Dalilin da ya sa muke son kafa kotun Kirista – dan majalisa Gyang

Yunkurin kafa kotun daukaka kara ta Kirista manufa ce ta warware matsalolinin mabiya addinin kirista a kotuna na musamman, a cewar wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, Istifanus Dung Gyang, wakili daga Jihar Filato. Gyang, wanda ya gabatar da kudurin a makon da ya wuce, ya ce al’amarin zai fadada harkokin shari’a da […]

Dalilin da ya sa muke son kafa kotun Kirista – dan majalisa Gyang

Yunkurin kafa kotun daukaka kara ta Kirista manufa ce ta warware matsalolinin mabiya addinin kirista a kotuna na musamman, a cewar wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, Istifanus Dung Gyang, wakili daga Jihar Filato.

Gyang, wanda ya gabatar da kudurin a makon da ya wuce, ya ce al’amarin zai fadada harkokin shari’a da aiwatar da dokokin kasa a Najeriya

“Gyaran da aka yi wa kudurin zai karfafa sashe na 37 sashe na (1) a kundin tsarin mulki, wanda ya bai wa kowane dan kasa ’yancin yin tunani da bayyana manufa da gudanar da addini, al’amarin da ya hada da yada addini da imani wajen yin ibada da koyarwa da ayyuka tare da kula.

“Baya haka, wannan zai bayar da dama fadada harkokin shari’a da warware matsaloli da aiwatar da dokoki a kasarmu, ta hanyar bin dokokin Ikilisiya na addinin Kirista wajen warware rikice-rikicen shari’a da suka shafi daidaikun dokokin Kisita da harkokin zamantakewa, bisa ka’idojin  Kotunan Ikilisiya,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko aiwatar da gyaran kudurin yana nufin samar da kotuna kwatankwacin na Shari’ar Musulunci ne, sai dan majalisar ya ce a’a, yunkuri ne kawai na tabbatar da aiki da sashe na 37 kashi na (1) a Kundin Tsarin mulki.

“Bai yi daidai da kotunan Shari’ar Musulunci ba. Wannan kawai manufa ce ta inganta aikin sashe na 37 kashi na (1) na Kundin Tsarin mulki,” inji shi.

Sai dai ana ganin wannan kudurin tamkar martani ne ga kudurion da aka gabatar na neman karin karfin iko ga Kotunan Shari’ar Musulunci. Amma sa ya ce, “Ba martani ba ne, kawai dai idan kundin tsarin mulki na da tanadin da ba a aiki da shi, akwai bukatar farfado da aikinsa. Wannan shi ne abin da muke yi. Tuni yana nan kunshe a kundin tsarin mulki.

Da aka tuntube shi don jin cewa, ko daga ina alkalan kotunan za su fito, sai ya ce: “Za su kasance mutane ne kwararrun masana a fannin shari’a da dokokin Ikilisiya, wadanda suka san Littafin Baibul. Gyaran da kudurin ya bijiro da shi ya bayyana karara kimar wadanda suka cancanci a nada su alkalanci, wadanda za a yi musu lakabi da Kadinal-kadinal.”

“Za a samar da sabon fagen nazari a fannonin ilimi. Wannan kyakkyawan abu ne da lamarin ya fito da shi. Sannan zai fada ayyukan tsara dokoki. Yanzu za a samar da kwasa-kwasai da za su bibiyi dokokin Ikilisiya. Zai yi matukar tasiri inganta harkokin shari’a da yin dokoki.

Dangane da jin cewa ko dokokin sun fi alaka da darikar Katolika ko cocin Romawa, sai ya ce:”E,. ta yiwu a ce haka game da al’amuran da ke tasowa. Zan dakatar da wannan tattaunawar, amma tabbas na san yana da alaka da su.

“Ba dokoki ba ne da ke damfare da addini. Kamar nada limamin addini Kadina, nadin alkalin zai kasance ne ta hannun Hukumar shari ta kasa (NJC). Wannan dai farkon al’amarin ne, tun da farawa aka yi mutane za su yi sharhi tare da bayyana fahimtar ra’ayoyinsu. Mun yi farin cikin jin cewa kudurin ya bude kafar tattaunawa. Wannan ba sabon abu ba ne. Wani bangare ne na dimokuradiyarmu, kuma tanadi ne da kundin tsarin mulki ya samar,” inji shi.

“Da zarar an sanya wa kudurin hannu ya zama doka, akwai al’amuran da za su biyo baya, wadanda suka hada da ka’idojin aiwatar da ayyuka a kotuna. Akwai sababbin dokoki da za a yi wadanda za su farfado da tanadin. Sai dai tunda akwai tanadin a cikin kundin tsarin mulki, akwai tsare-tsaren dokokin da za su biyo baya,” a cewarsa.

Yadda kotun kirista za ta yi aikinta

Majalisar wakilai ta fara yunkurin kafa kotun addinin Kirista a duk jihohi 36 na fadin Najeriya da birnin tarayya Abuja.

Majalisar ta ce za ta gyara sashe na 14 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin ta samu damar kafa kotun.

Saboda wannan dalilin, majalisar ta karanta kudurin karo na biyu wanda zai ba da dama a kafa kotun mabiya addinin Kristan wanda zai rika lura da al’amura da suka shafi addinin Kristanci da mabiya addinin.

kudurin wanda Istifanus Dung Gyang da Timothy Golu ‘yan majalisa daga jihar Filato a karkashin jam’iyyar PDP tare da wasu ‘yan majalisu guda 7 suka gabatar, ya kunshi ayyuka da karfin iko da ka’idojin cancanta da nade-nade da tsawon zangon zama ma’aikacin kotun idan aka kafa ta.

Wanda ya jagoranci tattaunawa a kan kudurin, Gyan ya ce, gyaran na daidai da sashi na 37 na kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ba da ‘yancin tunani da addini, wanda ya hada da tallata imani da ayyukan ibada da koyarwa da aikatace-aikacen addini da dabbaka su.

Ya ce, ‘Kadina’ wanda shi ne babban matsayi a majami’ar Katolica ne za su rika zama alkalan kotun wadanda kuma hukumar shari’a ta kasa ce za ta rika zaba, amma kuma za a rika zaban wadanda su ke da ilimin shari’a ne, kuma za su yanke hukunci ne daidai da yadda tsari da fahimtar addinin Kristanci da kuma dokokin kasa suka tanada.

A cewarsa, kotun za ta dauki nauyin lura da shari’a da kuma bin kadin dokokin shari’a na kasa wanda ke da alaka da abubuwa da suka shafi addinin Krista.

Ya kara da cewa, daga cikin bangarorin da sababbin dokokin za su shafa sun hada da tsarin auren addinin Krista da gado na mamaci da maganar yara da masu almubazzaranci. Sannan kuma a sabuwar dokar, dole ne ya zama dukkan wadanda abin ya shafa su zama mabiya addinin Krista ne kafin kotun ta saurari karar.

dan majalisan ya kara da cewa, sashen da dokar za ta shafa kuma za a gyara, sun hada da sashe na 6, 84,285,240,246,247,289,292 da kuma sashe na 318, sannan kuma za a saka sababbin abubuwa guda 4 wadanda za su taimaka wajen hada sabuwar dokar.

Da yake nasa jawabin a game da kudurin, Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya ce za a aika da kudurin da ke bukatar kafa wannan kotu zuwa kwamitin na musamman mai lura da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Da yake amsa tambayoyin wasu ‘yan jarida a game da ko akwai wani tsarin karatun shari’a na Krista, sai ya ce sabuwar dokar na da manufar fadada bangaren shara’ar Najeriya da kuma karatu ne, domin dole a kawo sababbin fannonin karatu a makarantu.

A game da maganar ko kotun za ta zama daidai da kotun shara’a na musulunci, dan majalisan ya nanata cewa, “wannan magana ce a kan sashe na 37 na kundin tsarin mulkin kasa,” wanda a cewarsa ya dade a ajiye.

Ba don ana da kotuna shari’ar musulunci muke neman tamu ba – Gyang

Ga cikakken hirar da aka yi da wakili Istifanus Gyang game da kudurin day a gabatar domin kafa kotun kirista a kasar nan.

                          

Aminiya: Me ya ba ka tunanin gabatar da wannan kuduri?

Abin da wannan kudurin doka ke nema shi ne, a farfado da Sashi na 37 (1) na Kundin Tsarin Mulki, wanda ke ba kowane dan kasa ’yancin tunani, walwala, yin addinin da ya zaba, tare da ’yancin yada addinin nasa, gudanarwa da kuma kiyaye shi.

Ba wannan ma kadai ba, kudurin zai ba mu damar fadada hukunce-hukuncen shari’a, yanke hukunci da kuma aikin lauyanci da kuma gudanar da rukunnan addinin Kirista da shari’arsa da suka shafi yanke hukunce-hukuncen da suka shafi Kiristoci kadai da kuma al’amuran da suka shafi al’amuran kasa da aka zayyana su a cikin dokoki, gudanarwa da tanaje-tanajen kotunan addinin Kirista.

Aminiya: Ko kuna neman kaddamar da kotuna kamar na Shari’a (Musulunci) ke nan?

A’a, ba irin kotunan Shari’a ba ne, a takaice dai muna son farfado da Sashi na 37 (1) na Kundin Tsarin Mulki.

Aminiya: Za a iya kallon cewa kamar kudurin yana martani ne ga kudurin da aka gabatar kwanan nan dangane da kotunan Shari’a, ba ka tunanin haka?

Wannan ba martani ba ne, kawai idan idan aka ce Kundin Tsarin Mulki ya tanadar da wani tsari, kuma ya kasance an bar shi, ba a amfani da shi, ya kamata a farfado da shi. Abin da muke kokarin yi ke nan, domin yana nan a cikin Kundin Tsarin Mulki da dadewa.

Aminiya:Daga ina za a samo alkalan da za su tafiyar da kotunan?

Za su kasance mutane ne sanannu a shari’a da dokokin addinin Kirista. kudurin ya tanadar da kimar ilimin alkalan, nada su, tsawon lokacin da za su yi a aiki da kuma cewa za a rika kiransu da lakabin ‘Limamai (Kadana).’

Aminiya: Shin akwai ma wasu dokoki da ake da su na musamman na addinin Kirista?

Dalili ke nan ya sanya muka ce wannan kuduri zai fadada al’amuran dokoki da hukunce-hukuncenmu. Za a samu gurbin fadada nazari, wannan shi ne abin lura mai muhimmanci kuma zai fadada ayyukan shari’a. Ke nan za a tanadar da kwas na musamman da zai takaita ga nazarin dokokin addinin Kirista. Zai kasance mai bijirar da babban kalubale ga al’amuran shari’armu da tsarin dokoki.

Aminiya: Ko wannan kudurin doka yana da wata dangantaka da tsarin shari’ar da manyan limaman coci suka samar?

Wannan sai daga baya za a ga yadda abin zai kasance. Ba zan ce komai ba kan wannan, nan gaba za a ci gaba da tattaunawa, amma tabbas zai kasance wani abu daga cikinsu ko kuma mu ce suna da dangantaka.

Aminiya: Za a iya samu karo tsakanin kudurin da tsarin shari’a nan da can saboda ya zuwa yanzu, akwai rarrabuwar fahimta tsakanin coci-coci. Me za ka ce game da wannan?

Wannan kuduri ba ya la’akari da darikokin da ke akwai a addinin Kirista. Kamar batun nada alkalan, wannan zai zama hakkin Hukumar Shari’a ta Najeriya ce (NJC). Komai yana da mafari kuma yana da karshe, dole ne mutane su yi sharhi ko su tofa albarkacin bakunansu. Mun ji dadi ganin cewa al’amarin zai bude kofar tattaunawa. Babu wani abu bako a cikin al’amarin nan, domin kuwa wannan na daga dimokuradiyya da abin da Tsarin Mulki ya tanadar.

Aminiya: Idan har an sanya wa wannan kuduri hannu ya zama doka, kana ganin kotunan za su fara aiki nan take?

Daga lokacin da aka sanya wa dokar hannu, akwai abubuwan da za su biyo baya, kamar hukunce-hukunce, yadda za a gudanar da su a kotu da sauransu. Akwai dokoki da yawa da za a haifar domin su tabbatar da wannan kudurin doka. Madamar akwai tanadin abu a Kundin Tsarin Mulki, to ai kuwa ya tanadar da tsarin yadda za a tafiyar da shi a doka.