Dalilin da ya sa na daina bara na koma sayar da jarida- Ibrahim dan-majago

Aminiya ta samu tattaunawa da wani dan shekara 18 da ke aji 3 na karamar sakandaren gwamnati mai suna Ibrahim Muhammad Bello da ake wa lakabin ‘dan-majago’ da ke garin Azare a Jihar Bauchi. Matashin wanda nakasasshe ne maimakon ya ci gaba bara sai ya fara sayar da jarida domin dogaro da kansa. Ga yadda […]

Dalilin da ya sa na daina bara na koma sayar da jarida- Ibrahim dan-majago
Dalilin da ya sa na daina bara na koma sayar da jarida- Ibrahim dan-majago

Aminiya ta samu tattaunawa da wani dan shekara 18 da ke aji 3 na karamar sakandaren gwamnati mai suna Ibrahim Muhammad Bello da ake wa lakabin ‘dan-majago’ da ke garin Azare a Jihar Bauchi. Matashin wanda nakasasshe ne maimakon ya ci gaba bara sai ya fara sayar da jarida domin dogaro da kansa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Me ya jawo hankalinka har ka fara sayar da jarida maimakon bara?
Ibrahim: To a gaskiya gani na yi in fara sana’a ta fi mini a’ala maimakon bara, domin bara ba sana’a ba ce, hasali ma tana kawo kaskanci ga masu yinta, duk da cewar wadansu ba a son ransu suke yi ba, rashin samun tallafin yin sana’a ne, domin a baya na fara bara, to amma daga bisani da na ga ’yan uwana ba su son in yi bara, sai kawai na yanke shawarar in nemi sana’ar yi, to shi ne, na fara sayar da jarida.
Aminiya: Me ya sa ka yanke shawarar fara sayar da jarida tun da hakan na bukatar yawo?
Ibrahim: Eh lallai haka ne, amma duk abin da aka ce sha’awa ai ta kawar da komai, kuma na ga zan iya ne shi ya sa na fara wannan sana’ar, sannan a lokacin da nake bara ai a wannan gidan mai na MEGA nake yi, lokacin kuma muna tare da masu sayar da jaridar a nan, to tun a lokacin nake sha’awar yin wannan sana’a, daga baya ne na samu maigidansu, sannan na ce ya rika ba ni jaridar in rika sayarwa, ya amince mini, ya fara ba ni, wanda a yanzu haka na zama dan gari a kan wannan harka, tun da yanzu na shafe ku san shekara 5 ke nan.
Aminiya: Ko lokacin da ka ce za ka fara sayar da jarida ka samu wata tirjiya daga magabatanka?
Ibrahim: A gaskiya ban samu wata tirjiya ba duk da cewar mahaifina  baya raye, amma mahaifiyata ta ba ni goyon baya tare da karfafa mini gwiwa a kan hakan, don dogaro da kaina maimakon ci gaba da bara, kuma alhamdulillahi ina samun abin kashewa.
Aminiya: Ko ka gamsu dangane da sayar da jaridar da kake yi?
Ibrahim: kwarai da gaske ina matukar samun gamsuwa daga wannan sana’a ta sayar da jarida, domin da farko duk yawan jaridun da na dauka ban taba kasa sayar da su ba, musamman jaridar Aminiya da Daily Trust da makamantansu, don kullum mutane sukan tsaya domin sayan jarida a wurina fiye da sauran abokan sana’ata masu kafa.
Aminiya: Ko me ya sa ka fi su samun ciniki?
Ibrahim: Zan iya cewa watakila mutane na yawan saya a wurina ne saboda lururar da nake fama da ita, kuma abin ma sha’awa yake ba ’yan uwana wadanda muke irin wannan sana’a, suna tallafa min don ganin na sayar da tawa jaridar, kuma a gaskiya da abin da nake samu  mafi yawan lokaci nake tallafa wa mahaifiyata da kuma kudin kashewa na makaranta da dan abin da ba a rasa ba.