Dalilin da ya sa na koma Real Madrid -Gareth Bale
Jim kadan bayan da kulob din Real Madrid na Sifen ya lallasa na Bayern Munich da ke Jamus da ci 4-0 a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai a ranar Talatar da ta wuce ne Gareth Bale ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya canza sheka daga kulob din Tottenham na Ingila zuwa […]
Jim kadan bayan da kulob din Real Madrid na Sifen ya lallasa na Bayern Munich da ke Jamus da ci 4-0 a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai a ranar Talatar da ta wuce ne Gareth Bale ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya canza sheka daga kulob din Tottenham na Ingila zuwa na Madrid a bara.
Gareth Bale ya ce yadda ’yan kwallon Madrid suke tinkaho da zaratan ’yan  kwallo da kuma yiwuwar lashe manyan kofuna na daga cikin dalilan da suka sa ya yanke shawarar komawa kulob din.  Ya ce da alama hakarsa ta fara cimma ruwa musamman ganin yadda ya fara karya kumallo da kofin Sarki (Kings Cup) sannan akwai yiwuwar kulob din ya lashe kofin La-Liga da kuma na zakarun kulob-kulob da ke Nahiyar Turai a bana duk a kakar wasa ta bana.
Gareth Bale ne ya taimaka wa kulob din Madrid lashe kofin Sarki kimanin makonni uku da suka wuce a wasan karshe bayan ya zura kwallo ta biyu a ragar FC Barcelona kuma hakan ta sa aka tashi wasan da ci 2-1.
Kawo yanzu kofin da Madrid ta lashe shi ne Babban kofin da Bale ya taba lashewa  a tarihin kwallonsa.