Dalilin da ya sa na fara fim din Hausa-Nkem Owoh
Nkem Owoh fitaccen dan wasan barkwanci da ke Kudancin Najeriya ne, ya yi fitattun fina-finan barkwanci da suka hada da ‘Osoufia In London’ da ‘Ukwa’ da sauransu. A kwanakin baya ya yi fim din Hausa mai suna ‘Maja’. Ya bayyana wa wakilinmu dalilin da ya sa ya fara fim din Hausa, ya kuma tabo wadansu […]

Nkem Owoh fitaccen dan wasan barkwanci da ke Kudancin Najeriya ne, ya yi fitattun fina-finan barkwanci da suka hada da ‘Osoufia In London’ da ‘Ukwa’ da sauransu. A kwanakin baya ya yi fim din Hausa mai suna ‘Maja’. Ya bayyana wa wakilinmu dalilin da ya sa ya fara fim din Hausa, ya kuma tabo wadansu batutuwa.
Daga Bashir Musa Liman, a Kano
Yaya ka ji da aka gayyace ka fim din Hausa?
Ban daga hankalina ba, na dai yi zamudin na fahimci yaya fim din Hausa yake? Kowa da ka gani yana son ya samu canji. Na saba da fina-finan barkwanci na Turanci, sai na rika tunanin yaya na Hausa zai kasance? Amma kasancewata jarumin da ya yi gwagwarmaya a harkar fim sai na ce wa kaina zan iya, domin jarumai a duniya sun yi fina-finai ba da yarensu ba, sai hakan ya ba ni karfin gwiwa.
Da yaya ka iya karanta labarin fim din ko da ma ka iya karatun Hausa?
Tsarina ne na karanta labarin fim don na fahimci inda ya dosa kafin na yi, don haka bayan sun kira ni ne suka ce zan yi fim din Hausa, sai na ce musu ta yaya zan fahimci jigon labarin? Sai suka ce mini za su turo mini da na Turanci na karanta. Bayan sun turo mini na karanta ne sai labarin ya burge ni, wanda kuma ga shi da idanunka ka ga ina yi.
Ga shi ba ka jin Hausa, amma kuma ka fara fim din Hausa, yaya ka iya magana da yaren ke nan?
Duk lokacin da aka zo fitowa ta gaba, zan tambaya me za mu yi? Sai a fada mini da Turanci, sannan a fassara mini me zan ce da Hausa, haka na rika yi.
Wannan ya sanya ka sha wahala ke nan?
Ban yi tsammanin zai yi mini sauki haka ba ma, kalmomin Hausa ba su da wuyar furuci don haka al’amarin ya zo mini da sauki.
Mene ne bambanci fina-finan barkwanci na Kudanci da na Hausa?
Babu bambanci sosai duka fina-finan ana yi don nishadantarwa ne, sai dai wannan Turanci ne, wannan kuma da Hausa.
Batun kayan aiki fa?
Kusan duk daya ne, bambanci babu yawa.
Ga shi na ganka sanye da kayan Indiya yaya ka ji a wannan lokacin?
Babu wani abu da na ji saboda yanayin rol din ne ya zo da haka. Rol din da nake takawa a fina-finai ai ba halina ba ne haka labaran suka zo da shi, don haka babu wani abu da na ji. Amma dai na kalli madubi na ga kayan sun yi mini kyawu. Jama’a da yawa kuma da suka gan ni sai suka rika dariya, hakan ya tabbatar mini idan ‘yan kallo suka kalli fim din zai kayatar da su. Dama kuma ba ni da wani buri a harkar fim face na nishadantar da ’yan kallo.
Mene ne ya fi bakanta maka rai a harkar fim?
Abin da yake ci mini tuwo a kwarya shi ne komai na yi a zahiri ba wai a fim ba sai a mayar da shi abin dariya, akwai lokacin da na je coci sai limamin cocin ya ce na yi addu’a, bayan na tashi, jama’a sun tashi ne sai na rufe idanuna, daga nan sai na ce ‘Muna cikin addu’a’, kawai sai aka fara dariya. A wurina wannan ba abin dariya ba ne, na samu ire-iren wadannan da yawa, sau da yawa idan na yi magana ba a daukarta da muhimmanci sai a rika dauka a cikin fim ne.
Shin za ka ci gaba da yin fim din Hausa?
Idan aka ci gaba gayyata ta na kuma ga labarin ya dace da ni zan yi mana. Ka gane ko a Kudu ba kowane fim nake yi ba har sai labari ya dace da ni.
Wa ya fi burge ka a cikin jaruman fina-finan barkwanci na Hausa da ka yi aiki da su?
Dukkansu sun yi kokari amma Sallau (Ibro) ya burge ni sosai, sai Baban Chinedu idan yana magana ba za ka taba cewa ba Inyamuri ba ne, sun burge ni sosai.
Ga shi tun da aka fara wannan hadaka tsakani Arewa da Kudu, ‘yan fim din Hausa ne suke gayyatarku, inda suka gayyaci Aki da Popo da John Okafor da Jim Iyke ga shi yanzu kuma an gayyace ka, shin kuna da yunkurin gayyatar wasu ‘yan wasa daga nan Arewaci?
Mun yi wannan yunkurin, nan ba da dadewa za mu yaukaka dangatakarmu, kuma idan ba za ka manta ba ai mun taba gayyatar Baba Ari wani fim inda ya fito a matsayin boka.