Dalilin da ya sa na shiga siyasa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa daya, kuma zabensa da aka yi a wannan karo ya nuna cewa ’yan Najeriya sun san abin da suke bukata. Janar Buhari ya bayyana haka ne a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu lokacin […]

Dalilin da ya sa na shiga siyasa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne domin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa daya, kuma zabensa da aka yi a wannan karo ya nuna cewa ’yan Najeriya sun san abin da suke bukata.

Janar Buhari ya bayyana haka ne a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu lokacin da yake ganawa da ’yan Najeriya mazauna kasar, bayan kammala taron kungiyar Tarayyar Afirka, inda ya ce, akwai wasu gurbabtattun mutane da suke son wargaza Najeriya saboda dalili na son kai, amma Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya.
“Zabena ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun san abin da suke bukata kuma da zarar sun daukar wa ransu, shi ke nan. Za ka iya ba su kudi, su ki amsa, wasu kuma su amsa, ka ji suna cewa ‘kudinmu ne’ amma daga karshe sai su aiwatar da abin da ya zama daidai.
“Don haka, me ya sa na shiga siyasa? A lokacin da na koma gida, mutane sun san cewa ba ni da dukiya kuma na dauka za su kyale ni haka nan in yi zamana. Amma sai suka ki yin haka, sai suka rika zuwa wajena suna ce mini in yi musu wannan, in yi musu wancan. Daga nan ne na fahimci cewa, hanya daya da zan iya biya musu bukata ita ce in shiga siyasa. A ganina, nan ne zan iya yin magana koda ni ba mai rike da wani matsayi ba ne, mutane za su saurare ni.”
Muhammadu Buhari ya kara da cewa: “Daga nan ne na shiga Jam’iyyar APP kuma daga farko ban yi niyyar takarar kowane mukami ba. Kuma da na so, da na shiga PDP a lokacin. Kila da na yi haka, babu mamaki da na zama Shugaban kasa tun can baya, to, amma na zabi in shiga jam’iyyar adawa.”
Buhari ya ci gaba da cewa: “Dalili na biyu da ya sa na shiga siyasa kuma na shiga jam’iyyar adawa shi ne, saboda abin da na yi la’akari da shi ya faru a Tarayyar Sobiyet. Kun san cewa Tarayyar Sobiyet ta kasance daula a baya amma a karni na 20 ta wargaje ba tare da an zubar da jinin kowa ba. Kowa ya kama gabansa kuma karshen al’amarin ke nan. A yanzu haka akwai kasashen 18 da suka kafu daga tsohuwar Tarayyar Sobiyet. A yanzu sun fi bunkasa da samun ci gaba a kimiyya fiye da kasashen yamma, domin sun nuna bukatar tafiya sararin samaniya, musamman a 1957 kuma suna da manyan masana game da tsare-tsaren yakin nukiliya fiye da NATO.”
“Kuma a lokacin ne na yanke kudurin cewa lallai babu gwamnatin da ta cancanta sai ta dimokuradiyya bisa jam’iyyu da yawa, musamman wacce za a gudanar ta hanyar sahihi kuma karbabben zabe. Wannan dalili ne ma ya sanya na samu matsala, saboda amanna da na yi da wannan kuduri. Daga Jam’iyyar APP sai na canja zuwa ANPP zuwa CPC, daga karshe kuma zuwa APC. Na yi takara a shekarar 2003, inda na kwashe wata 30 a kotuna, na karashe a Kotun koli. Na yi takara a 2011, inda na kwashe wata takwas a kotuna, nan ma na karashe a Kotun koli. Me ya sa na yi haka? Saboda na san dalilin kuma na yi amanna da tsarin,” inji shi.
Ya ce “A duk wadannan tashi-fadi a kotuna, mutanenmu da suka tantance abin da ya faru a rumfunan zabe, na rashin gaskiya da aringizo sun je kotunan sun bayar da shaida, amma duk da haka daga bisani kotunan suka ce sun amince da cewa akwai wasu wurare da ba a yi zaben daidai ba amma duk da haka PDP ta ci. Amma ga shi daga karshen karshe dai PDP ta fadi. Na kai makura a wannan hidima ne don in nuna wa mutane cewa, matukar ka daukar wa ranka kowane al’amari, kada ka sake wani ya karya maka gwiwa, ka ci gaba da turzawa!”
Shugaba Muhammadu ya ce: “Ina ma a ce na zama Shugaban kasa ne lokacin da nake da kuruciya, lokacin da nake Gwamnan jiha? Amma yanzu na tsufa, ina da shekara 72 a duniya, akwai abubuwan da ba zan iya yi ba. Na taba fafata yaki a fagen daga na tsawon wata 30, lokacin Yakin Basasa. Na rasa jajirtattun mutane da yawa, wadanda ke yi mini biyayya. Na rasa dan uwana kuma ’yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu. Don haka babu wani mutum da ya isa ya ce zai zo ya gaya mana maganar shirme. Za mu ci gaba da zama kasa daya, Allah Ya kara ba mu wata dama domin sake kintsa kasarmu. Duk wadanda suka jajirce suka bauta wa kasar nan, za ta saka musu.”
Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu su kasance jakadu nagari, ya kuma yi alkawarin cewa zai tattauna da Shugaba Jacob Zuma domin a dawo da kudaden Najeriya da kasarsa ta kwace a zamanin mulkin Jonathan.
“An shaida mini cewa akwai ’yan Najeriya 83 da ke gidajen yari a Afirka ta Kudu, ban san laifuffukan da suka aikata ba, amma na yi magana da shugaban kasar a yinin nan. Ya ce yana son zuwa Najeriya. Wadannan batutuwa ne da ya san da su, za mu tattauna game da su kuma ina fata jakadiyarmu za ta aiko mini da cikakken rahoto game da shari’unsu da kuma rahoto dangane da wadanda suka rasa dukiyoyinsu a lokacin tashe-tashen hankalin da suka faru a kasar kwanakin baya. Kuma a lokacin nan, zan yi kokarin tambayarsa game da kudin Najeriya Dala miliyan 9.7 da ba a maido mana da su ba.”