Dalilin da ya sa na karkata ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata – Bashir Datti

Fitaccen furodusa Bashir Datti ya ce ya karkata ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata ne saboda dimbin matsalolin da ake samu a rayuwar aure.Furodusan dan asalin Jihar Filato da ke da zama a garin Jos ya ce yakan kasance cikin bakin ciki da takaici a duk lokacin da ya ga ko ya ji labarin […]

Dalilin da ya sa na karkata ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata – Bashir Datti
Dalilin da ya sa na karkata ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata – Bashir Datti

Bashir Datti (a dama) tare da Ali NuhuFitaccen furodusa Bashir Datti ya ce ya karkata ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata ne saboda dimbin matsalolin da ake samu a rayuwar aure.
Furodusan dan asalin Jihar Filato da ke da zama a garin Jos ya ce yakan kasance cikin bakin ciki da takaici a duk lokacin da ya ga ko ya ji labarin ma’aurata suna cikin matsala ko kuma aure ya mutu.
“Idan ka bincika za ka samu kowane gida akwai matsalolin da suke ci wa ma’aurata tuwo a kwarya. Wani lokaci daga bangaren miji; wani lokaci daga bangaren mata, inda wani lokaci kuma dukkan ma’auratan ne ke da matsala. Don haka duk lokacin da na ga ko na ji labarin mutuwar aure ko samun sabani tsakanin ma’aurata sai in ji bakin ciki da takaici sun mamaye ni.” Inji furodusan.
Ya ce a dalilin haka sai ya mayar da hankalinsa ga shirya fina-finan da suka shafi ma’aurata don a gudu tare a tsira tare, kasancewar gida ya zauna lafiya, komai zai tafi daidai ba tare da matsala ba.
A karshe ya bukaci ma’aurata su rika tattauna matsalolinsu don su samu fahimtar juna, sannan su rika hakuri da juna.