Ina yin fim ne domin in taimaka wa addini —Maisana’a
Shaharren jarumin wasan kwaikwayo a masana’antar Kannywood, Musa Abdullahi Maisana’a, ya fadi musabbabin shigarsa sana’ar wasan Hausa. Maisana’a ya ce ya tsinci kansa a harkar wasan kwaikwayo ne saboda kasancewarsa mutum mai sana’o’i daban-daban kuma duk inda ya san zai samu dari-da-kobo zai shiga a dama da shi. Dan wasan ya ce a irin wannan […]
Shaharren jarumin wasan kwaikwayo a masana’antar Kannywood, Musa Abdullahi Maisana’a, ya fadi musabbabin shigarsa sana’ar wasan Hausa.
Maisana’a ya ce ya tsinci kansa a harkar wasan kwaikwayo ne saboda kasancewarsa mutum mai sana’o’i daban-daban kuma duk inda ya san zai samu dari-da-kobo zai shiga a dama da shi.
Dan wasan ya ce a irin wannan buge-bugen ‘a buga nan a buga can’ ne ya tsinci kansa a sana’ar fim kamar yadda ya shaida wa Sashen Hausa na BBC a wani hirar da suka yi.
Jarumin ya ce babban dalilinsa na shiga sana’ar fim shi ne yi wa al’umma da kuma yi wa addini hidima ba wai karan kansa kadai ba.
Sakamakon haka yake samun yabo daga wurin al’umma daidai gwargwado, duk da cewa duk abin da mutum yake yi ‘wani ba za ka yi masa ba’, a cewarsa.
“Ko wa’azi kake yi kana rataya gafaka a wuya, wani ba zai taba fahimtar ka ba”, inji shi.
Don haka ya shawarci al’umma da suka rika yi wa juna fatan alheri tare da furta alheri a kodayaushe, tare da cewa sharri a wani sa’ilin yana komawa izuwa dan aikensa.
Ya kuma yi hani gami da gargadi a kan aibata shugabanni tare da yin kira da a yi biyayya ga malamai da sarakuna.
Sannan kuma ya yi kira a kan al’umma su rika mutunta juna da kuma lura da ’ya’ya domin amana ce Allah Ya damka a hannun iyaye.
Maisa’ana mutumin jihar Kano ne, wanda aka haifa a Unguwar Arzai da ke Kofar Mazugal a Karamar Hukumar Dala da ke kwaryar birnin Dabo.