Dalilin da ya sa na rubuta littafin ‘Dear Father’ – UK Umar

Usman Katun Umar wanda aka fi sani da UK Umar dan jarida ne da ya fada harkar rubuce-rubuce don ganin ya taimaka wajen ilimantar da mata da kuma iyaye. A hirar da Aminiya ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ya rubuta littafin ‘Dear Father’ da kuma burinsa a harkar rubuce-rubuce, ya […]

Dalilin da ya sa na rubuta littafin ‘Dear Father’ – UK Umar
Dalilin da ya sa na rubuta littafin ‘Dear Father’ – UK Umar

Usman Katun Umar wanda aka fi sani da UK Umar dan jarida ne da ya fada harkar rubuce-rubuce don ganin ya taimaka wajen ilimantar da mata da kuma iyaye. A hirar da Aminiya ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ya rubuta littafin ‘Dear Father’ da kuma burinsa a harkar rubuce-rubuce, ya kuma tabo batun dabi’ar karance-karance a yankin Arewacin Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka
UK Umar: Sunana Usman Katun Umar, amma an fi kirana da UK Umar. Ni dan karamar Hukumar Bida da ke Jihar Neja ne. Na yi digiri a kan kwas din aikin jarida (Mass Comm.), sannan na yi digiri na biyu a kwas din Debelopment Communication duka a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka fara rubuce-rubuce?
UK Umar: Zan iya cewa tun ina karami nake da burin yin rubutu da kuma yin aikin jarida, ga shi yanzu na cika burina, kasancewar ina aiki da wata ma’aikatar watsa labarai ne a Abuja. A lokacin da nake karatun kwas din Debelopment Communication ne, na lura da cewa muna da fikirar da za mu ciyar da al’ummarmu gaba. Wannan kuwa ya hada da mata da maza da yara har ma da manya. Hakan zai samu ne idan har aka ba mu damar da ta dace da mu. Sannan idan mata da maza suka hada hannu za a samu abubuwan ci gaba masu yawa.
Amma bayan na yi nazari sai na fahimci ba a ba mata damar da ta kamata don su nuna irin fikira da fasahar da suke da ita ta bangarori da dama. Hakan ne ya sa kuma dole maza ne suke daukar dawainiyar gidajensu.
Aminiya: Me ya ja hankalinka ka rubuta littafin ‘Dear Father?
UK Umar: Littafina na farko shi ne ‘Dear Father’. Na samu karsashin rubuta littafin ne sakamakon irin ukubar da mata da kuma kananan yara mata suka samu kansu a ciki a wannan zamani musamman ma a nan yankin Arewacin Najeriya.
Aminiya: Ko za ka fada mana abubuwan da littafin ya kunsa?
UK Umar: Idan ka lura da yawancin jihohin Arewacin Najeriya za ka fahimci babu wani abu da mata suka samu kansu a ciki face dogaro da wadansu, wannan kuwa ya faru ne tun suna kanana, hakan kuwa ya faru ne saboda  wa’azin dakushe mata da ake yi da kuma yanayin al’ada a yankinmu, inda ake ganin mata ba a bakin komai ba. An mayar da su ’yan aikin gida, abubuwan biyan bukatar sha’awa da kuma masu haihuwa kawai. Inda su kuma matan sun amince da hakan duk da cewa suna da fikirar da ta fi ta wadansu mazajen ma.
Amma a zahirin gaskiya shi ne, dukkanmu maza da mata an halicce mu da fikira da fasahar da za mu iya samun daukaka. Mata kamar maza suna da fasahar da za su taimaka don a samu bunkasa da tsayuwar al’umma. Amma hakan ba zai yiwu ba sai iyaye da sauran al’umma sun ba su goyon baya. Don haka littafin ‘Dear Father’ yana kira ne ga iyaye da kuma al’ummarmu su fahimci mawuyacin halin da mata da kuma kananan yara mata suke ciki.
Aminiya: Kafin  kai akwai marubuta da yawa da suka dauki wannan jigon, me ya bambanta naka da su?
UK Umar: Tabbas marubuta da yawa sun yi rubutu a kan wannan jigon, amma duk da haka akwai bukatar a ci gaba da rubutu a kan wannan jigon don a samu sauyi. Hakan ya sa nake kira ga mata marubuta na yankin arewacin Najeriya da su dage wajen rubuta littattafai a kan wannan jigon. Hakan zai taimaka wa mata masu tasowa.
Bambancin littafin ‘Dear Father’ da sauran littattafai a kan wannan jigon shi ne, wannan ya dauke da sako kai-tsaye ne daga ’ya zuwa mahaifinta. An yi amfanin da salon labari da ke daukar sako daga wata zuwa wani. Yaren littafin mai sauki ne, a bayyane yake, kuma zai ba makaranci damar fahimtar abin da ake nufi cikin sauki. A cikin littafin akwai wadansu kalaman da tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela ya yi da kuma nazarce-nazarce da Dokta Nadwi ya yi.
Yana dauke da darussa kan yadda mata musamman ’yan makarantar sakandare za su tafiyar da rayuwarsu, su iya mayar da hankali kan karatunsu duk da matsalolin da suke fuskanta. Za su ga dabarar da za su bi don yin karatu duk da bayyanar kafafen sadarwa na Facebook da Twitter da Instagram da sauransu. A littafin yarinyar mai suna Zainab ta bayyana yadda za a magance matsalar wadannan kafafen sadarwar.
Babin karshe na littafin mai taken ‘Father Please’, yana kunshe da gundarin sakon da littafin ke tafe da shi, sako ne mai dauke da roko ga iyaye da su bar ’ya’yansu su rika zuwa makaranta, inda hakan zai ba su damar samun kwarewa da kuma fasahar da taimakon al’umma da kuma bunkasa kasa ba wai kawai zama a gida ba. Babin ya kuma ga baiken irin malaman da ke nuna a hana mata karatu.
Aminiya: Me ya fi burge ka dangane da littafin?
UK Umar: Abin da ya fi burge ni da littafin shi ne, ba shi da yawa, sannan zayyanar bangonsa na dauke da sakon littafin, sannan bangon littafin yana jan hankali.
Aminiya: Wane tasiri kake ganin littafinka zai yi ga al’umma?
UK Umar: Littafin zai kasance daya daga cikin littattafan karatu ga mata da iyaye, sannan ta hanyar kudin da aka samu wajen sayar da littafin zan dauki nauyin karatun wadansu matan don su amfanar da al’umma. A yanzu da muke magana da kai ina ta kokarin binciko matan da suke makarantun gaba da sakandare da ba za su iya biyan kudin makaranta ba, ko wadanda ake kokarin korar su daga makaranta, ko wadanda sun kammala sakandare amma ba su da halin ci gaba da karatu saboda rashin kudin makaranta, zan yi amfani da kudin da na sayar da littafin don taimaka musu.
Aminiya: Wane sauyi kake so ka ga an samu a cikin al’umma?
UK Umar: Ba ni da wani buri face in ga an samu ci gaba a cikin al’umma, ba wai a ce muna cikin al’ummar da al’ada ta hana ci gaba ba, in ga al’umma sun tafi da zamani, ba wai zamani ya tafi ya bar su a baya ba. Burina in ga cewa kowa yana ba da gudunmuwarsa wajen ganin yankinmu ya bunkasa. Ina so in ga yankinmu kowa ya samu damar kawo ci gaba ba tare da la’akari da jinsi ba.
Aminiya: Yaya kake ganin dabi’ar karance-karance a yankin Arewacin Najeriya?
UK Umar: Na tabbata masu ilimi a yankin suna karatu, amma tabbas akwai bukatar a sake zage damtse wajen karance-karance, musamman ma idan aka lura za a ga akwai bambanci mai yawa tsakanin wadanda suka iya karatu da wadanda ba su iya ba. Abin takaicin ma shi ne idan ka lura da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, hakan ba karamin hadari ba ne, za a samu raguwar hakan ne idan aka samar da dokar da ta za ta tilasta wa yaranmu zuwa makarantu, sannan a samar da hanyoyin da za su saukaka tsadar ilimi a kasar nan, ko ta hanyar daukar nauyinsu ko kuma yi musu kyaututtukan da za ta sanya kowa ya rika sha’awar zuwa makarantu.
Aminiya: Ta wacce hanya kake ganin za a cusa wa mutane dabi’ar karance-karance?
UK Umar: Yana da kyau makarantunmu su rika shirya tarukan karance-karancen littattafai, ko shirya takaddama tsakanin dalibai, ko kacici-kacicin da ke bukatar mutum sai ya yi karance-karance da sauransu.
Sannan ya kamata a bude wata kafa da jama’a za su rika zuwa don karance-karance, sannan a samar da litattafai a dakunan karatu na makarantu da kuma na jama’a. Sannan za a iya shirya gasar karance-karance don a samu wanda ya fi kwarewa wajen karance-karance.
Sannan ya kamata iyaye su rika fahimtar da ’ya’yansu muhimmancin karance-karance, za su iya hakan ne ta hanyar saya musu littattafai.