasashe 15. Ita kanta kasar Birtaniya kwanan nan aka yi zaben jin ra’ayin jama’a cewa yankin Scotland wanda kusan shekara 350 suna zaune waje daya sun ce wai sun gaji don haka suna neman ’yancin kai. Har yanzu ga batun yankin Ireland ta Arewa ana ta rikici a kan neman rabuwarsu. Saboda haka ba wani abu ba ne sabo kasa ta rabu. Sai dai abin da za mu lura da shi su ne dalilan da muke da su yanzu sun isa a ce Najeriya ta rabu? A wurina halin da muke ciki a yanzu ban ga isassun dalilan da za su sa kasa ta rabu ba. Amma watakila wadanda suke neman ta rabu idan suka kawo mana dalilan da suke ganin a rabu sai a rabu tunda ba mu ne farko da za mu fara rabuwa ba. Amma abin da za ka lura da shi, shi ne ba mu ke fata ba, akwai kila masu fata daga waje akwai kila masu fata daga ciki. Amma masu fata daga ciki muna son su kawo isassun dalilai da za su sa kowa ya ga cewa maimakon zama waje daya, zai fi alfanu a rabu. kila rabuwar ita za ta fi zame mana alheri.
Aminiya: Kana ji a jikinka cewa za a yi zaben nan lami lafiya idan aka yi la’akari da tashin-tashina a wasu yankunan kasa?
Farfesa Ango: Ina sa ran za a yi zabe mai zuwa a kasar nan amma lami lafiya, ka san abin da kake nufi lami lafiya. Wato babu wanda ya kwarzani wani ko ya zagi wani in wannan kake nufi sai in ce ba a taba zabe a wata kasa irin wannan da za a ce an yi shi lami lafiya ba. Fata dai shi ne a bar mutane su yi zabe a kirga kuri’arsu a kuma kai ta inda suke so a a kaita a kuma kirga a bada sakamakon wanda ya ci zabe, bisa adalci, shi kadai zai sa a yi zabe lafiya din da kake magana.
Aminiya: Me ye sakonka ga jama’ar kasa?
Farfesa Ango: Sakona ga jama’ar kasa, da farko dai wannan kasa abar rikewa ce idan ana so. Abin da kake so shi kake tarairaya ka rike shi da kyau. Kamar jariri ne uwarsa ke tarairayarsa har ya girma cikin ikon Allah. Ta haka nan jama’ar kasa ke da nauyin tarairayar kasarsu domin gina ta don jama’ar ciki su ji dadi. To, amma abin da za su lura da shi kullum shi ne tabbatar da cewa mece ce tasu gudunmawa ta yadda za su tabbatar da cewa wannan jaririyar ta zauna lafiya ta girma ta zo ta yi ’ya’ya da jikoki cikin jin dadi. Shi ne su fito kwansu da kwarkwata lokacin zabe domin ba za ka zauna a gida kana kukan cewa abu bai maka dadi ba, bayan an ba ka damar da za ka fito ka ce ga abin da nake so ga kuma abin da ba na so. Wannan shi ne sakona ga jama’a musamman a nan Arewa inda kukan ya fi yawa. karin sakon shi ne a fito a yi zaben kwatar kai.