Dalilin da ya sa na kirkiro rubutun Tafi -Musa Abdullahi
Musa Abdullahi shi ne wanda ya kirkiro wani sabon rubutu da ya sanya wa suna Tafi, ya yi digiri na daya a kan Kimiyyar Physics da na biyu a kan Sadarwa da kere-kere. Ya yi bayanin dalilin da ya sa ya kirkiro rubutun Tafi, matsalolin da ya fuskanta, burinsa dangane da rubutun da kuma dalilin […]
Musa Abdullahi shi ne wanda ya kirkiro wani sabon rubutu da ya sanya wa suna Tafi, ya yi digiri na daya a kan Kimiyyar Physics da na biyu a kan Sadarwa da kere-kere. Ya yi bayanin dalilin da ya sa ya kirkiro rubutun Tafi, matsalolin da ya fuskanta, burinsa dangane da rubutun da kuma dalilin da ya sa ya shigar da harsunan Yarabanci da Ibo cikin rubutun
Aminiya: Ko za mu ji tarihinka?
Assalamu alaikum, sunana Musa Abdullahi, an haife ni a Katsina a shekarar 1941. Na yi makarantar Elimentari ta Kayalwa da ke Katsina, sannan na yi makarantar Midil ta Katsina, sai kuma kwalejin Barewa. Bayan na kammala sai na samu gurbin karatu a Jami’ar Manchester da ke Ingila. Na yi digirina na farko a kan Kimiyyar Physics, na biyu kuma a kan Sadarwa da kere-kere. Na yi aikin koyarwa a makarantar Sakandare ta Funtuwa da Makarantar Tarayya da ke Sakkwato da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Daga nan na koma aikin gwamnatin har zuwa ritaya a shekarar 2000. Matsayin da na rike na karshe shi ne, Daraktan Sashin Ba da Ayyukan Injiniyoyi a karkashin Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da ke Abuja. Bayan na yi ritaya sai na yi aiki kadan da Jami’ar Fasaha ta Minna, a Jihar Neja. Yanzu kuma ina yin duk wani aiki da ya samu.
Aminiya: A kwanakin baya aka buga tallar tsarin rubutun Tafi da ka kirkiro a jaridu, shin tun wane lokaci ka fara aikin tsara rubutun?
Na fara tunanin kirkiro rubutun ne tun ina Jami’ar Manchester a Ingila, abin da ya kawo wannan kuwa shi ne, duk inda mutum ya shiga a lokacin sai a rika tambayarsa ko yana da yare, a lokacin akwai wadansu abokaina Turawa da na taba nuna musu rubutun Hausa, sai suka ce mini ai mun aro ne daga rubutunsu na Latin. Na sake nuna musu na Ajami, sai suka ce mun aro daga Larabawa ne. Tun daga lokacin na yi alkawarin kago sabon rubutun Hausa, wanda zai kunshi duk wadansu abubuwa nagari game da rubutun boko.
Aminiya: A wacce shekara ke nan ka fara tsara rubutun Tafi?
Na fara tsara rubutun ne a shekarar 1962, amma bai fito sosai ba sai lokacin da na rubuta wani littafi mai suna ‘A Study Of Writing & Debelopment Of Tafi’ a shekarar 1988.
Aminiya:Me ya ja hankalinka har ka kirkiro wannan rubutun?
Babu wani abu mai muhimmanci a duniya da ya wuce rubutu, domin sai da shi ne za ka isar da sakonka yadda ya kamata, kamar yanzu ne da duniyar nan ta kasance ta kirkire-kirkire, to idan babu rubutu hakan ba zai samu ba. Daraja da muhimmancin rubutu ne ya sanya na kirkiro rubutun Tafi.
Aminiya: Ta yaya wannan tsarin rubutun ya samu sunan ‘Tafi’?
Ya samu ne daga sunan littafi, sannan yana da nasaba da tafin hannu, shi ya sa a jikin bangon littafin akwai zanen tafin hannu. A yanzu an fadada shi ya kunshi yaren Ibo da kuma Yarabanci. Ina fata kuma nan gaba zan hada shi da sauran yarurrukan Najeriya.
Aminiya:Wane kalubale ka fuskanta wajen kirkiro rubutun Tafi, kasancewar ka dauki lokaci mai tsawo kafin ka fito da shi?
Idan za ka fito da wani sabon abu dole ya zama yana da tasiri, zai zamana ya fi sauran wadanda kake so ka maye. Na dauki lokaci ina nazarin hanyoyin rubutu iri-iri na duniya, tun daga rubutun mutane Masar na da can, wanda ake kira Hieroglyph da rubutun mutanen Fasha da Sinawa da sauransu.
Aminiya:Ko za a ce ayyukan gwamnatin da ka yi ne ya sanya ka dauki lokaci mai tsawo kafin ka fitar da rubutun Tafi, ko kuma tunanin yadda tsarin rubutun zai kasance ne ya haifar da tsaikon fitowar rubutun?
Na fara yunkurin fito da wannan rubutun ne fiye da shekara 40 da ta gabata. Za a iya cewa hakan ayyukan da na yi ne, kasancewar ba koyaushe nake yin aikin tsara rubutun ba. Duk lokacin da hali ya samu sai in yi. Tun ina Shugaban makarantar share fagen shiga jami’a (CAS) da ke Zariya na fara fito da rubutun.
Aminiya:Ko a yanzu haka akwai wadanda suke amfani da rubutun?
Tun ina shugaban Makarantar CAS ta Zariya muke musayar sakonni da wadansu dalibaina. Akwai mutanen da muke ci gaba da musayar sakonni da su har yanzu, amma ka sani duk wani abu sabo kan dauki lokaci kafin a san shi har a fara amfani da shi. Na kirkiro wannan rubutun ne saboda yara. Tsofaffi ko wadanda suka manyanta da wuya ka ce su zo su koyi rubutun Tafi.
Wani abu da nake so mutane su gane shi ne, rubutun Tafi ya fi rubutun boko na Hausa sauki nesa ba kusa ba. Zai yi saukin koyo ga yara.
Ko ka fuskanci kalubale daga malaman jami’o’i dangane da wannan sabon rubutun?
Sun gayyace ni a wata laccar da aka yi a Jami’ar Jihar Kaduna, kamar shekara uku da suka wuce. Na kuma yi lacca a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’ aduwa da ke Jihar Katsina da sauran makarantu. Sun yi mini tambayoyi iri-iri, inda amsoshinsu suka gamsar da su.
Aminiya:Bayan sun gamsu, shin sun amince za su rika koyar da shi a jami’o’i ko kwalejoji ko kuma makarantun sakandare?
Gaskiya ba su yi hakan ba, amma tun da na yi ritaya zan koma gida in gina makaranta, in rika koyar da rubutun Tafi. Watakila wannan makaranta ta zama cibiyar koyon Tafi.
Aminiya: Ko ka yi yunkurin wajen ganin gwamnati ta sa a rika koyar da rubutun a makarantu?
Ka sani abu sabo yana da wuyar sha’ani. Gwamnati ba za ta ce a rika koyar da shi ba, sai ta ga inda ya nufa tukunna.
Aminiya:Bayan ka fito da tsarin rubutun Tafi, da yaya ka sanya shi a kwamfyuta kasancewar bakon abu ne gare ta?
Shi Tafi ana kammala shi ne daga alamomi shida ne kawai.Idan ka dauki abu shida ka sanya su biyu-biyu, to za ka samu abubuwa 36. Wadannan abubuwa shida su ne wasulla, wato a, e, i, o, u, d. Idan ka hada su biyu-biyu aka samu 36 sai su zama haruffa. Wadannan an zauna an kago su ne. Kodayake wadannan wasulla sun yi kama da wasullan rubutun boko. Bambancin shi ne, daga wadannan alamomi 6, su ne yaro zai koya.Haka za a rika hada su.Wadannan abubuwa 36 sun isa a yi rubutu da su cikin harsunan Najeriya.
Aminiya:Shin ko ka shigar da rubutun Tafi zuwa ga kasashen Ibo da kuma Yarabawa?
Ina da abokai Ibo da Yarabawa wadanda suka taimaka aka fara Ibo da Yarabanci cikin rubutun Tafi. Na shigar da wadannan harsuna ne, don in hada kan mutanen kasar nan, kasancewar idan muna da rubutu iri daya, ai ka ga an fara samun hadin kai ke nan, ya zama wata rana wadannan harsunan za su hadu, sai ka ga harshe daya ya fito na Najeriya. Watakila mutane ba za su yarda da abin da nake fada ba, amma abu ne mai yiwuwa. Babu abin da ya fi rubutu dadewa, harshe zai iya mutuwa ya bar rubutu. Misali kamar rubutun Sinawa, harshen ya mutu, amma rubutun yana nan.
Aminiya:Idan mutum yana so ya yi amfani da rubutun Tafi a kwamfyuta yaya zai yi ke nan?
Tuni na kirkiro manhajar rubutun Tafi, kuma zan iya sanya wa mutum a kwamfyutarsa. Akwai shi a turakar intanet dina mai adireshi kamar haka: www.tafiwriting.com. Za ka iya mayar da rubutun boko na Hausa zuwa rubutun Tafi, har da ma na Turanci. Na ma sanya littafin da na buga a intanet din. Dalilin da ya sa na yi haka kuma shi ne, duk lokacin da sabon abu ya fito jama’a ba sa ba shi daraja, amma daga ya samu daukaka sai wani ya ce ka saci tunaninsa ne, amma idan yana intanet, to wannan ba zai taso ba.
Na samu takardun yabo daga kasashen New Zealand da Amurka da Birtaniya da Maldoba game da Tafi. Abin da ya ba ni takaici shi ne, lokacin da na fara saka rubutun a intanet na samu sakonni 300 daga Amurka, amma 5 kawai na samu daga Najeriya.
Aminiya:Ko me wasikun da ka samu suka kunsa?
Wasiku ne da suka kunshi tambayoyi da yabo da karin bayani da sauransu.
Aminiya: Kana da shawara ga ’yan Najeriya?
Shawarata ita ce, mu dukufa wajen karatu don tafiya da zamani, domin ta haka ne za a dauke mu mutane kamar sauran mutanen duniya da suka samu ci gaba. Mutum zai ci gaba ne ta hanyar amfani da kwakwalwarsa.
A kuma fahimta ba sai an gina ajujuwa za a fara karatu ba, hakan ba daidai ba ne. za a iya karatu a ko’ina. Idan kuwa muka ce sai mun gina ajujuwa to ba za mu je ko’ina ba.