Dalilin da ya sa na bar aikin dan sanda na koma fim – Bashir kaya
Muhammad S Bashir wanda aka fi sani da Bashir kaya fitaccen jarumin fina-fanan Hausa ne. A hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana dalilin da ya sa ya bar aikin dan sanda zuwa harkar fim da nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da harkar ke fuskanta a […]
Muhammad S Bashir wanda aka fi sani da Bashir kaya fitaccen jarumin fina-fanan Hausa ne. A hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana dalilin da ya sa ya bar aikin dan sanda zuwa harkar fim da nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da harkar ke fuskanta a yanzu.
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Muhammad Shitu Bashir. An haife ni a unguwar kofar Gayan da ke birnin Zariya, na yi makarantar firamare da sakandare. Na yi Difloma a Kwalejin Koyon Aikin Gona da ke Zariya. A shekarar 1992 na shiga aikin dan sanda wanda ya kai ni garin Kano, ina cikin haka ne sai na fara sha’awar in yi fina-finan Hausa, daga nan na bi dukkan hanyoyin da suka dace har na fara fitowa a fina-finan Hausa. Bisa la’akari da cewa ba a hada taura biyu a baka, sai na koma harkar fina-finan Hausa gadan-gadan. Na fara harkar ne a shekarar 1999 da wani fim mai suna ‘Mahandama’.
Yawan fina-finan da na fito a ciki
Akalla za su kai guda 60. Kuma fim din farko da na fara shiryawa da kaina shi ne ‘kaya’.
Dalilin lakabin kaya
Na samu lakabin Bashir kaya ne, sakamakon fim din da na shirya mai suna ‘kaya’.
Nasarori
Babbar nasarar da nake ganin na samu ita ce zama dan wasan Hausa, saboda wannan buri ne da nake da shi a zuciyata da dadewa. Nasara ta biyu ita ce, yadda na samu suna Gabas da Yamma; Kudu da Arewa.
kalubale
Babu wani kalubale da zan ce na fuskanta a sana’ar nan. Amma abin da ke ci wa masana’antar fina-finan Hausa tuwo a kwarya shi ne, rashin kyakkyawan shugabanci, ba mu da jagorori a kungiyance. Saboda wadanda ke jagorantar mu a yanzu, shugabanni ne da suka shigo da siyasa cikin harkar. Ya kamata a ce dan wasa na kowa ne, kuma idan yana da ra’ayin wata jam’iyyar siyasa, bai kamata ya bayyana ta ga duniya ba saboda shi mutum ne da ke so ya tafi da kowa da kowa. Ya dace shugabanninmu su raba harkar fim da siyasa domin ci gabanmu.
Inda na koyi rawa da iya fada
Ra’ayin rawa ya samu asali ne tun kafin shiga ta harkar fim, saboda tun muna yara, mukan shirya kade-kade da raye-raye tsakankaninmu don fitar da gwanaye. Wannan ya yi tasiri sosai a kaina. Maganar iya dembe kuma ko fitowa a matsayin jarumi a fim, zan iya cewa a jinina yake, musamman ma saboda yadda nake yawan kallon fina-finan kasar Sin.
Dalilin da ya sa kwana biyu ba a jin duriyata
Ita sana’ar ta gaji haka, saboda yadda ta kunshi hawa da gangara. Amma ba wai na bar harkar ba ne. Kuma ko a yanzu akwai fina-finai sababbi da na fito a ciki kamar su: ‘Basaja’ da ‘ Na Cuci Kaina’ da ‘Wankan Gida’ da ‘Jadina’ da sauransu.
Burina
Ina da burin koma wa makaranta don ci gaba da karatuna. Kodayake babban burina a yanzu shi ne, in gan ni a masa’antar shirya fina-finai ta duniya (Hollywood).
Iyali
Ina da mata daya da ’ya’ya biyu.