Dalilin da ya sa na koma makarantar koyon fim a Amurka – Ali Nuhu

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana cewa muhimmancin ilimi a kan sana’ar da mutum yake gudanarwa ne ya sanya ya koma makarantar koyon aikin fim da ke Jami’ar Kudancin Kalifoniya da ke kasar Amurka.Jarumin ya bayyana wa Aminiya haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinta a kafar sada zumunta a shafin […]

Dalilin da ya sa na koma makarantar koyon fim a Amurka – Ali Nuhu
Dalilin da ya sa na koma makarantar koyon fim a Amurka – Ali Nuhu

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya bayyana cewa muhimmancin ilimi a kan sana’ar da mutum yake gudanarwa ne ya sanya ya koma makarantar koyon aikin fim da ke Jami’ar Kudancin Kalifoniya da ke kasar Amurka.
Jarumin ya bayyana wa Aminiya haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinta a kafar sada zumunta a shafin Facebook a makon da ya gabata.
Jarumin ya tabbatar da cewa zai ajiye sana’ar fim na tsawon mako shida don ya samu damar samun ingantaccen ilimi a kan yadda ake shirya fim, inda zai taimaka masa ya rika tafiya da zamani a bangaren shirya fim, kuma hakan zai taimaka wa masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood.
“Komai mutum zai yi ka lura idan yana da wadataccen ilimi a kansa sai ya fi samun nasara. Ba zai yiwu ba ka da ilimin abu, sannan ka ce za ka samu nasarar a zo a gani a kansa ba. Hakan ya sanya na yanke hukuncin komawa Jami’ar Southern California da ke kasar Amurka don in karanci sabbin dabarun shirya fina-finai.
“Hakan zai taimaka mini sosai a bangaren samar da fina-finan da za su rika fitar da Kannywood kunya, sannan zai sanya fina-finan su rika gogayya da takwarorinsu a duniya, musamman ma wajen daukar fim ta hanyar amfani da kyamara.” Inji shi.
Jarumin ya roki masoyansa da su yi hakuri na rashin ganinsa da za su yi na wani lokaci, hakan yana da nasaba da ilimin da ya je karowa ne, kuma ya yi hakan ne don ya samar musu da fina-finan da za su rika yabo ba kushewa ba.
A karshe ya bukaci ’yan uwansa ’yan fim da su koma makaranta don neman karin ilimi a kan harkar fim, inda hakan ne kawai zai fitar musu da kidimammen jakin da ke gonar dumansu.