Dalilin da ya sa na yi wakar ‘Mu je Kano’- Ejike

Matashi Ugwuanozie Kingsley Ejike wanda aka fi sani da ‘Wasky Amana’ ya yi digirinsa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Jihar Enugu. Ya kammala hidimar kasa a Jihar Kano. A yanzu ya rungumi waka inda ya ce ya fi sha’awarta fiye da komai. A tattaunawarsu da Aminiya ya bayyana yadda aka yi ya sami […]

Dalilin da ya sa na yi wakar ‘Mu je Kano’- Ejike

Matashi Ugwuanozie Kingsley Ejike wanda aka fi sani da ‘Wasky Amana’ ya yi digirinsa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Jihar Enugu. Ya kammala hidimar kasa a Jihar Kano. A yanzu ya rungumi waka inda ya ce ya fi sha’awarta fiye da komai. A tattaunawarsu da Aminiya ya bayyana yadda aka yi ya sami sunan ‘Amana’ da kuma yadda ya fara waka.

A matsayinka na wanda ya karanta kimiyya ya aka yi ka samu kanka a harkar waka?
Bayan na kammala karatu sai na gano cewa zan iya bayar da gudummawa a harkar waka, don haka sai na fara. A yanzu haka ina jin dadin abin da nake yi zan kuma ci gaba da yin waka babu juya baya.
Yaya aka yi ka yi wa Gwamna Kwankwaso waka?
Da farkon lokacin da aka turo ni Kano don yin hidimar kasa mutane sun rika gaya min cewa kada na je. Amma daga baya sai na yanke shawarar zuwa ganin cewa mutane ne ke rayuwa ba aljanu ba, don haka sai kawai na taho. Na zo Kano cike da tunane-tunane masu yawa sai dai da na zo sai na iske mutane ne masu karamci da son mutane. Abin da ya ja hankalina shi ne yadda Gwamnan Kano ke yin ayyukan ci gaba. Daga nan na zama daya daga cikin masoyansa. Shi ya sa ma na kara Kalmar ‘Amana’ a sunana har kuma na yi masa waka.
Shin ka yi albam na wakokinka?
Yanzu ne dai na fara fitar da albam wanda ya kunshi wakoki guda bakwai wanda ake kira “Wasky Mu Je Kano” wanda kuma na sadaukar da shi ga mutanen Kano. Sai dai a halin yanzu na fara aiki a kan albam na biyu wanda nake sa rai zan kammala nan ba da dadewa ba.
Kana da niyyar zama a Kano ka ci gaba da wakokinka?
Mawaki ba shi da wani wuri guda daya da zai zauna. Ya kamata a ce mawaki yana yawo wurare daban-daban don karin samun fahimta. Ko ban zauna a Kano ba na dauki Kano a matsayin garina na biyu, zan kuma ci gaba da yin alfahari a koyaushe cewa na yi mu’amala da mutanen Kano.