Dalilin da ya sa na rungumi Musulunci – ’Yar fim Vivian Metchie

bibian Metchie, ’yar fim din Ingilishi daga Kudancin Najeriya ta bayyana cewa ta rungumi addinin Musulunci ne saboda ta samu gano cewa rudani ne cunkus a tsohon addininta na Kiristanci.A tattaunawarta da mujallar ‘Yes’ ’yar fim din ta ce ta dauki wannan mataki ne da kashin kanta. “Zabina ne na kashin kaina da na rungumi […]

Dalilin da ya sa na rungumi Musulunci – ’Yar fim Vivian Metchie

’Yar fim din da ta rungumi Musulunci, Vivian Metchie (Fareedah)bibian Metchie, ’yar fim din Ingilishi daga Kudancin Najeriya ta bayyana cewa ta rungumi addinin Musulunci ne saboda ta samu gano cewa rudani ne cunkus a tsohon addininta na Kiristanci.
A tattaunawarta da mujallar ‘Yes’ ’yar fim din ta ce ta dauki wannan mataki ne da kashin kanta. “Zabina ne na kashin kaina da na rungumi Musulunci. Idan ina karanta Alkur’ani, nakan fahimci sakonsa sosai fiye da Baibul. Ta haka ne na gano cewa babu abin da ke cikin Kiristanci sai rudani kuma idan na ci gaba da bin addinin, zan haukace. Babana Kirista ne, mabiyin darikar Katolika amma mahaifiyata ’yar darikar Deeper Life ce. Na zo na auri mijina, wanda shi kuma mabiyin ‘Redeemed Church ne.’ Haka kawai sai na ga wadannan dariku na la’antar juna, ni kuma na ga ba zan iya jure wa hakan ba.” Inji ’yar fim din.
Ta ci gaba da cewa: “Da na shaida wa wata kawata matsalar da nake ciki game da addinin Kiristanci, sai ta ce mini idan na zurfafa karatu, zan fahimta kuma ba zan kasance cikin rudani ba. Abin takaicin shi ne, na kasa natsuwa da abin da nake karantawa. Lokacin da na fara bincike, ina neman abin da zai sanya ni cikin natsuwa da lafiyar zuciya, ina cikin wannan bincike sai na hadu da Alkur’ani kuma nan ne na samu natsuwa da farin cikin da nake nema.”
bibian, wacce a yanzu ta canja sunanta zuwa Fareedah, tana da ’ya’ya hudu, ta bayyana cewa mahaifinta ya yi na’am da shigar ta Musulunci kuma yana mutunta ta da yin haka, wanda dalili ke nan ma yake kiran ta da sabon sunanta na Musulunci, Fareedah maimakon bibian.
Binciken Aminiya ya tabbatar da cewa ’yar fim din, wacce ta kasance jarumar fim din ‘Candle Light’ za ta dawo wa shirin fim kwanan nan. Wannan kuwa ya biyo bayan rabuwar ta da tsohon mijinta a bara.