Dalilin da ya sa na ajiye limancin masallacin Jami’ar ATBU — Farfesa Yelwa

Malamin ya ce gina sabon masallaci a jami’ar zai haddasa rarrabuwar kawuna.

Dalilin da ya sa na ajiye limancin masallacin Jami’ar ATBU — Farfesa Yelwa

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Farfesa Mansur Isa Yelwa, ya bayyana dalilin da ya sa ya yi murabus daga muƙaminsa na Babban Limami kuma jagoran ayyukan wa’azin Musulunci a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi.

Ya sanar da murabus ɗinsa ne lokacin da yake huɗuba a ranar Juma’ar da ta gabata.

Farfesa Yelwa, ya bayyana cewa ya sauka ne bayan da hukumar jami’ar ta amince wa ƙungiyar ɗalibai ta ɗarikar Tijjaniyya su gina masallacinsu na musamman a cikin jami’ar.

Ya bayyana cewa jami’ar ba ta nemi shawararsa ba kafin ta yanke wannan hukunci.

Farfesan, ya ce akwai fargabar samun rabe-raben masallatai na ɓangaranci wanda zai haifar da tsaiko wajen zaman lafiya da haɗin kai a jami’ar.

Ya yi gargaɗin cewa idan har aka samar wa ɗarikar Tijjaniyya masallacinsu, to nan ba da daɗewa ba sauran ƙungiyoyin kamar Izala, Salafiyya, da Shi’a za su nemi a ba su filin don gina nasu.

Farfesa Yelwa, ya bayyana cewa ya shafe shekaru 17 yana tafiyar da masallatan jami’ar da kuma haɗa kan ƙungiyoyin Musulmi daban-daban.

Ya bayyana cewa ba zai koma kan muƙaminsa ba har sai idan hukumar jami’ar ta janye amincewar da ta bayar na gina sabon masallacin.