Dalilin da ya sa muke yi wa Buhari kamfe – Iyantama

Hamisu Lamido Iyantama yana daya daga cikin ’yan fim din da ke yi dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar APC Janar Buhari kamfe. Aminiya ta tattauna da shi inda ya bayyana dalilan da ya sa suke tallar a zabi Janar Buhari a lokacin zabe mai zuwa: An bayyana cewa kai ne ka jagoranci […]

Dalilin da ya sa muke yi wa Buhari kamfe – Iyantama
Dalilin da ya sa muke yi wa Buhari kamfe – Iyantama

Hamisu Lamido Iyantama yana daya daga cikin ’yan fim din da ke yi dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin Jam’iyyar APC Janar Buhari kamfe. Aminiya ta tattauna da shi inda ya bayyana dalilan da ya sa suke tallar a zabi Janar Buhari a lokacin zabe mai zuwa:

An bayyana cewa kai ne ka jagoranci ’yan Kannywood don tallata Janar Muhammadu Buhari, me ya sa kuka zabi yi wa janar din kamfe?
Da farko dai ba ni ba ne na jagoranci ’yan Kannywood zuwa hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ba, akwai wani dan fim wanda ya san Ishak, shi ne ya gayyace shi, saboda ya san muna da ra’ayin neman canji, sakamakon tabarbarewar tattalin arzkin kasa, faduwar darajar Naira da faduwar farashin man fetur, rashin aikin yi, rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar nan, musamman sashin Arewacin kasar nan da kuma halin da muka shiga na dukurshewar ma’aikatu da rashin aikin yi, ni matsayina na Hamisu Lamido Iyantama sai na yi nazari, na ce to gwamnatin PDP ta shekara goma sha tana alkawari musamman ma a kan wutar lantarki, me ya sa ba za mu canza akala ba?
Kada ka manta muna da ’ya’ya da jikoki, amma ba mu san yaya rayuwarsu za ta kasance nan gaba ba, idan kana tafiya ka yi tuntube yau, ka sake yi gobe, to ya kamata ka sauya hanya, ni dan siyasa ne, na yi shugaban jam’iyya a Kano, na yi sakataren jam’iyyun adawa na Najeriya, na kuma yi takarar gwamna a Jihar Kano, ganin yadda al’amura suka gudana wadansu ’yan siyasar babu Allah a cikin al’amarinsu sai na koma kasuwanci. A yanzu wanda muke ganin zai magance matsalolin da na ambato shi ne tsohon soja, a lokacin da ya rike kasar nan ya zo mana da tsari na yaki da rashin da’a, idan akwai doka da oda a kasar nan babu wanda zai ci hanci, ko ya ci kudin gwamnati. Wannan dalili ya sa bayan an gayyaci Ishak (Sidi Ishak) shi kuma ya gayyace ni, sannan muka hada mutane.
Da kuka je hedikwatar me kuka yi a can?
Na je hedikwatar jam’iyyar a matsayin dajjito ne, ba wai shugaban tafiyar ba. A tafiyar akwai shugaban kungiyar AFMAN na kasa, Abdullahi Sani Abdullahi (Baba karami), akwai mataimakinsa Salisu Ofisa, akwai Isma’il NaAbba Afakallah, akwai Hajara Usman da Baballe Hayatu da Rahama Sadau da sauransu. Mun je hedkiwartar jam’iyyar muka yi rijista, sannan muka sanar da su idan ana neman wata gudunmuwa za a iya tuntubarmu, za mu bayar daidai gwargwado saboda ’yan fim din Arewa ba masu kudi ba ne, saboda durkushewar tattalin arziki, wannan gwamnati ba ta kula da mu kamar yadda ya kamata ba, ta dan ba mu horo ne na mutum 45, an ce za ba mu miliyan ashirin da biyar-biyar a tsarin Sure-P na graduate intensibe ke nan, amma ba mu san inda kudin suka tafi ba, mun cika duk wata ka’ida, sannan an kai mu Indiya mu 19, ya kamata a tura mutane sama da 500, ’yan kudancin Najeriya sun fi mu morar kudaden da shugaban kasa ya ware don habaka masana’antar fina-finai, kwanan nan an bada kudin capacity building, don na fito na yi magana a kafafen yada labarai sai aka cire ni daga cikin wadanda suke neman tallafi na miliyan shida ko bakwai. Ni da Afakallah mun kira taron ’yan jarida muka kalubalanci gwamnati ta yi bayanin abin da ta yi wa ’yan Kannywood, mun yi hakan ne don a fahimci cewa muna bada gudunmuwa ma, an ware kudi amma ba a yi mana ba, sai aka hana mu, ba wai bakin ciki nake don ban samu ba, na yi magana ’yan uwana sun samu, ina alfahari da hakan.
Daga nan wadanne aikace-aikace kuka gabatar?
Mun tattauna da BSO, daga nan muka yi talla marar hoto mai motsi, sannan muka kira ga masoyanmu, idan har kai masoyina ne, to ina neman alfarmar ka zabi Buhari da APC. Bayan wannan sai muka yi na bidiyo wanda shi ne ake ta yadawa, wannan da yawunmu gaba daya masu shirya fina-finan Hausa na Kannywood aka yi shi. Wannan ra’ayinmu ne, kowa yana da damar da zai iya son wanda ya ga dama.
Kana da labarin wata Kannywood din ta je fadar shugaban kasa har ta yi wa matar shugaban kasa Dame Patience alkawarin za ta zabi mijinta?
Na kalli lokacin da ake yada shirin kai-tsaye a talabijin, na riga na ba ka amsa kowa yana da ra’ayinsa.
A cikin wadanda kuka sa a ciki tallarku kamar Halima Atete da Nafisa Abdullahi suna cikin wadanda suka je fadar shugaban kasa, me za ka ce a kan hakan?
Wannan babu gardama, ni ma na gani, na samu labara watakila ya zama gaskiya ko karya, an ce an yi musu alkawarin za a ba su miliyan daya kowannensu, don su halarci wannan taron, amma sai aka ba su Naira dubu 200, daga baya na samun labari an ce sun yi da-na-sanin zuwa. Abin jira kawai shi ne za mu gani ko za su yi Jonathan talla, ko za su ci gaba da yi wa Buhari talla.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa