Dalilin da ya sa na fara daraktin fim – Hauwa Maina

Hajiya Hauwa Maina fitacciyar jaruma kuma furodusar fina-finan Hausa ce. A kwanakin baya ta fara ba da umarni. A zantawarta da Aminiya ranar Lahadin da ta gabata a Kaduna, ta bayyana yadda ta fara harkar fim da irin kalubalen da ta fuskanta a harkar da kuma dalilan da suka sa ta fara ba da umarni. […]

Dalilin da ya sa na fara daraktin fim – Hauwa Maina
Dalilin da ya sa na fara daraktin fim – Hauwa Maina

Hajiya Hauwa Maina fitacciyar jaruma kuma furodusar fina-finan Hausa ce. A kwanakin baya ta fara ba da umarni. A zantawarta da Aminiya ranar Lahadin da ta gabata a Kaduna, ta bayyana yadda ta fara harkar fim da irin kalubalen da ta fuskanta a harkar da kuma dalilan da suka sa ta fara ba da umarni. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu fara da tarihinki a takaice?
Assalamu alaikum da farko dai sunana Hauwa Maina, an haife ni a Jihar Kaduna, amma ni ’yar asalin Jihar Barno ce. Na yi makarantar firamare da sankandare, bayan haka ne na wuce Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna (Kaduna Polytechnic), inda na samu takardar shaidar difloma a fannin Dabarun Tafiyar da Al’amura wato (Management). Kodayake daga bisani na shiga harkar fim, inda na fara da wani fim mai suna suna, ‘Tuba’ a shekarar 1999. Fina-finan da na fito za su kai kimanin guda 50. A yanzu haka na kammala wani fim dina mai suna ‘Rai da So’, wadda gaf yake da shiga kasuwa.
Har ila yau, a yanzu bayan fitowa da nake a matsayin jaruma, ina shiryawa da kuma ba da umarni a fina-finai.
Me ya ja hankalinki zuwa aikin ba da umarni a fina-finai?
Hakan ya samo asali ne daga wata dama da na samu, inda aka ba mu horo a kan aikin a Jihar Legas, wadanda suka jagoranci kwas din kuwa wasu Turawa da suka zo daga birnin New York da ke kasar Amurka. A lokacin mun kwashe kimanin wata daya ana ba mu horo kan kabli da ba’adin aikin. Ka ga ba da ka na shiga fannin ba, na karbi irin horon da ya dace.
Kodayake zan iya cewa sha’awa ce ta sa ni shiga aikin, kuma akwai mata da dama da suke wannan aikin, wannan ya sa na ga ni ma me zai sa a bar ni a baya. Kuma Alhamdulillahi, na samu dukkan goyon bayan da ya kamata daga gare su.
Wadanne fina-finai kika yi daraktin?
A gaskiya har yanzu ina aiki ne a kan fina-finaina, wani bai taba kira daga wani wuri don ya ba ni aiki ba. Saboda idan ba mutane sun ga fina-finanka sun fita ba, wato sun ga irin kamun ludayinka, sannan ne za su fara ba ka aiki. A yanzu dai ayyukana ne nake yi tukuna.
Me ye gaskiya batun da ake cewa kina daya daga cikin ’yan wasan Hausa 19 da za su je kasar Indiya kwas?
Gaskiya ne. Har ila yau, za mu je don halartar wani horo kan aikin daraktin da kuma sauran harkokin fina-finai baki daya. Za mu yi kimanin wata guda a can. Kodayake ba ni kadai zan amfana da wannan horon ba daga arewacin kasar nan. Akwai sauran wadanda za mu yi tafiyar tare kamarsu: Ali Nuhu da Ibrahim Mandawari da Hamisu Lamido Iyan Tama da Ishak Sidi Ishak da Mustapha Musty da dai sauransu. Kuma za mu je ne karkashin Gwamnatin Tarayya a shirinta na Nollywood Project Act, wadda ta kirkiro domin tallafa wa masana’antar fim a Najeriya.
Idan muka dawo bangaren sana’arki wadanne irin kalubale ne kika fuskanta?
Ahamdulillah, babu abin da zan ce sai dai godiya ga Ubangiji, saboda ba yadda mutum zai rayu ba tare da fuskantar kalubale ba. Amma muna ta kokarin shawo kansu, musamman ma da yake kowane kalubale da zai bijiro, idan aka yi hakuri da yardar Allah za a ga bayansa. Hakan muka yi har Allah ya kawo mu yanzu.
Batun nasarori fa?
A gaskiyar magana ba sai na lissafa ba, saboda nasarorin suna nan birjik, sai dai mu gode wa Allah mu kuma gode wa jama’a, saboda yadda suke nuna mana kauna. Misali idan da zan fita neman wani abu, albarkacin wannan sana’ar za ka ga na samu cikin sauki. Na samu kyautar jarumar-jarumai a shekarar 2010, wato (SIM awards) a birnin Landan.
Kina da wani kira ga sauran abokan sana’arki?
Baban kirana a gare su bai wuce na ja hankalinsu kan muhimmancin hadin kai da tafiya a kungiyance ba. Saboda a gaskiya idan har ba mu hada kanmu ba, to a kullum za mu ci gaba da kasancewa koma-baya tsakankanin tsararrakinmu. Wani karin jan hankalin da zan yi kuma shi ne, yana da kyau mu rage kwadayi ko son shugabanci, saboda yadda hakan yake ci gaba da kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninmu. Ga duk wani da ke da sha’awar shugabanci, ya bari jama’a su bukace shi da ya yi hakan bayan sun yi na’am da halayyarsa da kuma kyawawan dabi’unsa.
Mene ne gaskiyar batun kin fara shirye-shiryen daukar wani fim da yaren Babur?
Haka ne. Kuma zan yi hakan ne saboda irin sha’awar da nake da ita ta tallata harshena.
Me ya sa sai yanzu ne za ki yi hakan?
Saboda komai nazari ake a kansa. Kuma dole sai mutum ya yi aiki tukuru waje lalubo ’yan wasa, ko kuwa za ka koya wasu yaren ne, a’a, zuwa za ka yi ka same su a can. Duka wadannan abubuwa ne da dole mutum ya yi la’akari da su, kuma abubuwa ne da wajibi ne su dauki lokaci mai tsawo. Da farko ma sai ka yi nazarin da wane irin labari za ka fara. Na biyu da su waye za ka gudanar da aikin, idan dauko mutane za ka yi daga nesa, dole ne ka tanadar masu da wurin kwana da abincin da za su ci da sauransu. Wannan ya sa ba karamin aikin ba ne da mutum zai gudanar cikin hanzari.
Cikin fina-finanki, akwai wanda kika fi so?
A’a, duka fina-finan da nake ciki ina kaunarsu gaba daya, amma na fi son wadanda suka danganci tarihi da kuma al’adunmu na gargajiya. Dalilin da ya sa na fi sonsu shi ne, irin dimbin darussan da suke tattare da shi. Misali kamar fim din ‘kueen Amina’ da ‘Daurama’ da na fito a ciki, fina-finai ne da suke sa yaranmu kanana su ilmantu matuka. Akwai wasu iyayen da suka taba kira na suna bayyana mini irin farin cikinsu saboda yadda ’ya’yansu suka fa’idansu a makaranta sakamakon kallon wadannan fina-finan biyu. Ka ga akwai fa’ida sosai da yaranmu suke samu daga irin wadannan fina-finan.