Dalilin da ya sa na koma ba da umarni – Nazifi Asnanic

Fitaccen mawakin fina-finan Hausa Nazifi Asnanic ya rikide daga mawaki zuwa mai ba da umarni, inda ya bayyana cewa tun fil’azal yake da sha’awar ya rika ba da umarni a fina-finai. Mawakin wanda ya shirya fina-finai irinsu Rai Da Buri, dakin Amarya, Shu’uma da sauransu a karkashin kamfaninsa mai suna Asnanic Mobietone zai ba da […]

Dalilin da ya sa na koma ba da umarni – Nazifi Asnanic
Dalilin da ya sa na koma ba da umarni – Nazifi Asnanic

Fitaccen mawakin fina-finan Hausa Nazifi Asnanic ya rikide daga mawaki zuwa mai ba da umarni, inda ya bayyana cewa tun fil’azal yake da sha’awar ya rika ba da umarni a fina-finai.

Mawakin wanda ya shirya fina-finai irinsu Rai Da Buri, dakin Amarya, Shu’uma da sauransu a karkashin kamfaninsa mai suna Asnanic Mobietone zai ba da umarnin ne a wani sabon fim din barkwanci mai suna Hedimasta.
Tun bayan rasuwar shahararren jarumin barkwanci Rabilu Musa Ibro, fina-finan barkwanci suka samu kansu cikin mawuyacin hali, kasancewar dukkan furodusoshi sun rasa yadda za su samo bakin zaren, wato su haifi jarumin barkwancin da zai maye gurbinsa, inda a halin yanzu wani kamfani ya yunkuro don raya fina-finan barkwanci.
Mawakin wanda a yanzu ya zama darakta, ya bayyana cewa tuntuni yake da sha’awar ba da umarni kuma furodusan fim din ya gamsu da cewa zai iya samar da abin da ake so ne ya sanya ya neme shi duk da cewa akwai daraktoci da yawa a masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood).
Ya ce: “Tun da duk wanda ya neme ka, kamar furodusa ya ce wane ina so ka yi mini daraktin fim dina, ka ga wata kila yana ganin kana da wata rawa da ka taba takawa wadda ya gane ka iya ko ba za ka iya ba, saboda idan har ya yarda ya kawo maka aikin, sannan ka karanta ka ga za ka iya, ganin na gamsu da labarin ne sai ya ja hankalina har na yanke shawarar ba da umarni a cikinsa.”
Dangane da batun jita-jitar da ake cewa kasancewar abokansa irinsu Aminu Saira da Ali Gumzak da Kamal S. Alkali dukkansu daraktoci ne sai hakan ya sanya ya ce bari ya fara ba da umarni sai ya ce, “ba haka ba ne, idan haka ne su me ya sa ba su fara waka ba? Ai ni ma abokinsu ne amma dai ina da sha’awar ba da umarni tun fil’azal.”